Skip to content
Part 56 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Wani irin zama ne Fatima da Blessing ke yi na masu wayau biyu, ko wacce ba ta barin a ga fault din ta, gara ma Blessing ta kan yi borinta a gaban Mustapha, idan kishinta ya motsa, Fatima kuma shariya, sai ta tattare su duka ta share kamar babu su a gidan. Da zarar ta ga abin da bai gamshe ta ba.

Haka Mustapha zai ta fama lilo a tsakanin su biyun, na ganin ko wacce ta warware. Wannan abu ba karamin wahala yake ba shi ba, hada mata biyu ko sama da haka gaskiya matsala ne, lokacin da bassa tare ba ya shan wahala haka. Ina ma ko wacce da gidanta ya yi mata, ba fada suke na cacar baki ba, amma idan bai gyara wadannan guntayen matsalolin ba, sune zasu girma su zama manya.

Inda kawai yake jin dadi ko wacce a cikinsu ta san aikinta, ko wacce tana kokari wurin sauke nauyinta.

Na kulawa da shi, wajen nan ba shi da korafin komai, tsabta, abinci da kula da shimfida bai san wacce ta fi wata a cikin su biyun ba.

Blessing karfe takwas na safe take fita aiki, sometimes ita ke tafiya da yara ta aje su a school, Mustapha kuma sai 9am,gidan zai kasance Fatima kawai ita da yara

Shi ya sa ta kosa ta tafi, musamman yadda aka ce an fara musu tests, Mustapha kuma ya hana wai dole sai ranar Lahadi. Shi ya sa take ta kumburi

Yau Juma’a misalin karfe daya Blessing ta shigo gidan, kuma dama ita ce da girki, wani abu da Blessing din ta kiyaye shi ne no matter how idan har ita ke da girki to Mustapha abincinta yake ci.

Ta kan ta shi tun 4:30am ta shiga kitchen don yin breakfast, abincin rana kuma ta san ba ci yake a gida ba sai na dare, shi ya sa take baro wurin aiki da wuri ta shiga kitchen don shirya mishi abincin daren.

A hankali Fatima ke karantar ta, tana yi wa Mustapha irin So da biyayya kamar za ta mishi sujada, duk wani abu da ya shafe shi muhimmantar da shi take, ga wankan kananan kaya, ga wasu mayukan turare da har hawan kai suke saboda kamshi.

Ba ta gajiya da aikinshi ta dire wannan ta dau wancan.

Nan Fatima ta tabbatar Mustapha ba karamin So yake mata ba, yadda yake samun kulawa daga Blessing idan ya manta da ita ba za ta yi mamaki ba, don gaskiya ba za ta iya hidimar da Blessing take mishi ba da wannan kwantar da kan. Amma haka ya hakura ya zauna da ita yadda take, wani lokaci ta kan yi copyn wani abun, amma da zarar sun hadu da Mustaphan sai ta kasa aiwatarwa, dole ta daina tunanin kwaikwayon komai, kowa ya zauna yadda Allah Ya halicce sa.

Abun da Fatima ba ta sani ba shi ne, sau tari Blessing ita ma ta kan ji ina ma ita ce Fatima, ta iya share miji da kowa ma idan taso, amma kuma hakan bai sa miji kin yi mata abin da take so. Da yawan maza Allah na jarabtarsu da soyayyar mace da ke basu wahala. Yana matukar ba Blessing haushi gami da mamakin irin yadda Fatima ke dagula gidan idan ta so, da zarar ta birki ce, haka Mustapha ke birkicewa duk yadda ya so boyewa sai Blessing din ta gano ya damu da damuwar Fatima.

Kamar a cikin kwanaki biyun nan da Fatiman ta daga hankalinta wai tafiya za ta yi, Mustaphan ya ce dole sai Sunday, tun daga lokacin har zuwa yau Friday da Blessing ta karbi girki gidan ba dadi.

Yau haka kowa ya tashi rai bace sai dai suna kokarin da news, kamar Blessing ma kasa dannewar ta yi sai da ta fadawa Momynta, kamar kullum dai hakuri ta ba ta hade kwantar mata da hankali da kuma karfafa mata gwiwa.

Lokacin da ta Parker motar tata, a parking space,ba ta ɓata lokaci ba ta wajen daukar abin da take bukata ta shige ciki, a hanzarce ta shiga kitchen, dama ta yi miya tun safe, don haka farar shinkafa ta dora.

Zuwa karfe uku ta kammala komai har da wanka, dama Ihsan na wurin Fatima da sauran yaran.

