Skip to content
Part 51 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Duk yadda Fatima ta so gocewa zuwa asibitin sai da Mustapha ya tasa keyarta, bayan ya kai Beauty gidan Mama.

A can asibiti kuwa gwaje-gwaje aka aka yi wa Fatima, irin su typhoid, Malaria da kuma ciki. Malaria da typhoid ne aka samu kadan, suka hada mata magunguna.

Gidan Mama suka wuce kai tsaye.

Mama tsaye da goyon Beauty a tsakar gida tana faman jijjigata, da alama so take yi ta yi bacci.

Ta amsa sallamarsu tana bin su da kallo, addu’arta kar ace Fatima cike gare ta, sosai ba ta son cikin nan a yanzu.

A tsakar gidan Mustapha ya barsu, yayin da Fatima ta wuce daki ta kwanta kan kujera

Mama ta shigo dakin hade da tambayarta jiki.

“Da sauki” ta amsa hade da mika hannu ta karbi Beauty.

“Amma ba ciki ba kam?”

“Ba shi ba ne.” ta ba ta amsa hade da murmusawa.

Aunty Hauwa ta shigo hannunta rike da na su Hassan da alama daga makaranta suke.

“Har an tashi?”
Fatima ta tambayi Aunty Hauwa lokacin da ta shigo cikin falon sosai.

“Su dai aka tasa, kuma yau mai kawo su gidan ba ta zo ba, dole na baro makarantar na kawo su. Na hadu da Ummi yanzun nan ta ce asibiti za ta je wajenki wai ba ki da lafiya.”

Fatima ta bi Mama da kallo har sai da ta fice, a hankali ta ce “Ƙalau nake fa”

Aunty Hauwa ta zuba mata ido alamun karin bayani.

“Bariki na ga za a nuna min, shi ne nake son nuna musu ni a can ma na kwana”

Aunty Hauwa ta rike haɓa cike da mamaki ta ce “Ni ban gane ba fa”

Fatima ta korawa Aunty Hauwa labari, sannan ta dora da “Wlh idan ban ga dama ba sai dai ta biyo shin, kuma ko ta zo, ta zo ma banza. Ba sai dai da kwanciyar hankali za ta samu abun da take so din ba.”

“Duniya!” Aunty Hauwa ta ce, hade da zama a kan 1seater

“Wlh ki daina irin haka, kar Allah Ya jarabce ki, tun farko ba ke kika sakar mata Mustaphan ba, sai yanzu kuma ki ce wai son shi kike yi, ai ke ma kin san karyarki, tun farko an fada miki kuskure kike yi, kika ki ji”

Tura baki ta yi kafin ta ce “Aunty idan na tsaya competition a kan Ya Mustapha wlh ba zan yi karatun ba, hankalina biyu zai rabu, amma idan na gama, sai in je a zuba ta a faifai kowa ya kwashe.”

Tabe baki Aunty Hauwa ta yi kafin ta ce “To yasin ki warke ya koma wajen matarshi ban san daukar alhaki, haka kawai ki tayar mishi da hankali yana ta kashe kudi a iska.”

“Allah ba zan warke sai ranar Juma’a ma zan fara samun sauki”

Sallamar Ummi ce ta hana Aunty Hauwa yin magana.

Zarah Fatima ta fara amsa, kafin ta amsa gaisuwar Ummin, inda take shaida mata, ta je asibiti da kuma can gidan ba ta same ta ba.

Duk hirar da suke Aunty Hauwa na ji, wata ta tsoma baki, wata kuma ta yi shiru.

A nan Aunty Hauwa ta yi sallahr azhur, Ummi kam sai la’asar ta bar gidan Mama.

Mustapha bai dawo gidan ba, sai da ya yi sallahr isha’. A gidan Mama ya ci abinci, sannan suka wuce gida.

Safiyar talata Mustapha shi ya yi ta hidima a gidan, hatta shirya su Hassan zuwa makaranta, don a gidansu suka kwana.

Fatima ta yi lamo a gado, inda ta ce, idan ta mike jiri take ji.

