Skip to content
Part 48 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Lokacin da ta koma 200L 1st semester ne da sati biyu sakon haihuwar Blessing ya risketa, inda ta samu Baby girl, Fatima ta kira ta yi Barka amma kam ba ta yi niyyar zuwa suna ba. Aunty Hauwa, Aunty Lami da Aunty Ayyo ne suka je, sai Ummi da kuma wasu ƴan’uwan Mustapha.

A can suka samu wasu daga cikin ƴan’uwan Blessing ƴan Maiduguri.

Tun kuma a daren kananun maganganu ke fita, wai Fatima ta mayar da Blessing yar rainon ta, ta bar yara da Blessing tana ta faman wahala ga ciki, ita kuma Fatima tana can tana karatu.

Duk yadda Blessing taso fahimtar dasu sun ki fahimta, gani dai kawai suke an shanye Blessing din, don tuni aka basu labarin ƴan Katsina mugun asiri gare su.

Safiyar suna yarinya ta ci sunan Inna inda ake mata lakabi da Ihsan, a lokacin ne kuma maganar mayar da Blessing yar raino ta bayyana.

Aunty Lami ce ta shiga dakin Blessing da kanta, inda ta, iske ƴan’uwan Blessing din na ta fada Blessing na kuka.

Duk maganganun da suke fada Aunty Lami na jin su don basu san ta shigo ba.

“Ku dakata!” Aunty Lami ta yi maganar cikin bacin rai.

Duk suka juyo suna kallon ta, cikin bacin rai ta ce “Ku Kalle mu da kyau, akwai alamun yunwa a jikinmu?”

Cikin sauri Blessing ta taso hade dukawa wurin Aunty Lami cikin kuka ta ce “Please Aunty, please don’t say anything I’m begging you in the name of Allah please Aunty, wlh ni ba ruwana.”

Aunty Lami ba ta bi ta kan Blessing ba ta ce “Dama ba da ke nake ba, masu magana zan ba amsa, ke kin san ba, a kan son Fatima aka debo mata yara zuwa nan ba, kuma ko da ace Mustapha ba Fatima yake aure mu masu rike mishi yara ne, bare yar’uwarmu ya aura kuma yaranta. Sannan yara nan gidan ubansu ne ba kwadayi suka zo ba, kuma du kuke maganar asiri, to da muna yi da yarku ma ba ta shigo nan gidan ba. “

Blessing ke ta kokarin janye Aunty Lami zuwa waje, amma bakin Aunty Lamin ya ki shiru, inda ta tabbatar yau su Hana basu kwana gidan, kuma su da zuwa hidimar Mustapha har abada sai dai idan Fatima ta, shafa, zasu zo don ita, don Mustapha har yanzu bai yi arzikin da za a wulakantasu a gidanshi ba.

Yadda Aunty Lami ke masifa da watsa maganganu ƴan’uwan Blessing basu yi tsammanin abun zai kai haka ba, su da kansu suka rika bayar da hakuri, ƴan’uwan Mustapha ma hak’urin suke bayarwa, don sosai Aunty Lami ta hau sama.

Blessing ta kira momynta cikin kuka ta labarta mata abin ya faru, sannan ta dora da “Momy ina, son Mustapha ke ma kin sani, amma son da yake min ba na jin ko kwatar na matarshi ya kai, yana son Fatima sosai, sannan yana son yaranshi, ni da kaina na dakko su Hana na kuma ce ya sanya su a makaranta a nan Abuja, wannan zai karamin kusanci dasu duka din, musamman matarshi mai wuyar sha’ani, ni zaman lafiya nake so ba tashin hankali ba, don Allah ki kira Aunty Hauwa ta lallashi Aunty Lami a bar yaran nan, kwashe su tamkar raguwar darajata ce a familyn Mustapha da na Fatima.”

Momy ta sauke ajiyar zuciya cikin sigar lallashi ta ce” please everything will be alright. Bari in kira Aunty Hauwan.”

Ba ta jira cewar Blessing ba ta yanke kiran, hade da kiran Aunty Hauwa.

Sai dai Aunty Hauwar ta shaida mata ta yi hakuri yanzu Lami ta hau sama, amma sha Allah komai zai daidaita.

Lokacin da Mustapha ya shigo gidan, saboda kiran da Blessing ta yi mishi ka sa cewa komai ya yi, bai yi tunanin abun ya kai haka ba.

