Skip to content
Part 47 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

A duk lokacin da suka so nishadi, su kan fiddo karamar katifar su Hassan ne a kofar daki su zauna, sosai zaman yana yi musu dadi lafiyayyar iska na kadawa, musamman idan akwai wani abu na motsa baki, tun Umaima ba ta saba da hakan ba, yanzu kam ta gano romon da ke cikin wannan yanayin, ita da kanta ma wani lokaci take fiddo katifar.

Kamar yanzu ma da suke zaune a kofar dakin Umaima. Fatima jotting take yi, saboda jibi zasu rubuta papernsu ta karshe.

Yayin da Umaima ke kwance rub da ciki, tana shan raken da ta siyo mai zaki, an yankashi ne guntu-guntu.

Dariya take yi sosai lokacin da Fatima ta gama ba ta labarin, wai wani me siyar da kifi ne, ya sayi rake yana sha, sai aka zo sayen kifin, aka tambaye shi nawa-nawa kifi?
Shi ko mai kifi sai ya ce “gaɓa-gaɓa”

Kiran da Aunty Hauwa ta yi ma wayar Fatiman ne ya katse dariyarsu.

Umaima ta mika mata wayar tana fadin “Aunty Hawee is calling”

Fatima ta amshi wayar hade da karata a kunnenta.

“Fatima kin ji Aliya ta rasu?”
Aunty Hauwa ta ce bayan Fatima ta daga kiran.

“wacece haka?” Cike da rashin sani Fatima ta yi tambayar ita ma.

“Matar Jamilu”

Gabanta ya fadi “Wa ne Jamilu? Kar dai Jamilunmu?”

“Wlh shi Fatima”

“Innalillahi Wa’inna Ilaihir Rajiun!!!” kalmar da Fatima ta rika maimaitawa kenan, kafin daga bisani hawaye suka sakko mata. Ta zare wayar a hankali cike da mutuwar jiki.

Umaima wacce jikinta ya yi sanyi ta ce “Menene ya faru?”

Cikin muryar kuka Fatima ta ce “Matar Yayana ce ta rasu.”

Kuka take yi sosai Umaima na kwantar mata da hankali, kafin daga bisani ta mike zuwa daki ta shiga hada kayanta.

“Ina za ki je Momyn Twins?” Umaima ta tambaya cikin sanyin murya.

“Gida zan tafi.”

“Jarabawar fa?”

“Na hakura Umaima, karatun ma gaba daya na hakura da shi, na fasa yi gida zan tafi.”
Cikin kuka take maganar don maganar gaskiya mutuwar Aliya na daya daga cikin mutuwar da ta dake ta, idan ta tuna ko magana basu taba yi ba, duk kuwa da yadda Aliyar ta rika shige mata sai hankalinta ya tashi, ta ji tsoron Allah Ya kara kamata, me ye cikin duniya da zai rudi mutum ya rika hura hanci, kamar jiya a kai ta badakalar auran Aliya da Jamilu, yau ga shi ba Aliya a doron duniya, to me ye zai sa ta dogon buri, ba mamaki ma gobe ta mutu, gara kawai ta je ta rungumi yaranta ko sun san dadinta kafin ita ma ta mutu ta bar su, kamar yadda Aliya ta bar tata yarinyar.

Umaima ta sauke ajiyar zuciya hade da amshe kayan da ke hannun Fatima ta zaunar da ita gefen Katifa

Cikin sanyi murya ta ce “I’m sorry mom twins, sorry please, sannu Allah Ya ba ku hak’urin rashi, ya raya abin da ta bari, amma don Allah ki saurare ni”

Ta zubawa Umaiman jikakkun idanunta.

“Jarabawarki tana da muhimmanci, tun da kin ce ba anan garin suke ba, in fact ma ba a Kasar ba, ki yi hak’uri ki rubuta, na daukar miki alkawari, zan jira ki, sannan in kai ki har gida, I promised you, please don Allah ki jira.” ta kai karshen maganar cikin kwantar da murya.

Fatima ta share hawayenta, cikin muryar da ta sha kuka ta ce” Umaima karatun nan ya fita a kaina, kawai ina karfin hali ne, amma kwarin gwiwata ya kare, na baro yarana, na bar mijina ma wata, na taho ba mamaki ma ba zan gama ba in mutu, ko in gama din, amma kafin cikar burina na samun aikin in mutu, ga Aliya ba zato ba tsammani ta rasu. Gara in koma in rungumi yarana su ji dumina. “

Hannayenta du biyun Umaima ta rike hade da kallon ta sannan ta ce” Ita rayuwar nan dama cike take da kalubale, ko min kudinka ko talaucinka, mutuwa kuma tana wuyan kowa, ba mu san yau ne ko gobe ba. Ki cire wannan tunanin, ki Kalle ni mana, ni ko auran ma ban yi ba, yanzu ni din ma zan iya, mutuwa, amma ban bar kowa ba, sai iyayena da ƴan’uwana, ke kuwa bayansu har yara gare ki, da zasu rika miki addu’a wannan bai ishe ki godiyar Allah ba. “

Shiru Fatima ta yi, tana sauraron yadda Umaima ke kwantar mata da hankali, har dai ta hakura.