Abun ya fi daga hankalin Mustapha shi ne yadda jikinta ba zafi, amma kuma kullum babu lafiya, duk da likitan ya ce ana samun hakan, amma hankalinsa ya kasa kwanciya, damuwarsa kar ace mutanen boye ne.

Bai samu ya zauna ba sai wajen goma na safe, yayin da Fatima ke baccinta hankali kwance, a cikin baccin ta ji karar wayarshi, da sauri ya dauka zuwa falo don kar ya tashe ta.

Duk da kasa-kasa yake maganar, hakan bai hana ta jin abin da yake cewa ba.

Cikin fada-fada yake magana “To wai zan yi miki karya ne, saboda ke fa dama na kashe wayata”

Ya dan yi shiru, alamun yana sauraron abin da ake fada daga daya bangaren.

“Duk yadda na so tahowa dai kin san ba zan taho in bar Fatima ba lafiya ba”

Shiru ya dan ratsa kafin ya ce “Look! Fatima matata ce, idan har ba ta yi korafin a kanki ba, bai kamata ke ki yi a kanta ba. Ban ba ta da lafiya, tun da na aureki, mun taba yin sati biyu a tare?”

Ya yi shiru kadan kafin ya dora “To ki cire bakinki a maganar matata, ina sonki ina sonta, ko wane yana da hakki a kaina, na san kuma abin da nake yi, idan za ki taho ai kin san hanya”

Ya kuma yin shiru kafin ya ce “Please ba kuka na tambaye ki ba, idan za ki taho, ban hana ki ba.”

Daga haka ya yanke kiran.

Fatima ta kuma lafawa kamar dai ba ta ji wayar ba.

Shigowarshi bedroom ba da jimawa ba, wayarta ta hau ringing.

Cikin yanayin bacci ta sanya hannunta ka san pillow ta janyo wayar, ganin sunan Blessing sai ta yi receiving.

A can Blessing ta daidaita muryarta hade da gaishe da Fatima.

Cikin yanayin muryar bacci ta amsa gaisuwar, sannan Blessing din ta yi mata ya jiki, ita kuma ta amsa mata da sauki, Blessing ta dan jajanta mata sannan suka yi sallama.

Mustapha kam gidan Aunty Hauwa ya tafi don karbo musu abincin rana.

Don tun da Fatima ta fara ciwon karyarta a can yake karbo musu abincin rana da kuma na dare. Shi kuma ya hada musu break

Shi ya sa ranar Alhamis bayan Mustaphan ya karbo abincin Aunty Hauwa ta kira Fatima a waya.

Da gawar ta ke wuya Auntynta ta ce “Wlh Fatima zan ci ubanki, yau naga iskancin banza, ni din aikinku nake yi ne, da kullum nake a gindin murhu ina muku abinci, to wlh yau ki warke a ciwon nan idan ba haka ba, ranki zai yi mugun baci”

Fatima da ke kunshe dariyarta ta ce “Ayyah Aunty! Gobe fa zan ji sauki”

“Ba sauki za ki ji ba, wlh warkewa za ki yi gabadaya, idan ba haka kin san Allah zan fadawa Mustapha komai kin san dai zan iya.”

“kai Aunty!” ta fada a marairaice.

“To don Allah kar ki warke ki ga abun mamaki”

Fatima ta kwashe da dariya, yayin da Aunty Hauwa ke ta masifa, har sai da Fatima ta yanke kiran tana dariya.

A daidai lokacin Mustapha ya shigo dauke da food flask.

Ta narke kamar ba ita ce ta gama dariyar ba, haka ya shiga lallashin ta a kan ta ci abinci.

Yadda Aunty Hauwa ta taso ta a kan dole ta warke, duk da haka Mustapha bai koma Abuja ba sai ranar Lahadi.

Blessing ta san hannunta, koda ya koma ba ta nuna wata damuwa ba, ta amshe shi hannu biyu, kamar basu samu sabani ba.

Ganin haka shi ma sai ya watsar da guntun bacin ranta da ya taho da shi.

  Mustapha ya tafi da kwana biyu Fatima ta koma Katsina, don gidan radion sun neme ta, sannan zasu fara lecture ta 300 level, wacce take zama karshen shekarar Fatima a makaranta.