Bayan ta zubawa Mustapha, ta debi nata, sai ta kaiwa Fatima food flask din gabadaya.

Mustapha bai shigo gidan ba sai biyar saura, tun da ya shigo kuwa Blessing ba ta zauna ba, ta shiga ta fita sai da ya ci abinci ya kara yin wanka. Duk da ta fahimci hankalinsa ba ya jikinsa, saboda tun da ya shigo ko tarin Fatima bai ji ba.

6pm ya shiga dakin Fatima, yayin da Blessing ta shiga gyara mishi dakin.

Ranta babu dadi, duk hidimar da take da shi, hankalinsa dai na wurin wata, wani lokaci sai ta ji kamar ta tattare shi ta watsar kamar yadda Fatima ke yi, amma ba ta iyawa, kowa da yadda Allah ya yi shi, idan ta ce za ta ari character Fatima ba za ta yi mata kyau ba.

Zaune take tsakiyar yaran, jikinta sanye da doguwar jar rigar atamfa, ta yi kyau duk da powder ce kawai sai man lebe a fuskar tata. Hasken fatarta ya kara fita fes.

Yaran da suka mishi oyoyo ya fara dagawa, sannan ya zauna kan kujerar da ke fuskantar ta.

Take yaran suka fice zuwa wurin Blessing, don an koyar dasu hakan, idan har Babansu ya shiga daki, to su zasu fita sai idan an ce su dawo.

“Duk a kan maganar tafiyar ne ko gaisuwa babu?”

Sai da ta hade fuska sosai kafin ta ce “Ai ba haka mu ka yi da kai ba, cewa ka yi 2daz kawai, amma yau kwanana takwas.”

“shekarata nawa a nan, sai yanzu ne kika zo kika min kwana takwas shi ne har kike korafi?”

Tura baki ta yi ba tare da ta ce komai ba.

“Ina mamaki irin yadda kika fifita karatunki a kaina, kullum dai a kan karatu ne muke samun matsala”

Yanzu din ma ba ta ce komai ba.

Ya nisa kadan kafin ya ce, “Ki shirya sai in kai ki gobe, idan kin ga dama ko kin gama karatun ki ci gaba da zama a can Katsinan. Kuma ba zan zo ba, kuma ba zan ce miki ki zo ba.”

Kai karshen maganar ta shi ya yi daidai da mikewarshi ya fice daga dakin.

Ta bi bayanshi da kallo kafin ta tabe baki tana fadin “Dama kai ka matsa min in zo, haka kawai an zo an hada ni da wata mata, ta shiga in shiga, ta fita in fita, yaushe zan iya wannan rayuwar zuciyata ai sai ta buga, wlh kai ta fushin ka ni tafiya ta zan yi, zaman Abuja kuma dama kune kuke sona da shi, amma na fi son Sandamu, har cikin zuciyata aka ce in zaba tsakanin Sandamu da Abuja zan dauki garina. “

Ta kai karshen maganar zucin nata hade mikewa zuwa bedroom saboda jin kiran sallahr magariba.

Lokacin da yake shaidawa Blessing zai mayar da Fatima gobe, tsalle ta yi ta dire ta ce ba a kwananta, dole Fatima ta hakura sai ranar girkinta.
Me ya sa abin da Fatima ke so shi za a yi a gidan koda kowa bai so.

Cike da mamaki Mustapha ya kalle ta ya ce “Kin manta karatu take yi ne? Kuma sun fara test. Ki fada min me na yi wa Fatima a gidan ban yi miki ba, yaushe Fatima ta zauna a nan har da kike cewa abin da take so shi ake yi?”

Cike da bacin rai Blessing ta ce “Ga example Dadyn Hana, lokacin da ta ce ba za ta zo walimar gidan nan ba, ina kula da yadda hankalinka ya ki kwanciya har sai da aka ce tana kan hanya. Tun da ta iso hankalinka na kanta kamar a ranar aka daura muku aure, yanzu kuma ta tayar da hankali wai za ta tafi, hankalinka ya ki kwanciya, dole za ka yi mata abin da take so. Me ya sa ba ta tayar da hankalin tafiyar tata ba sai da girki ya dawo kaina”

Mustapha kallon Blessing yake yi, wani banzan tunani sai mata, abu ƙarami su ruruta shi ya zama babba. Su mata dai idan suna su biyu komai za ka yi sai sun ce ka yi rashin adalci.

“Please get out of my side. Ba na son wadannan maganganun” ya yi maganar hade da nuna mata hanyar fita.

