Duk yadda Fatima ta so gocewa zuwa asibitin sai da Mustapha ya tasa keyarta, bayan ya kai Beauty gidan Mama.
A can asibiti kuwa gwaje-gwaje aka aka yi wa Fatima, irin su typhoid, Malaria da kuma ciki. Malaria da typhoid ne aka samu kadan, suka hada mata magunguna.
Gidan Mama suka wuce kai tsaye.
Mama tsaye da goyon Beauty a tsakar gida tana faman jijjigata, da alama so take yi ta yi bacci.
Ta amsa sallamarsu tana bin su da kallo, addu'arta kar ace Fatima cike gare ta, sosai ba ta son cikin nan a yanzu.
A tsakar. . .