Yana kallon Aunty Lami ta watsa yaran a mota hade da umurtar su Aunty Ayyo ma su shiga, cikin mintuna biyar motar ta fice daga gate din.

Yayin da fada ya, koma tsakanin Blessing da ƴan’uwanta, rufe ido ta yi, ta ce kowa ya, bar mata gida, ba zasu kashe mata aure ba. Ƴan’uwan Mustapha da aka bari sai suka koma ƴan kallo.

A can kan hanya kuwa Aunty Hauwa ce ta ce “Lami maganganun da kika fada sun yi tsauri, kamar har da gori fa.”

“Tsakuwa na tauna, wannan zai sanya su kiyayi gaba, ƴan kan’uba jibga-jibga dasu su zo su raina mana wayau, ba da hakoran Mustaphan talatin suka same shi ba, ga wacce ta ci wuya da shi, ba ta yi tashin hankali ba sai wacce ta zo daga baya. Zasu ce wai an dorawa ƴar’uwarsu wahala ga ciki, ba ita ce ta bukaci yaran ba. Allah ya karawa Fatima ma yar banza, ta tattara miji ta bar ma wata, ko sau daya ba ta taba zuwa gidan nan ba, ta ya raini ba zai shiga ba. “

Aunty Ayyo ta ce” Ai duk jikinsu ya yi laushi, sai bayar da hak’uri suke. “

“Yo mu zasu rainawa hankali, kaf dinsu ba kallonsu nake yi ba, idan na ga dama tun jiya ba sai in hana su bacci cikin salama ba, mu fa kunya gare mu amma ba tsoro ba.”

Cikin dariya Aunty Hauwa ta ce “Gaskiya kin daga musu hankali, Allah dai Ya kyauta na gaba”

“Amin” duk suka amsa, tare da ci gaba da tattauna matsalar.

Babu wanda ya ba Fatima labarin abin da ya faru, shi ya sa ba ta san komai ba. Ba ta san ma su Hana sun dawo Sandamu ba.

Bayan kwanaki uku da faruwar abun Mustapha ya biyo hanya, abin da Mama ke so kenan ta samu damar haife cikin Mustapha, shi ya sa ta ce ta karbe su Hana, ta cewa Aunty Hauwa idan Mustapha ya zo amsar yara ya zo ya karba a wurin ta.

A lokacin Aunty Hauwan cewa ta yi “Mama don Allah dai kar ki yi wata magana da za a zo a kunya.”

Cike da takaici Mama ta ce “Sai ko na yi, ni ma fa ƴata naƙuda na yi na haife ta, bawai daga sama ta fado, to lokaci ya yi da zan magantu, na gaji da, kawaicin da nake wa Mustapha.”

“Mama Mustapha kamar ɗa yake a wurinki kuma ke suruka ce, kar mutumci ya zube.”

“Ya zube mana, ke yanzu fa ba da ba ne, lokaci ya wuce da iyaye zasu zuba ido ana wulakanta musu yara su yi shiru, wai saboda alkunya, saboda surukan yansu basu san kawaici ba, dole sai an fito an nuna musu sun yi ba daidai ba. Shirun da mu ke yi ba ma shiga wata maganar ke sanyawa yaranmu zama a wulakance, sai mazan su ga kamar basu a kowa, shi ya ko wace shara sai su watsa musu, to ni kin ganni nan ba zan iya goyon dan jaki ba nauyi ya kashe ni. Daga nan har Abujar zan iya biyan kudin mota in je, in kare darajar ƴata. Ba fa yar banza na haifa ba. Tun da bai san zuru ba, ita kuma ta kasa yi mishi magana ni zan yi sai dai ya ce gori na yi mishi”

Ganin yadda Mama ta hau sama a lokacin sai ta kyale ta. Shi ya sa da Mustaphan ya zo ta tura shi wurin Maman.

Ana fitowa sallahr azhur kuwa ya shiga gidan dauke da sallama.

Mama da ke cikin daki ta amsa, hade da ba shi umarnin shigowa.

Bayan su gaisa Mama ta ce “An ce ka zo daukar yara ko?”

Ya daga kai a hankali, don har lokacin kanshi a kasa yake.

“To ai ka ji abin da Hauwan ta ce ko?”

Ya kuma daga kai a hankali.

“Me ta ce ma?”

