Kai tsaye Fatima dakin Umaima tazarce, a lokacin Umaiman zaune take kan katifa tana yi wa Beauty video wacce ke koyon tafiya.
Ganin Fatima sai ta dakata tare da fadin "Har ya tafi?"
"Ban sani ba." Fatima ta amsata bayan ta daure fuska.
Dariya Umaima ta yi kafin ta ce "What again?"
"Ba ki san me kika yi min ba ashe?" cewar Fatima tana harararta.
"Me na yi?" cikin dariya Umaima ta kuma tambaya.
"Yayana fa kika wulakanta." har zuwa lokacin harararta Fatima ke yi.
Ta dakata da dariyar tata kafin ta ce "Shi ne ya fara wulakanta ni ai. . .