Amma kwana biyun jin su take yi kamar shekara biyu, kashe wayoyinta ma ta yi, ku san wuni take yi kuka, Allah Ya sani mutuwar Aliya ta zo mata a ba za ta, fatan ta dai Allah Ya gafarta mata kura-kuranta ya raya abin da ta bari.

Ranar Alhamis kuwa misalin karfe goma na safe ta fito papern karshe, ba ta bata lokaci ba ta yo gida, inda Umaima ke jiranta, don ita tun ranar Laraba ta gama tata jarabawar, ta tsaya dai cika alkawarin da ta yi wa Fatiman ne na kai ta har gida, ko ba komai kuma ta yi musu ta’aziyya saboda kullum kara kusanci suke yi da Fatima.

Misalin karfe 11am na safe kuwa suka hau hanyar Daura. Tafiya ce mai nisa babu laifi, amma haka suka yi ta kamar kurame, wani lokacin dai Umaima kan tambayi wani abu ko karin haske a kan wani abun, kasancewar ita ba ta taba bin hanyar Daura ba, ita ba ma a Nigeria ta tashi ba, a Saudiyya ta tashi, kasancewar mahaifinta ambassador ne Nigeria a Kasar Saudiyya. Rasuwarshi ce ta sanya su dawowa gida Nigeria Kaduna, inda kuma ta zabi yin karatu a Jami’ar Yar’aduwa. duk dai har yanzu ba ta taba fadawa Fatima komai nata ba, kamar yadda Fatiman ma ba ta taba fadawa Umaima komai a kanta ba. Amma through communication kowa na fahimtar kowa.

Lokacin da suka isa Sandamu karfe biyu na rana, ga shi kuwa ana gantsara rana kamar ta gashin shege

Daga kofar gidansu Fatima zuwa kofar gidan Hakima rumfunan canopy ne aka kakkafa, na karbar gaisuwa, tamkar dai a nan Jamil din suke zaune.

Babu hanyar da Umaima za ta shiga cikin gidan da motar, dole ta samu wurin parking a waje.

Sosai Mustapha ya yi mamakin ganin Fatima ta bude motar ta fito, ya kara wara idon shi, sai ga Umaima ma ta fita, ta nufi boot inda karamin akwatin Fatima yake.

Dukkansu sanye suke da katon light brown din hijab Har kasa, fuskar nan fayau, yayin da alamun damuwa yake shimfide a fuskar.

Rabon shi da ganin Fatiman tun bikin Zainab, duk lokacin da ya jima bai ganta idan zai sake ganinta zai ya ga bakon canji a tare da ita, kamar yanzu ma sai ya hango wata tarin nutsuwa a tare da ita.

Sai da suka shige gidan sannan ya dauke idonshi a kansu.

A cikin gida kuwa Fatima jikin Mama ta fada hade da fashewa da kuka, abin da ya ba mutane mamaki, babu wanda ya yi tsammanin Fatima za ta damu da mutuwar Aliya haka, kasancewar ba wani shiri suke yi ba, amma ga mamakinsu har rama sai da ta yi duk da akwai exam pressure ma.

Sai da komai ya lafa ne, ta yi introducing din Umaima, sai kuma a lokacin ne ta ga Blessing, wannan ya tabbatar mata da Mustapha ya zo.

Duk da rasuwa aka yi, hakan bai hana an yi wa Umaima kyakkyawar tarba, duk da Umaiman fura kawai ta iya sha. A abincin da aka tara mata

Sai kuma a lokacin ne ta tabbatar Zainab ba ta kama da Fatima, yau kam ta ga masu kama da ita raɓa-raɓa. Musamman da ya kasance ma Zainab din tana wurin.

Ta yi mamakin Familyn Fatima, ita, da kanta take cewa lallai Familyn babba ne.

Abu da ya kara ba ta mamaki shi ne ganin Hana da Ziyad kuma aka tabbatar mata yaran Fatima, yara sun girma kamar ba ita ta haife su ba, abun ya burgeta sosai.

Fatima na sallahr magariba a ka zo kiranta Ummi na asibiti za ta haihu.