A hankali ya ce “Cewa ta yi kun ce a’a, in zo wurinku.”

“Yauwa. Ni ce nan na ce ba zasu koma ba Mustapha, idan ka ga yaran nan sun koma wannan gidan sai da uwarsu. Har yanzu ba a haifo wadanda zasu ci wa zuriyata mutumci ba har da gori ba Mustapha. Yaran Fatima ko sun fi haka kai ka san Allah Ya hore mana abin da za mu rike su, kuma ba neman kai muke yi dasu ba, kai da kanka ka ce a ba ka zasu je hutu. To tun da abun ya zama haka b zasu koma ba, kar wahalarsu ta kashe matarka, ka bar su nan, mu wahalarsun ta kashe mu.”

Shiru ya yi bai ce komai ba, saboda ya fahimci Mama a sama take, ba tun yanzu ya san tana jin haushin shi ba, shi ya sa ma ba ya son magana mai tsawo ta hadasu, yanzu ma Aunty Hauwa ce ta matsa ya zo, amma da cewa ya yi, tun da maganar ta dangana da wurin Mama ba zai je ba.

“Wlh! Ka ji na rantse ma, (ta katse mishi tunanin shi) ban da akwai alaka tun farko a tsakaninmu, to da Fatima ta gama zama da kai. Saboda kai ba ka yi mata halacci ba.”

Karon farko da ya dago kai ya kalli Maman, kafin ya mayar da kansa kasa.

“Kwarai ma kuwa. Ba gori zan yi ma ba, amma a lokacin da kake na ka karatun wace wahala ce Fatima ba ta sha ba, me ye ba ta yi ma ba, iye! Amma a nata karatun fada min mai ka yi mata, dubu goma a sati ko? To Allah Ya tsinewa dubu gomanka a sati Mustapha, wlh Fatima ta fi karfin dubu goma a wajenka. Kuma kai kanka ka san ta fi karfin dubu goman. “

Sosai maganar Mama ta daki kirjinsa, bai taba tunanin ta dauki zafi da shi har haka ba, duk da ya san tana da zafi dama, idan ranta ya baci komai fada take yi, shi ya sa ya kara nutsuwa bai ce uffan ba.

” Mustapha ace da ranka da lafiyarka, Yarinyar nan har ta shiga shekara ta biyu, amma kafarka ba ta taba taka inda take ba, sai ka ce ba matarka, saboda ka samu wata ba ka damu da ina take kwana ba, ya take rayuwa oho. A komai na karatun Fatima ba ka sani ba, tana ci ba ta ci oho, ya take biyan kudin makaranta oho. Tun da dai kai ka yi naka ba ka da damuwa. Ina lura da kai fa, idan yarinyar nan ta zo hutu sau daya kacal kake zuwa, ka yi kwana biyu ka koma. Ita waccan kwanaki nawa ka kake kwashewa a wajen ta? Ko auranta ya fi na Fatima dauruwa ne. To ka bude kunnenka da kyau ka ji ni, magana ta gaskiya ba zan dauki wulakanta min yarinya ba.”

Jin babu alamun zai yi magana ta kuma cewa

“Ina sane da kai fa, da gayya ka zo ka kwashe mata yara ka kai su inda za a ci mutumcinsu da namu. A wulakanta mu. A gabanka, a rika yi wa yaranka gorin abinci. Me ye kuke ci a Abujar da basu ci a nan, har da za ace wai kwadayi ya sa muka tura su da hassada. To wlh ban da ina kallon wani abu, ka ga zamanka a dakin nan, ba ka tashi sai ka dire min takardar sakin auran Fatima, ni ba yar banza ba ce, da za a rika wulakanta ƴa da ciwa jikokina mutumci ina kallo. Yauwa! “

Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke jin ta yi shiru, da alama ta sauke rabin abin da ta tanadar mishi. cikin girmamawa ya ce” Mama har gobe ina son Fatima, kuma wlh ban taba yin komai da niyyar wulakantata ba, Fatima ba a bar wulakantawa ba ce a wurina. Duk abubuwan da suke faruwa a yanzu kawai rashin fahimta ne a tsakaninmu, amma Sha Allah zan gyara nawa bangaren don Allah a yi min afuwa.”