Fashewa da kuka ta yi a hankali hade da jan kofar ta fice, ya bi bayanta da kallo, ji yake da gaske kamar bai yi mata adalci ba, amma mayar da Fatima shi ne kwanciyar hankalinsa ta fi Blessing rikici, tabbas Blessing na hakuri amma bangaren kishi abu kadan ke tado mata shi.

Jiki ba kwari ya kwanta sosai kan gadon, yana tunanin ya je wurin Blessing ne ko ya kyale ta.

Can bangaren Blessing tana shiga dakinta ta iske wayarta na ringing, ganin Momy da sauri ta daga, cikin muryar kuka ta ce “Momy!”

“Are you crying?” cikin sauri Momy ta tambaya.

Cikin kuka Blessing ta ce “Momy ban san ranar da Dadyn Hana zai Soni is a kamar yarda yake son matarshi ba, wlh ina ji a jikina kawai yana zaune da ni ne saboda girman addininshi da na karɓa (ta shiga labarta wa Momyn abin da ya faru)”

“To za ki fita daga addinin ne?”

“No!” da sauri Blessing ta amsa Momy.
Kafin ta dora “A yanzu ba zan iya fita daga musulunci ba Momy, ina jin dadin kasancewa a cikinsa, ina kuma jin na yi asarar shekarun da na yi ba a cikinsa ba.”

“To ki yi hak’uri Rahma (Ta kira ta da sunan da ta ci a musulunci) aure dama yana tattare da kalubale, musamman ace akwai abokiyar zama. Ita tana nan tana kallon yana miki abun da bai mata, tana jin yana sonki fiye da ita. Zaman aure da abokiyar zama zargin zargi ake yi, tana zargin ya fi sonki, kina zargin ya fi sonta. Ki rika dauke idanunki da bakinki a kan matarshi sai kin fi mutumci a gurinshi da agurinta. Ki rika danne kishinki”

“Yanzu har Momyn Ziyad za ta ji ya fi sona a kan ta? Blessing ta tambaya cikin raunanniyar murya.

” Kwarai ma kuwa, idan an ce miki dalilin hakan ne ya sa ta matsa sai ta tafi kar ki yi gardama. Kuma ke ba dama ma za ki kara samu ba, I have been telling you since, Ki daina bude kofar da za ki samu ɓaraka da mijinki a kan wata. Just let them go, ba zai taba yin wata daya a can ba, idan ya kai ta gobe, dole zai dawo jibi ko Monday ko don aikinshi, so stop crying please. “

” Thank you Mommy ” Blessing ta fada hade da share hawayenta.

Sosai Momy ta kwantar mata da hankali kafin suka yi sallama.

Ko ba komai ta dan ji sanyi, wancan zafin da take ji yanzu ya ragu.

Ba tun yanzu take tunanin zaman da zasu yi da Fatima a gida daya ba, ta so ace raba musu gida aka yi, amma za ta ci gaba da hakurin kamar yadda Momyn ta ce.

Mustapha shi kadai ya kwana dama ya san Fatima ba zuwa za ta yi ba, don ita girkinta ne kawai ke kawo ta dakinshi, ko gaisuwa sometimes sai ya shiga duba ta ne take gaishe shi.

Blessing kam watarana kafin ta fita aiki ta kan leko su gaisa, ita ma idan kishin nata yana ka, ba ta lekowa.

Fatima dama tun dare ta hada kayanta, asubar fari ta karasa gama shirinta.

Amma har 8am Mustapha bai shigo ba, abin da ya yi matukar bata mata rai, don ta ga shigarsa dakin Blessing bayan ya dawo masallaci, kuma tun da ya shiga bai fito ba. Cika ta yi fam kamar za ta fashe, ita da taso 6am suna hanya amma har 8am suna gida.

Yara ma ita ta yi musu abinci suka ci, ta kuma rakasu islamiyarsu, da yake ba nisa a kafa suke zuwa.

Sosai take ganin abin da Mustaphan ya yi mata wulakanci ne, don kawai ya ga tana son tafiya, kamar ba daki daya suka kwana da Blessing din ba, to koma dai basu kwana daki daya ba, dawowa fa gidan zai yi su ci gaba da kwanansu.

Ta ja dogon tsoki hade da dakko wayarta, checking balance ta yi, matsalar daya yau Saturday, da bank ta tafi, ta cire kudin mota.