Dole ta tsarawa kanta komai, musamman da ya kasance shirin ba kai tsaye ba ne, ta kan je ta dau shirin ne, su kuma su dora.

Duk da yana cikin masu tsara labarin wasan kwaikwayo da gidan radion suke dorawa.

*****

Yau din tun safe garin ya nuna za a yi zafin rana, a haka Fatima ta fita don dakko wani rahoto a wani taro da ake gabatarwa babban dakin taro na Dikko.

Misalin karfe biyu na rana ta dawo gidan a gajiye likis.

Kai tsaye dakinta ta wuce, ruwa ta fara watsawa, kasancewar Beauty na gidan raino, nan kusa dasu take kai ta raino idan za ta fita aiki.

Sai da ta yi sallah ta ci abinci sannan ta fita dakko Beauty.

Tana kokarin bude daki ne motar Umaima ta shigo, dalilin da ya sanyata dakatawa tana kallon Umaiman da ta Parker motar cikin kwarewa.

“Sai yanzu wai?” Fatima ta fara tambayarta

Umaima da ta zama kalar tausayi ta ce “ki bari fa.”

Dariya Fatima ta yi sannan ta ce “Zama likita akwai wahala, ni ma ban jima da dawowa ba, yarinyarki na je na dakko gidan Baaba”

Dariya mai kama da yake Umaima ta yi ma Beauty hade da jan kumatunta sannan ta manna mata kiss a bayan hannunta, tana fadin “I missed you my Beauty Queen”

Beauty kuwa ta wangale mata baki hade da mika mata hannunwanta wai ta dauke ta.

Kai Umaima ta langabe cikin murya kamar za ta yi kuka ta ce “Ban iyawa, cikina babu abinci”

Duk suka yi dariya a tare sannan Fatima ta shige daki.

Umaima ma ta yi hanyar nata dakin.

Misalin karfe biyar na yamma Umaima ta buga kofar Fatima tana fadin “Momyn Beauty a fito waje a sha iska.”

Ganin Fatima ta fito rungume da laptop, Umaima ta ce “Wai yau da laptop din kika taho?”

“Ba dole ba, gobe da safe fa za a karanta rahoton a labaran safe” ta karasa maganar daidai tana zama kan katifa a gefen Umaima.

Sannan ta dora Beauty a tsakiyar bayan Umaima kasancewar kwance take rub da ciki.

Take ko Umaima ta fara tsallen doki.

Cikin ƴar karamar kara Umaima ta birkice tare da maido Umaima saman ruwan cikinta.

Hakan ya sa duk suka yi dariya su duka ukun kafin Umaima ta ce “Wlh yau na gaji sosai. Wani sabon likita ne ya zo, shi ne aka hadani da shi kan maganar project din nan, in fada miki yana ta wani sha min kamshi, ya bar ni a tsaye, wlh haushi ya sa na baro mishi kaf tarkacen project din na taho”

Fatima ta dakata da dariyar da take yi tana fadin “To wa kika yi ma wa?”

“Yo oho! Sosai ya ba ni haushi” ta yi maganar bacin rai shimfide a fuskarta, tamkar Fatima ce likitan.

Shigowar motar ne ya katse dariyar da Fatima take yi, yayin da Umaima ta bata rai, alamun dai ta ji haushin abin da ya farun.

Duk suka zubawa yar karamar yarinyar da ta fito daga cikin motar, a yanayin tafiyar kadai za ka fahimci ba ta gama kwarewa a tafiyar ba.

Sosai Fatima ta zuba mata ido, kallon sani take mata, dalilin da ya sanyata saurin dora kwayar idonta a kan sumar yarinyar.

Cikin sauri ta mike tsaye tana fadin “Umaima me nake gani kamar Maama (Tana nufin diyar Jamil)”

Sai a lokacin Umaima ta tashi zaune tana kallon yarinyar da ta yi kansu gadan-gadan.

Da sauri Fatima ta karasa hade da daga yarinyar sama tana kare mata kallo, kafin ta nufi motar.

Jamil ya bude marfin motar yana murmushi.

Sosai Fatima ji ta yi kamar ta rungume shi, bayan Aunty Lami da Zainab babu mai zuwa wurinta a cikin ƴan’uwa.

