Skip to content
Part 58 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Sai ya sallami mutum uku da ke jiranshi, sannan ya cewa su Fatima su shigo.

Kan dan karamin gadon da ke office din ya ce Umaima ta hau, ba gardama kuma ta hau.

Ba jimawa wata nurse ta shigo, yana tsaye har ta ja jinin Umaima, wacce ganin idon Jamil ne kawai ya sa ta tsaya.

Ba jimawa nurse din ta dawo da result din.

Da kansa ya fita sayen duk wasu magunguna na da ake bukata.

Bayan ya sanya mata drip din ne Fatima ta ce “Na baro Beauty a gida fa, yanzu ya za a yi?”

Ya dan yi jim kafin ya ce “Just go, I will handle everything”

Ita ma shiru ta yi cikin nazari kafin ta ce “To ya za a yi da Umaima din?”

“Za ta kwana a nan.” ya fada kansa tsaye.

Cikin zaro ido ta ce “Kwana kuma, to waye zai kwana tare da ita?”

Sosai ya gaji da yawan tambayoyin ta, dalilin da ya sa ya mata shiru. Har sai da ta kara maimaita tambayar tata. Kafin ya ce “Ba akwai nurses ba.”

Daga yadda ya amsa mata ta san ya gaji da maganar ne.

Shi ya sa ita ma ta yi shiru, amma ba don ta gamsu da barin Umaima a asibitin ita kadai ba.

Cikin mutuwar jiki ta karasa inda Umaiman ke kwance tana bacci, yayin da drip din ke diga a hankali zuwa jikinta.

Dankwalinta da ya zame ta gyara mata, take kuwa Umaiman ta bude idonta a hankali masu dauke da baccin, kafin ta mayar dasu ta lumshe.

Ganin Fatima ta nufi kofa, sai ya mike hade da bin bayanta.

Ya dauka mashin za ta hau, amma ga mamakinsa, gani ya yi ta nufi motar Umaima da ke Parke, hade da bude driver seat ta zauna.

Cikin mutuwar jiki ta murza key din motar tare da fita daga parking space din zuwa gate.
Yana tsaye cike da mamaki ta fice.

Gani yake kamar ba Fatima ba ce, wata ce daban, yaushe ta iya tuki?

Da mamakinta ya koma ciki, ganin Umaima bacci take yi sosai, sai ya ci gaba da aikinsa, lokacin zuwa lokaci dai ya kan gyara mata zaman hannunta mai drip, ko kuma ya duba tafiyar ruwa.

Fatima kuwa a can ta kasa nutsuwa, shi ya sa ana yin sallahr isha’i, ta kuma juyowa zuwa asibitin. Daidai Umaima na shan tea da Jamil ya hada mata, jira yake ta shanye ya sanya mata dayan drip din.

Shigowar Fatima ta sanya su mayar da hankalinsu kanta.

Sosai Umaima ta ji dadin ganinta, don dama duk a takure take.

Ta dan rike dariyarta saboda kallon da Jamil din yake mata kafin ta ce “Ina wuni Ya Jamil.”

Bai amsa ba, haka bai dago kanshi daga danna wayar da yake ba ya ce “Zan cinye ta danya ne?”

Tabbas Umaima ta ga bakinshi ya motsa, amma ba ta san me ya fada ba, kasancewar akwai dan tazara a tsakaninsu. Fatima kuwa da yake zaune take a kujerar duba marasa lafiya ta ji shi, shi ya sa ta dan yi dariya kadan kafin ta ce “Ba haka ba ne, amma ka san bai dace in bar nurse su kwana da ita ba, kamar wata mara gata.”

Tabe baki ya yi ba tare da ya ce komai ba.

Mikewa ta yi zuwa inda Beauty ke zaune a tsakiyar gado tana sipping din tea a hankali, hade da ba Beauty da ke tsaye a kasan gadon.

” Ya jikin? “

” Akwai sauki” Umaima ta amsa a hankali.