Wata dabara ce ta fado mata, don haka da sauri ta saba Beauty ta ja karamin akwatinta, lokacin da take kokarin fita gate Mustapha ya fito daga dakin Blessing, cike da mamaki yake kallon ta, yayin da ita kuma ta yi kamar ba ta gan shi ba, ganin tana kokarin rufe gate ya ce “Ina za ki je?”

Ba ta amsa ba, illa rufe kofar gate din da ta yi.

Da sauri ya sauka kan entrance din ya bi bayan ta.

Akwatin ya rike yana fadin “Ina za ki je?”

Sai da ya maimaita tambayar ta shi kafin ta ce “tafiya zan yi.”

“Ba na ce ni zan kai ki ba”

“Ba na son in takura maka ne” ta fada hade da kallon gefen ta.

Nisawa kadan ya yi wato ita ma har ta shaka, yana can yana lallashin wata, wata nan nan tana sabon fushi. Anya kuwa zamansu a taren nan zai yiwu, kar fa ya saka kansa a uku.

“Shi kenan, yi hak’uri, ban san sammako kike so a yi ba, mu je in canja kaya sai mu tafi.” ya kai karshen maganar ta shi hade da juyawa zuwa cikin gidan akwatinta a hannunsa.

Rai bace ta biyo bayan shi, daidai lokacin kuma Blessing ta fito hannunta rike da leda irin ta shopping, turarurruka ne masu kyau, na jiki, daki, da kuma na kaya ta ba Fatima.

Godiya ta yi mata hade da karbar ledar, Blessing na wurin a tsaye har sai da su Mustaphan suka fice.

Sun dauki tsawon 2hrs a hanya kowa bai tsinkawa dan’uwansa ba, Beauty kuwa ba a jima da fara tafiya ba ta yi bacci.

“Fatima!” ya katse shirun nasu ta hanyar kiran sunanta.

Ba ta amsa ba, amma ta dago kai sun hada ido.

“Zuwanki nan, akwai abin da bai yi miki dadi ba ne?”

Kai ta girgiza alamar a’a.

Ya mayar da hankalinsa kan hanya.

“Ina sonki, so na sosai, kina kuma da kima a idona, kin yi min abubuwa da yawa, har yanzu ban biya ba, ga shi zan kara neman alfarma a wurinki.”

Hankalinta ta tattara kaf bisa kansa.

Shi ya sa ya dora “Na san kin girmi Momyn Ihsan a aure, don haka dole kin fi ta experience a kan zaman aure, don Allah Fatima idan kin ga wani abu da bai yi miki ba, ki rika hakuri, ni din ajizi ne, ban isa in yi wa kowa daidai ba, abin da nake so ki sani dai shi ne ina sonki da kaunarki, ni din nan kin fi karfin wulakanci a wurina. “

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce” Na gode, Allah Ya ba ni ikon yin abin da kake so, ya bamu zaman lafiya. “

” Amin” ya ce

Ita ta katse shirun da fadin “Ka ce a bar su Hussaini Abuja, gaskiya aikin zai mata yawa, yara biyar kenan fa, ga shi tana fita aiki, me zai hana a samo mai taimaka mata”

“Ina wannan tunanin, ban san a ina za a samu ba ne.”

Kwanciyar Beauty ta gyara kafin ta ce “A yi wa Aunty Lami magana ta samar mana”

“ki yi mata to”

Haka suka ci gaba da tattaunawa har zuwa lokacin da suka shiga garin Katsina.

Lokacin da suka isa gidan Umaima ba ta nan, dama ta fadawa Fatima sai wajen 6pm za ta dawo, su kuma sun isa around 2pm.

Komai na dakin Fatima a gyare tamkar ba ta yi tafiya ba, ga abinci Umaima ta girka musu.

Ga shi Mustapha ya yi musu take away, wanda Mustapha ya saya suka ci, sai da ya yi sallahr la’asar kafin ya ce mata zai je gidan Aunty Lami ya mata bangajiya sannan ya wuce Sandamu.

Bayan tafiyar Mustaphan ba jimawa Umaima ta shigo gidan, ai sai labari ya tashi kamar sun yi shekara basu hadu ba, sallah kawai ke daga su, around 10pm ne Umaima ta koma dakinta don yi karatu, ita Fatima handout ta dakko, ta dan taba kafin lokacin bacci don agijiye take.

Safiya Sunday misalin karfe daya Mustapha ya shigo Katsina, hotel ya kama sannan ya matsa lallai Fatima ta zo kuma ban da Beauty.

