A duk lokacin da suka so nishadi, su kan fiddo karamar katifar su Hassan ne a kofar daki su zauna, sosai zaman yana yi musu dadi lafiyayyar iska na kadawa, musamman idan akwai wani abu na motsa baki, tun Umaima ba ta saba da hakan ba, yanzu kam ta gano romon da ke cikin wannan yanayin, ita da kanta ma wani lokaci take fiddo katifar.
Kamar yanzu ma da suke zaune a kofar dakin Umaima. Fatima jotting take yi, saboda jibi zasu rubuta papernsu ta karshe.
Yayin da Umaima ke kwance rub da ciki, tana shan raken da ta siyo. . .
Amma Fatima Tana mistake sosai, I hope ba za ta zo tana regretting ba ai wannan shirme ne
Wannan shi ne ajizanci, bai yiwuwa Ace kullum mutum daidai yake yi