Duk suka yi shiru, kafin ya dora da” Don Allah ku yi hak’uri Mama, ku yafe min, matsayin uwa kike a wurina ko ba ki ba ni auran Fatima ba, sannan kin cancanci in yi laifi ki yi min fada. Don Allah ki yi hak’uri”

“Hakuri namu ne duka, na fada ma abin da ke ci min tuwo a ƙwarya ne, saboda na ga ko ba auran Fatima kake yi ba, ai tafi karfin ko wace alfarma a wajenka Mustapha, bare da igiyar har da zuri’a.”

“A yi hakuri don Allah!” Ya kuma fada cike da girmamawa”

Jin ba ta ce komai ba ya kuma cewa “To Mama yaran fa?”

“Na gama magana Mustapha, zasu koma amma da uwar su.”

“Mama suna makaranta ne a can, kuma makarantar akwai kyau, don Allah ku yi hak’uri kar a tsere musu, kuma wlh babu laifin Blessing a ciki.” cikin kwantar da murya ya yi maganar.

“Su fi ruwa gudu, su masu tsere mu sun.
Mustapha! Yara ba zasu koma ba, sai da uwarsu. Na gama magana”

Ya dan yi shiru sannan ya ce “Mama Fatima ita ce fa ta ki zuwa. Wlh na yi fama da ita amma ta ki zuwa”

“Wannan kuma tsakaninku.”

Ta yi maganar hade da mikewa ta bar mishi dakin.

Sai a lokacin ya samu damar sauke doguwar ajiyar zuciya. Abin da ya fahimta, zama da mace sama da daya sai an jure, kullum cikin matsala da tashin hankali, wannan bangare yana kallon ba a yi mishi adalci ba, wannan ma yana kallon ba a yi mishi adalci ba.

Yau kam Mama har da mishi gori, kuma ya tabbata da ace daga shi sai Fatiman ne ba lallai hakan ta faru ba.

Tabbas bai kyauta ba, da bai taba zuwa inda Fatima take ba, haka ko sau daya bai taba biyan registration nata ba. Wannan kam babban laifi ne, ita ta biya mishi registration fiye da sau daya. Akwai bukatar ya gyara wannan.

Jiki a mace ya fito daga dakin ya yi wa Mama sallama, gidan Aunty Hauwa ya koma ya yi mata bayanin yadda suka yi da Mama, ita ce ta dan kwantar mishi da hankali, sannan ta ce sha Allah yaran zasu dawo Abujar su dai ba Mama lokaci ta huce.

Haka ya juyo zuwa Abuja rai bace, komai baya mishi dadi, musamman idan ya wayi gari ya ga abokan su Hana suna ta tafiya makaranta sai ya ji wani kunci ya mamaye kirjinsa.

Bayan haihuwar Blessing da wata daya Fatima ma da haihu, ita ma an samu Baby girl, a gidan Aunty Lami aka yi shagalin suna, kasancewar Fatiman na gab da fara jarabawar 1st semester 200L, shi ya sa ba ta koma gida ba, ba ma ta yi wani taron suna ba, su Umaima da Zainab ne su kai ta hidima, Yarinya ta ci sunan Aunty Hauwa suna kiranta da Jiddah. Umaima kuma da Beauty take kiranta, don kaf yaran Fatima babu wanda ya kai ta kyau, Aunty Lami har tsokana take yi, ta ce wannan karon dai an haifo wa Mustapha yara kyawawa. Don yarinyar Blessing ba daga baya a wajen kyau.

Mustapha kam ya yi rawar gani a wajen sunan, mahaifiyar Blessing da kanta ta zo wajen sunan, sannan ta wuce Sandamu wajen Mama a kan batun su Hana, sai a lokacin ne Fatima ta san abin da ya faru, amma ba ta sanya baki.

Cikin sa a kuma Mama ta amince ta bawa Maman Blessing din yaran, suka koma Abujan tare.

Fatima ba ta yi arba’in ba, suka fara jarabawa, wannan karon ba ta sha wahalar jarabawar ba, kila ko don ta fara sabawa.

Koda suka gama jarabawar ba ta dawo gida ba, sai da ta kammala da maganar attachment din ta, inda ta samu yin aiki da gidan radion jaha.

Umaima kuma da Federal medical center Katsina.

Ganin Komai ya kammala sai ta wuce Sandamu kafin ranar fara aikin da suka ba ta ta zo.

<< Daga Karshe 47Daga Karshe 49 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×