Cikin kasa da murya ta kuma cewa “Don Allah ki roke shi, mu tafi gida, sai ya sanya min drip din a can ban son zama a nan.”

Juyawa Fatima ta yi inda Jamil yake zaune kamar bai san dasu a cikin office din ba.

Ita ma a hankali ta ce “Ki roke shi mana ke.”

Bata rai ta yi, hade da make kafada alamun a’a.

Murmushi Fatima ta yi kadan hade da juyawa zuwa inda Jamil yake zaune

“Me ya faru ne?” ya fada bayan ya tamke fuska, ganin Fatima ta sanya shi a gaba.

“Dama cewa na yi, tun da gobe tana da exam, don Allah ko za ka taimaka mu je can gida a sanya mata drip din a can, so that da safe sai ta wuce makaranta.”

Bai ce komai ba, kamar yadda bai nuna ya ji abin da Fatiman ta ce ba.

Umaima daga inda take zaune take kallonsu, cike da fatan amincewarsa.

Da sauri ta janye idanunta ganin sun hada ido da shi, yayin da gabanta ya tsananta faduwa.

Ta rasa dalilin da ya sa idan ta gan shi ko ta ji maganarshi gabanta ke irin wannan faduwar kamar dai tana jin tsoron shi.

Ta yi mamakin yadda ya yi ta cakarta dazu amma ba ta yi komai ba, shi din kawai zai yi mata haka ba tare da ta yi gardama ba.

“Ku mu je” ya fada a hankali.

Kamar jira Umaima ke yi, ta duro daga gadon, take kuma jiri ya debe ta.

Tsakanin Fatima da Jamil ne suka shiga rige-rigen rike ta.

Inda Jamil ya riga Fatima yin hakan.
After some minutes ta dawo daidai, shi ya sa ya cewa Fatima da ke tsaye tana kallon su “Zo ki taimaka mata.”

Da sauri ta karaso hade da raba Umaima daga jikin Jamil din, shi kuma ya dauki Beauty hade da ledar magungunan ya bi bayansu.

Ita taimakawa Umaiman ta zauna a seat din mai zaman banza, sannan ta zagaya zuwa driver seat, tana kokarin rufe kofar ne Umaiman ta ce “Ji nake yi kamar zan yi amai”

Dakatawa Fatima ta yi tare da fadin “To ko za ki fita.”

Daga kan Umaiman ya yi daidai da bude kofar motar ta fice da sauri.

Da saurin ma Fatima ta bi bayanta zuwa wurin kwatar da Umaiman ta duka tana kwarara amai.

Jamil ya karaso wurin rika da gorar ruwa ya mikawa Fatima, sai da Umaima ta wanke fuskar ta, sannan Fatima ta kamata. Jamil ya kuma bin su a baya.

“Ya Jamil kodai ta dawo wajenka ne?” Fatima ta fada tana kallon Jamil din.

“Me ya sa?” ta tambaya idonsa zuba a kan Umaima da ta langabe jikin Fatima.

“ina jin tsoro, ba zan iya tukin ba.”

Da hannu ya yi mata alamar ta kai Umaima cikin motar tashi.

Seat ya kwantar mata yadda za ta ji dadi sosai, sannan suka fice, Fatima na gaba shi kuma yana bayanta.

A dakin Fatima ya sanya mata drip din hade da nunawa Fatima yadda za ta cire idan ya kare. Sannan ya fada mata idan ta ga abin da ba ta gane ba, ta kira shi komin dare.

Sai a lokacin Fatima ta samu nutsuwar amsa kiran da Mustapha yake mata.

“Ina kika aje wayar ne?” ya tambaya rai bace bayan amsa sallamarta.

“Tana a cikin jaka, Umaima ce ba lafiya shi ne mu ka je asibiti”

Ya dan sassauta kadan “To ya jikin nata?”

“Akwai sauki, Ya Jamil ya sanya mata drip”

“Subhanallah! Har abun ya kai haka?” a tausashe ya fada.