Yau sai ga Jamil kamar daga sama.

Fuskarta ta kasa boye farin ciki ta, don shi kanshi ya lura da hakan, bangare daya kuma ta kankame Maamah a kirjinta, kaunar yarinyar na ratsa duk wani sassa na jikinta.

“OH my God! Ƴa Jamil what a surprise?”

Ya fadada murmushin kafin ya ce “Just. I want surprised you and…”

“You did!” ta karashe mishi maganar cikin fara’ar da ta kasa barin fuskarta.

“Na yi farin ciki sosai da ganinku. Yaushe ka zo?”

“Yau kwana uku.” ya ba ta amsa.

“Shi ne babu wanda ya fada min” ta yi maganar a shagwabe.

Ya dan murmusa kafin ya ce “Ni na hana”

“Amma Ya Jamil zuwan yamma” yanzu ma a shagwaben ta yi maganar.

“Tun safe ina nan, na tsaya yin wani abu ne”

“Maamah ta yi girma” ta karashe maganar tana kallon yarinyar.

Da alama ba ta da hayaniya, don tun da rike ta ba ta yi kokarin sauka ba, kawai dai lafe a jikinta ne.

“Ita kadai ce ta girma?”

Dariya ta yi sannan ta ce “Har da kai. Wlh ka canja sosai, ka zama babban mutum ka yi wani fresh da kai abunka.”

Karon farko da sautin dariyarshi ya fita tare da fadin “Da gaske idan ace zan gan ki a hanya, zan fara tunanin anya ke ce kuwa. Kin canja, irin canjin da ban taba tsammani ba.”

Ta bi jikinta da kallo tana dariya “Na zama yar gayu yar boko ko?”

Shi ma dariyar ya yi yana fadin “sosai”

Ta juya tana kwalawa Umaima kira, har lokacin dariya take yi.

Hannunta sabe da Beauty ta kara so wurin, ya amsa sallmar da ta yi lokaci daya kuma yana dago kanshi.

Take Umaima ta canja fuska zuwa daurewa, yayin da shi kuma yake mata kallon ina ma ya santa

“Ya Jamil kenan, wanda kika rakani gida gaisuwar matarshi. Kuma ma ai kin sha ganinshi a hoto” Cewar Fatima ganin yadda fuskar Umaima ta canja lokaci daya.

“Ina wuni!” ta fada a hankali.

Fatima ba ta jira Jamil ya amsa ba ta ce “Umaima kenan, my best friend turn to like a blood sister.”

Kai ya shiga jinjinawa alamar gamsuwa.

Duk sai suka yi shiru, abin da ya ba Fatima mamaki, musamman da ta ga Umaima ta juya, maimakon ma ta zauna a wajen sai ta shige daki.

Dalilin da ya sanya Fatima mayar da hankalinta kan Jamil suka ci gaba da hirarsu cikin nishadi.

Ganin Maamah ta yi bacci, sai Jamil ya gyara seat Fatima ta kwantar da ita, a lokacin ne kuma Jamil din ya ce zai wuce.

Cikin marairaicewa ta ce “Ya Jamil tun yanzu?”

Ya dan yi murmushi sannan ya ce “Nan fa ba Sandamu ba ne, bare ki ce za ki yi kuka”

Ita ma ta murmusa kadan tare da fadin ” ba za ka gane farin cikin da nake yi ba. Babu fa mai zuwa Wurina sai Aunty Lami da Zainab, ita ma Zainab tun da ta yi aure ta daina, Aunty Lami kam dama sai da dalili”

“Shi ne abun damuwar?”

Ta gyada kai alamar eh

“Amma ai saura shekara daya, komai yana da lokaci, kada hakan ya dame ki. Kuma ni yanzu zan rika ziyartarki a kai-a kai.”

“Na gode” ta fada a hankali. Alamun dai abun na damunta.

Shi ne ya ciro mata manyan ledoji guda biyu, ta amsa hade da godiya.

Sosai ta ji wani iri lokacin da ya tafi, ji ta yi kamar ta bi shi, karon farko da ta ji kewarshi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 50Daga Karshe 52 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×