Tana sallame wa kuwa ko Umaima ba ta jira ba, a rude ta nufi asibitin.

Cikin ikon Allah misalin karfe takwas na dare Ummi ta sullubo kyakkyawar yarinyarta mace.

Amma sai da safe aka sallamosu.

Fatima dai ba ta dawo gidan Mama ba sai 11am,hankalinta duk yana kan Umaima. Kuma har zuwa lokacin basu wani kebe da Mustapha ba, iya ka ci su hadu a can, ko a nan. Sun ma fi haduwa a asibiti

Lokacin da ta zo gidan ma ba ta samu Umaiman ba, wai suna gidan Ya Bashir ita da Zainab.

Ba ta zauna ba ta wuce gidan Ya Bashir.

A can ta same su Umaima har ta yi wanka.

Suka gaisa sannan ta ce “I’m sorry na bar ki ke kadai, wlh…”

“Bai sai kin rantse ba, an yi min bayani, fatan dai tana lafiya yanzu.” Umaima ta katse ta.

“Alhamdulillahi ita da Baby duk suna lafiya. Wai shirin tafiyar ne?”

“Wlh fa. So na yi ma ana gama addu’a in dau hanya, so don dai ba kya kusa”

“Amma za ki dawo mana suna ko?”
Zainab ta tambaya.

“To ban dai sani ba, Kaduna na yi daga nan.”

“Kina kokari fa da tafiya mai nisa haka?” Fatima ta fada tana kallon Umaima.

Murmushi ta yi kafin ta ce “Wannan ne karona na farko da na yi tafiyar mai nisa ai.”

Haka suka ci gaba da hira har Umaima ta gama shirinta.

Sai da suka koma can gidan Umaima ta yi musu sallama, sannan su Fatima suka yi mata rakiyar har bakin mota. Kowa na yi wa kowa godiya, saboda Umaima tsarabar Nono, manshanu da fura aka yi mata.

A ranar Mustapha ya matsa lallai sai ta koma gida tun da an yi addu’ar uku, ga kuma Ummi ta haihu.

Haka ta kwashi yara suka taya ta gyaran gidan bangarenta da kuma bangaren Blessing, tun da suna nan sai an yi suna.

Jamil kuwa yana can bai dawo ba, saboda Aliya wurin haihuwa ta rasu, kuma yarinyar bakwaini ce, shi ya sa ya tsaya.

Sai dai a nan har salatul ga’ib aka yi wa Aliya.

Sai misalin karfe goma na dare Fatima ta samu kanta, a lokacin ma pampers take sanyawa Hussaini don tuni suka yi bacci.

Mustapha ya shigo dauke da sallama, ta amsa mishi ba yabo ba fallasa.

Duk suka yi shiru, kafin ya katse shirun da “Kina fushi ne?”

Kai ta girgiza alamar a’a.

“So what’s all that?”

“Ba komai.” ta ba shi amsa.

Ya tabe baki hade da dage kafadunsa sama, sannan ya ce “Amma a Abuja za kiyi wannan hutun ko?”

Kai ta girgiza alamar a’a.

“Me ya sa?”

“Haka nan.” ta ba shi amsa.

A can kuma ƙasan zuciyarta fadi take, wai ina dalili ne, za a dame ni da wata shegiyar Abuja.

“Fatima!”
Ya kira sunanta, ba ta amsa ba, amma ta dago kai tana kallon shi.

“Kin san auran ki nake yi ko? Akwai hakkina a kanki, so it’s okay, ya ishe ni haka irin wannan zaman, ke ce kawai nake fama da ke, idan na ce nan ki ce nan, halinki ya ishe ni haka.”

Shiru ta yi yayin da ta yi kicin-kicin da fuska.

Wannan shi ne karo na karshe da zan yi miki maganar zuwa wurina idan kin ga dama ki je, idan kin ga dama ki zauna. Kuma ki sani ni ma ba zan kara zuwa nan don ke ba, sai dai ko idan tawa ce ta kawo ni.”

Yana gama fadin haka ya shige toilet.

Ta bi shi da kallo hade da nazarin maganganunshi.” To idan bai zo ba sai me? ” ta yi maganar a hankali, kafin ta, dora da” Akwai lokaci Ya Mustapha, in sha Allah ba zan sare ba, kai ne mutum na farko da na yi tsammanin zan samu dukkan wani support daga gare shi a kan komai nawa, sai ga, shi kai ne mutum na farko da kake ta hadani da matsaloli, in Sha Allah zan jure hakan. Abuja kam a yanzu dai ba zan je ta ba, ku je can kui ta zama, idan kana son zuwana Abujar ai ba izza za ka nuna min ba.