“Wallahi”

“To Allah Ya sawake.”

“Amin.” ta amsa a hankali.

“Nan din za ki zo ko Sandamun?”

Sai da ta dan narke murya kafin ta ce “Ina son zuwa Sandamun ma.”

“OK. Mu hadu a can, zan je in duba wata gona da aka yi min talla.”

“Cike da farin ciki, ta ce thank you so much”

“Ki yi wa Umaiman sannu”

“Za ta ji sha Allah.”

Daga haka suka yanke wayar hade da yin sallama.

Fatima ba ta kwanta ba, sai da ruwan ya kare ta cire mata sannan ta samu bacci.

Wanshekare da safe ma ita ta tsare Umaima ta sha magani sannan ta kai ta exam, ta jira ta gama sannan ta maido ta gida, inda ta kintsa musu kayansu, ta kai Umaima gidan Aunty Halima ita kuma ta dawo tasha don tafiya gida.

Ana kiran sallahr magariba mashin ya aje ta kofar gidan Mama, saboda ta san gidanta dole akwai kura, kuma ba za ta iya gyarawa a yanzu ba dai, saboda a gajiye take.

Tun daga kofar gida ta fara ganin canjin a gidan nasu, an yi modernizing din shi, har da katon gate, ba ta gama shan mamaki ba sai da ta shiga dakin Mama, inda aka hade tsohon dakin Fatima da falon Mama ya zama katon falo, aka shimfida mata tiles hade da jibga-jibgan kujeru masu numfashi, ga wasu labulaye masu kyau, ga TV plasma falo dai ya hadu kamar ba Mama ce a ciki ba.

Cike da Mamaki Fatima ta aje jakar hannunta tana fadin “Ikon Allah! Duk yaushe aka yi wannan gyaran Mama. Kin ga kuwa yadda Fallon nan ya yi kyau?” ta kai karshen maganar ta zama a kan kujera.

Cikin murmushin farin ciki Mama ta ce “tun kafin Zainab ta haihu”

“Amma shi ne ni ko labari ba a ba ni ba?”

“Yanzu da kika gani abun bai fi miki dadi ba?”

“Ya fi min wlh” ta amsa hade mikewa tana tattaba labul-bulin.

“Amma Mama waye duk ya yi wannan?”

“Ƴan’uwanki mana”

“Allah Sarki ba rabon Alhaji zai ga wannan, amma da yana da rai, ba za a buge mishi katanga a yi gate ba, na san ba zai bari ba.” cikin dariya ta karasa maganar.

“Ko ni ma sun sha fama kafin in bari ba ma shi ba.” cewar Mama lokacin da take daukar Beauty da ke kan kujera.

“Amma kuma sosai gidan ya yi kyau Mama, sun yi renovating din shi wlh kamar ba shi ba, kai komai yana son gyara, Allah Ya saka musu da alkairi, muma Allah Ya bamu ikon siya miki mota da kujerar Hajji Mama”

“Amin-amin” Mama ta amsa da sauri kafin ta ce “Idan kuma Jamilu ya riga ku duk wannan shi kenan, tun da ya ce bana sha Allah da ni za a daga zuwa kasa mai tsarki.”

Cike da farin ciki Fatima ta juya daga tabe-taben da take yi a jikin TV stand ta ce “Allah Mama. Kai ma sha Allah. Allah Ya tabbatar da alkairi.”

“Amin.” Mama ta kuma fada. Ta dora da “Ya jikin Umaiman kuma?”

“Ta ji sauki ba laifi”

“To Allah Ya kara sauki”

“Amin.” Fatima ta amsa lokaci daya kuma tana fita zuwa tsakar gida inda take ta kare ma komai kallo, don kamar gidan ne aka canja ba ki daya, duk girman tsakar gidan shimfide da interlock.

Bangaren Alhaji ma Jamil ya buge shi ya gyara shi zuwa plat daya mai kyau, wai nan zai rika zama da matarshi idan ya zo.