Umaima ta samu abun tsokana, tun daga lokacin da Mustapha ya sanar mata ta same shi a hotel din Umaima ke tsokanarta. Musamman da Fatiman ta ce “Wane irin hotel kuma kamar wata yar iska”

Cikin dariya sosai Umaima ta ce “kun fa yi wa hotel mummunan fassara ne, amma shi kawai wurin saukar baki ne, ko ke kika ji kina da bukatar kadaici za ki iya zuwa ki kama daki, ki huta abun ki idan mun dame ki da hayaniya.”

“Ni!” Fatima ta nuna kanta da yatsanta manuniya.

“Ke kuwa.”

“To idan Mama ta ji na je hotel tsine min ne kawai ba za ta yi ba, amma sai ta ce in je in nemi gafarar Allah da aurena na je hotel. Cewa za ta yi shi Mustaphan hauka yake yi da zai dauki matarshi ta sunnah zuwa hotel”

Dariya Umaima ta kuma yi kafin ta ce “To ke labari za ki ba ta”

“Na sanni sarai, zan iya ba ta din ma.” Fatima ta amsata lokacin da take ci gaba da shirin ta.

“Mu je in sauke ki, mu gidan Aunty Halima ma za mu je”

“Yaushe za ki fara koya min tukin ne?”

Umaima ta bude baki tana kallon Fatima, don daga dawowarta jiya zuwa yau ta yi magana a kan tuki fiye da 70

“Wai da gaske kike yi dai ashe”

Tana rolling din dankwalin blue black din doguwar rigar da ta sanya ta ce

“Au! Wai kin dauka da wasa nake yi? A duniya dai ban iya tukin mota ba ai na sha haushi.”

“To ba sai ki dauki direba ba.”

Cikin sauri Fatima ta juyo kamar Umaima ta fadi wani abun zunubi ta ce “In sayi motar da kudina, sannan in koma baya wani ya ja ni, ai ban mori kudina ba, ai kawai in murza kan mota malama, in fito ina babbasarwa, in wani kulle ko ina, sannan in juya ina kwas-kwas Haba!!! Dadi kashe ni, Allah Ya nuna min ranar.

Cikin dariya Umaima ta ce” Amin “

Haka suka fice cikin nishadi, a kofar hotel din Umaima ta sauke ta, suka wuce gidan Aunty Halima Umaima na ta kwasar dariyar yadda Fatima ta yi tsuuu alamun dai kan dole ta zo, dari-dari take da komai.

Tun daga waje ta rika yaba tsarin ginin, tsit ba hayaniya.

Mustaphan ne ya zo suka tafi, ta shiga karewa dakin kallo, a zuciyarta ta ce “Masu kudi dai suna morewa”

Lokacin da ba ta mallaki dakinta na Abuja ba, aka ce za a yi mata kyautar wannan ta rayu a ciki, to da kwarin gwiwarta za ta karɓa, wanda zai rayu a kabari ya samu wannan ba sai godiya ba, komai akwai a ciki.

“Wai yaushe kika fara sanya dogayen riguna ne?” Mustapha ya yi tambayar daidai yana zaunar da ita gefen gadon, saboda tun da ta shigo a tsaye take sai Kalle-Kalle kawai take yi.

“Ba su yi min kyau ba hala?”

“Zan iya cewa bayan riga da siket wannan ita ce shiga ta biyu da take miki kyau. Kina yin kyau a ciki sosai, sai ki fito kamar wata Dr ko ambassadorn Kasar Saudiyya musamman idan kin sanya eye glass, sosai kike tafiya da ni. “

Dariya sosai ta yi kafin ta ce “Kai Ya Mustapha”

“I’m telling you” ya fada yana kallon yadda take dariya.

Ta dakata da dariyar “Ya ka baro Mama, me kuma ta ce a kan maganar su Hassan da aka baro su can”

“Fada ta yi sosai, ta ma ce a maido su, wai sun yi kankanta da zama ba kusa da uwarsu ba.”

“Ba na fada ma ba, dama na san za ta yi fada, to za ka maido sun ne?”

“Ba dole ba.” ya fada hade da zare ido. Kafin ya dora “Kin ga fadan da ta yi kuwa? Na ki ma na can yana jiranki”

Murmushi Fatima ta yi kafin ta ce “To yaushe za ka maido su?”

“Momyn Ihsan za ta kawo su next weekend sha Allah”

“Allah Ya kai mu”

“Amin” ya fada hade da janyo ta jikinsa yana fadin “Ba zan sake zuwa ba fa, idan kina da bukatata kin san inda nake ai, amma na gaji da bin ki.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 55Daga Karshe 57 >>

2 thoughts on “Daga Karshe 56”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×