Sai ya sallami mutum uku da ke jiranshi, sannan ya cewa su Fatima su shigo.
Kan dan karamin gadon da ke office din ya ce Umaima ta hau, ba gardama kuma ta hau.
Ba jimawa wata nurse ta shigo, yana tsaye har ta ja jinin Umaima, wacce ganin idon Jamil ne kawai ya sa ta tsaya.
Ba jimawa nurse din ta dawo da result din.
Da kansa ya fita sayen duk wasu magunguna na da ake bukata.
Bayan ya sanya mata drip din ne Fatima ta ce "Na baro Beauty a gida fa, yanzu ya za a yi?"
Ya dan. . .