Skip to content
Part 60 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Ya bi dukkaninsu da kallo, kafin ya juya kan Mama cikin girmamawa ya ce “Mama ina wuni?”

“Lafiya lau” ta amsa lokaci daya kuma tana shigewa cikin dakinta.

Aunty Hauwa ta katse shirun nasu da faɗin “Maman Ihsan din ta koma gidan?”

Cikin wata irin murya mai dauke da tarin damuwa ya ce “Ki bar ta kawai a gidan naki ta kwanan, goben sai ta wuce.”

“A kan me za ta kwana a gidana? Shi gidan naka me ya same shi?”

“Aunty! Bana son tashin hankali, kawai ta kwana a nan din, ita ma ta ce ba za ta koma gidan ba.”

“Kenan dai ya tabbata abin da Fatiman ke so shi kake yi?”

Shiru ya yi bai amsa ba, dalilin da ya sanyata dorawa.

” kenan ita yanzu Maman Ihsan din ba dama ta zo nan, ta kuma sauka a gidanka? Ita m akwai gadonta a ciki, magana ta gaskiya wannan tsarin ba zai yiwu ba. “

“Aunty!” Ya kira sunan nata a hankali sannan ya dora.

“Don Allah a bar maganar nan, Mamn Ihsan tana da damar zama a gidan can, idan ma ta ce a nan za ta zauna din-din za ta iya, yanzu abun ya zo da sarkakiya. Ita dai Fatima ta wuce zuwa gidan yanzu. “

“Ni babu inda zan je.” Cewar Fatima daga inda take tsaye.

“To ka ji” Cewar Aunty Hauwa lokaci daya kuma ta juya zuwa kofar fita.

Sai a lokacin Mama da ke daki ta yi magana “Ki wuce ki ta fi gidan ki, ke din ma wata ce za ta koroki daga gidan mijinki, ina da aka wanke ki, nan aka kai ki? To wuce ki tafi. “

Suka kalli juna a tare ita da Mustapha , kafin ta karaso inda kularta take, dukawa ta yi ta dauka hade da ficewa daga gidan, Mustapha ma ya bi bayanta, amma shi gidan Aunty Hauwa ya shiga.

Bai shigo gidan ba sai karfe tara na dare, wannan ya tabbatarwa da Fatima yana tare da Blessing, ba mamaki hakuri yake ta ba ta, sosai ran ta ya baci amma ta danne, yadda bai yi magana a kan abin da ya faru ba, haka ita ma ba ta ce mishi komai ba.

Wanshekare da safe Blessing ta koma Abuja amma ba tare da su Hana ba.

Normal suka koma rayuwarsu cikin faranta ran juna kamar komai bai faru ba, ranar Juma’a da ya cika sati biyu ya koma Abuja.

In da Fatima ke shirin komawa school ranar Sunday ko Monday, yadda bai yi mata magana a kan batun su Hana ba, haka ita ma ba ta ce komai ba, kuma ta daukarwa kanta har abada ma ba za ta ce koman ba, dama su suka dauka da kansu ba ita ta roka ba, haka idan sun ajiye su ma duk daya.

Duk da yadda take ganin canji a karatun Hana da ziyad din za ta zo ace sun ci gaba.

Ranar Juma’ar da Mustapha ya tafi wainar (masa) shinkafa ta yi da miya, wacce ta ji naman kaza.

Tun da ta gama ta aika babbar kula guda gidan Mama kafin ta iso, saboda ta san yau gidan Maman zai ta samu baki.

Bayan ta gama shiri lace army green Riga da Zane, yayin da ta shirya Beauty cikin riga yar kanti blue, ta yi kyau sosai, zaune take tana kamawa Beautyn kai da band ta tsinkayi sallama kamar ta muryar Umaima.

Da alama hatta Beauty ma ta ji kamar ta san muryar don kasake ta yi hade da kallon kofa.

Umaima ta shigo sanye cikin doguwar riga kamar dai ko wane lokaci ta nade kanta da veil din rigar.

Baki bude Fatima ta ce “Da gaske ke ce?”

Cikin dariya Umaima ta ce “Kwarai ma kuwa” ta karasa maganar hade da daga Beauty tana fadin “I missed you my Beautiful baby” ta kai karshen Maganar hade da manna ma ta kiss a gefen kumatu.

“Amma ko dazu fa mun yi waya.”Cewar Fatima har lokacin da mamaki a kan fuskar ta.

“Kawai ina son ba ki mamaki ne. “

” Kuma kin ba ni. Amma ya aka yi kika gane ke da zuwanki daya. “

“Su drivers din ba sun san hanya ba? “

“Sun sani kam”cewar Fatima tana mikewa tsaye

“Ina za ki je?” Umaima ta dakatar da ita.

“Abinci zan sawo miki”

“Ba masa da miya ba, ai na ci a can gidan Mama”

Ido Fatima ta fitar “Wai tun yaushe kika zo ne?”