Da alama Mustaphan ya yi fushi sosai, don koda ya kwanta baya ya juya mata, duk da abun bai yi mata dadi ba, sai ta kuma dannewa ta nuna ko a jikinta, abin da ya kara ɓatawa Mustapha rai.

Shi ya sa da gayya yake shigewa Blessing don kawai ya ba Fatima haushi, duk da tana jin haushin amma ba ta nuna ba, musamman yadda kullum take cikin hada-Hadar shagalin sunan Ummi.

Kowa ya yi rawar gani a sunan Ummi Mustapha dama uba ne, komai na uba ya yi, yayin da Fatima take matsayin uwa sai ita ma ta yi komai na uwa, Blessing ma ta yi rawar gani. Yarinya ta ci sunan Fatima inda suke kiranta da Zarah.

Wanshekaren suna, dakin Fatima su Goggo Asabe ne da Blessing sai Mustapha inda ake shawarar tafiya wankan jegon Ummi. Duk maganar da suke yi Fatima na jin su ba ta tanka ba.

Blessing ce ta ce “Tun da Momyn Ziyad makaranta za ta koma, Ummin ta bi mu Abuja mana.”

Duk mutanen falon suka zubawa Fatima da ido, da alama suna jiran cewarta ne.

Ita kuwa nazarin maganar Blessing din take yi, don Blessing ta yi subul da baka ta shaidawa Fatima wai Mustapha zai tafi da Hana da kuma Ziyad hutu Abuja, kenan sai su hada har da Ummi, ita kuma su bar ta nan ɓau, kamar wata wawuya, sai da ta gama sham kamshinta sannan ta ce “Abuja ta yi nisa, iska zai yi wa jaririya yawa, za a nemo wacce za ta zauna da Ummin”

Mustapha ya cika da mamakin yadda Fatima ke yanke hukunci cike da kasaita, sosai take ba shi mamaki idan ya ga ana jiran umarninta kan wani abu, ita kuma sai ta yanke hukunci kai tsaye cike da mulki. A cikin zuciyarsa ya yi murmushi ya dora da “Sarauta ba karya ba ce, kasaita a cikin jininsu take. Ko yane ka shafi sarauta sai wannan kasaitar ta yi aiki a jininka.”

Sosai Blessing ba ta ji dadin yadda Fatima ta yanke hukuncin ba, amma sai ta hakura, sai yanzu ta rika danasanin azarbabin da ta yi, na fadawa Fatima tafiya dasu Hana Abuja, duk da a lokacin ba ta ce komai ba, amma tana tsoron ta hana, saboda so take ta, kwace yaran, idan har yaran suka zo hannunta, kuma ta rikesu da kyau dole Fatima ta yi biyayya saboda ana barin halas ko don kunya.

Dole wani abun Fatima ta hakura ko don yaranta.

To burin Blessing dai ya cika, don Fatima ko kallon Mustapha ba ta yi ba a kan maganar tafiya dasu Hana, ta, San dai so yake ta yi magana kuma ba za ta yi ba, ya tafi dasu lantsandanma gaban lahira.

Sosai Aunty Hauwa ta yi fada kan daukar yaran, amma Sai Fatima ta ce a kyale shi, yaranshi ne shi ma.

Sati biyu ta koma makaranta, suka kama karatun 2nd semester. Shakuwarsu da Umaima kullum kara karuwa take yi.

Wannan semester sosai ta ji dadinta, kila saboda Umaima ne, don dama kadaici na daya daga cikin abin da yake haddasa damuwa.

Tun da Fatima ta koma makarantar ba ta je Sandamu weekend ba, kuma Mustapha ma bai zo makarantar ba, su kan y dai waya sama-sama, sannan duk sati yana tura mata 10k, a bakin Aunty Hauwa ma take jin wai ya sanya su Hana makaranta a can, wannan ya tabbatar mata da ya karbe yaranshi. Yadda bai fada mata ba, ita ma ba ta yi mishi maganar ba.

Successfully ta gana exam din 2nd semester ta koma hutu, zuwa lokacin daga ita har Blessing cikinsu ya girma, ba a san waye zai riga wani haihuwa, Mustapha dai ya zo sau daya, shi ma, maganar noma ce ta kawo shi, don noma yake yi sosai, kwananshi biyu ya koma babu wani kyakkyawan shiri a tsakaninsu.

Ba ta damu ba, don ta kanta ma take yi a lokacin. Har ya zo ya tafi kuma bai yi mata maganar su Hana ba, ita ma kuma ba ta yi mishi ba.

<< Daga Karshe 46Daga Karshe 48 >>

2 thoughts on “Daga Karshe 47”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.