Karon farko da ta zo gida, ta riski farin ciki mara misultuwa.

Sai misalin karfe takwas na dare ne ta nutsu, abinci Aunty Billy ne a gabanta, tuwon Masara miyar yauki, hade da manshanu.

Mama kuwa radio ta kunna bayan tasa dole an kashe inji wai sai ta gama jin shirin iya ruwa sun kunna injin din.

“Na dauka Abujar za ki wuce ai?” cewar Mama tana kallon Fatima da ke cin tuwo.

Sai da ta dan ɓata fuska sannan ta ce “Ni fa Mama bana son Abujar nan”

“Me ya sa?” wannan karon sai da ta rage karar rediyon kadan.

“Ni dai kawai haka nan na fi son nan.”

“Kenan sai ki dawo nan ki zauna, wata na can da mijinki”

“To ai ni na fi jin dadi a nan.”

“Wani abu suka yi miki lokacin da kika je?” Mama ta tambaya da sauri bayan ta tashi zaune.

“Babu abin da suka min.”

“Kin tabbata?”

Dariya Fatima ta yi kafin ta ce “Allah babu komai, ni dai na fi son nan din ne kawai”

“Ayyawo!” cewar Mama lokaci daya kuma ta koma ta kishingida tare fadin “Na dauka wani abun suka miki ai, in sille Mustaphan tass. Don ba zai dauke ki ya kai ki can ba, kuma ya wulakanta ki. Ba zan yarda ba.”

Dariya Fatima ta kuma yi kafin ta ce “Dama ya ce wai ke ce mai tare min fada”

“Haka ya ce?” Mama ta tambaya cikin dariya.

“Eh.” ita ma Fatima ta amsa cikin dariya.

“Na yi wa Ƴan’uwanki magana a kan kawarki, sun ce wai ba lallai ta auri Jamilu ba”

Tsame hannu Fatima ta yi cikin miyar tana fadin “Me ya sa?”

“Sun ce iyayenta na da kudi sosai, kuma kin san irin yaran wannan gidan da yawansu ma Kasar waje suke aure.”

Shiru Fatima ta yi kafin ta ce “Gaskiya kam suna da kudi sosai, amma sai in ga kamar ba haka suke ba su.”

“In ji wa? Maganar aure daban maganar kawancenku daban, bare suna ganin ita kadai ce mace, don haka mu bar wannan maganar. Jiranshi nake yi ya zo, ya je ya nemi ƴar gidan Alhaji Bawa asiri rufe.”

“Wacce a ciki?” Fatima ta tambaya tana kallon Mama.

“Yusrah. Yarinya ce mai hankali, kuma ita ma karatun lafiyar nan ta yi, aiki ma take yi”

“Tana da hankali kam, ga ta kyakkyawa ita ma ba laifi.”

“To kin gani.”

Haka suka ci gaba da hira har wajen sha biyun dare sannan suka kwanta.

Tun Safe Ummi ta samu Fatima gidan Mama, don za ta taya ta gyaran gida.

Gidan Aunty Hauwa suka shiga, don ganin Zainab, a lokacin ne kuma su Hassan suka san ta zo. Yanzu kam sun gane ita ce Mamansu, tun da ta shiga gidan suke like da ita, haka tare suka taho gida, da sauran yaran da ke gidan Aunty Hauwan

Basu kammala gyaran ba sai wajen karfe biyu, daga gidan Mama aka kawo musu abinci.

Har cikin ranta tafi son zamanta Sandamu. Gidanta na Sandamu ne take jin shi nata, amma gidan Abuja ji take yi kamar na aro. Da ace Mustapha zai yarda, ita kam za ta yi zamanta a nan.

Sai da aka yi la’asar Ummi ta tasa yaran zuwa gida. Yayin da Fatima ta yi wanka, saboda Mustapha ya ce mata yana hanya.

<< Daga Karshe 57Daga Karshe 59 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×