Ya bi dukkaninsu da kallo, kafin ya juya kan Mama cikin girmamawa ya ce "Mama ina wuni?"
"Lafiya lau" ta amsa lokaci daya kuma tana shigewa cikin dakinta.
Aunty Hauwa ta katse shirun nasu da faɗin "Maman Ihsan din ta koma gidan?"
Cikin wata irin murya mai dauke da tarin damuwa ya ce "Ki bar ta kawai a gidan naki ta kwanan, goben sai ta wuce."
"A kan me za ta kwana a gidana? Shi gidan naka me ya same shi?"
"Aunty! Bana son tashin hankali, kawai ta kwana a nan din, ita ma ta ce ba za ta. . .
Thanks