“Ina nan aka shiga masallacin juma’a”

“Amma shi ne sai yanzu za ki zo wurina, ni fa kika sani ba su ba. Yau na ji ikon Allah”

Cikin dariya Umaima ta ce “Ni ma yanzu ai yar gida ce. Mama ma cewa ta yi in yi zamana za ki zo, na ga hankalinta ya tafi wani waje ne na gudo”

Suka yi dariya a tare, kafin Umaima ta ce

“Da gaske dai kin ki zuwa Abuja”

“Nan din bai yi ba ko?” Fatima ta tambaya ita ma tana bin dakin da kallo.

“Ko ban fada ba ke ma ai kin san ba hadi, a zauna a buga miki gida, a zuba miki kaya amma ki ki zama.”

“Ke ni fa Sandamu ta yi min. Kin ga dai wannan gidan ko, to har fada na yi a kansa saboda an zo shi.”

Cikin dariya Umaima ta ce “To sannu. Aike kam halinki daban. Amma ba zan iya barin wancan gidan ba, in zauna a nan. Kuma mijinki ma yana can. Kin san Allah fa kika yi sakaci matar can za ta amshe miki miji.”

“Don Allah kyale ni, ni fa kun kasa gane ni har yanzu, abin da mutane suke muhimmantar da shi ni fa bai wani cika damuna ba, bare ma in ta wani ririta shi. Ita dai da take mayyar miji ta je tai fama.”

“Uh-uh gizo!” Umaima ta fada tana nuna Fatima da yatsanta manuniya

“Da gaske koki.”

Suka yi dariya a tare kafin Fatima ta ce “Ammyn ta dawo?”

“A’a. Amma za ta dawo cikin satin nan sha Allah.”

“To Allah Ya dawo da ita lafiya.”

“Amin.” Umaima ta amsa.

Sai da suka yi la’asar sannan suka jera zuwa gidan Mama, yayin da Umaima ke dauke da Beauty a kafadarta.

A kofar gida suka hadu da Jamil hannunsa rike da Maamah, Umaima wucewa ta yi cikin gida, ita kuma Fatima ta tsaya suka gaisa, daga nan ta dakko Maamah zuwa cikin gida.

Kamar ko wane lokaci dai tsakar gidan zuriyar Mama ne, yaranta mata da jikoki, sai su Aunty Bilki.

A tsakar gidan ita ma ta zauna ba tare da ta shiga daki inda Umaima da Mama ke zaune ba, da wasu yaran.

Hirar Ya Bashir ta samu suna yi, wai yana neman wata yarinya.

“To auranta dai zai yi ko?” Fatima ta tsoma baki ko zama ba ta yi ba.

“Ya ce wai auranta zai yi.” Aunty Ayyo ta amsa.

Ta kalli inda Aunty Bilki take kwance kafin ta ce “Allah Ya yi wa Ya Bashir albarka to, zai fara rama min abin da aka yi min, shi ya sa yayyu maza akwai dadi, ai tun da aka yi min kishiya ban ki ko wace mace a duniyar nan a yi mata ba. Shi ya sa Su Ziyad su shirya duk ba mai zama da mace daya, yadda aka yi wa uwarsu kishiya dole su yi ma wasu, su ma wadancan su ji abin da na ji.”

Aunty Aisha ta ce” Ke zafin kishiya kika sani? Yaushe ma kika zauna bare ku yi kishin. Don Allah ki bar mu, mu da muke ganin tsulum, kuma mu ga tsame mu yi magana. Amma ke me kika sani.”

“To ai kuwa ni ce zan yi maganar kishiya Aunty Ayyo, ni da dole na hakura ma na bar mata mijin.”

“Wai ni maganar kawarki da Jamil ta daidaitu ne? “Aunty Aisha ta katse musu waccan hirar

“Wace kawar tawa? “

“Ta dakin Mama” Aunty Aisha ta amsa

“Me kika gani?”

“Tare suka zo.”

Cikin zaro ido Fatima ta ce “Da gaske.”

“Allah Ya sa in ga annabi haka” Aunty Sadiya ta fada hade mikewa zaune.

“Wlh ni ban sani ba, kawai dai na ganta.”

“To Allah Ya sa ma sun daidaita din, ni ina son haka.”

“Bayan Mama ta riga da ta yi magana a kan Yusra.”

Cewar Aunty Ayyo tana kallon Fatima wacce ta yi maganar.

“Ai da iya mu kawai ta yi maganar fa” Cewar Aunty Aisha

“To da sauki.” ku san hada baki suka yi wajen fada.

Daidai lokacin kuma Aunty Hauwa ta shigo. Aunty Aisha ce ta ce “Ka ga uwar Ango, uwar Amarya, kuma uwar, uwar gida, uwar zuma ki tashi da gayya sannu da shigowa Hakima. Mun kusa yi miki wannan nadin sarautar ai, Hakima babbar ce.”

“Ina wuni Aunty Hauwa?” Fatima ta katse dariyar da suke yi. Tun da abin da ya faru tsakaninsu da Blessing sai yau ne suka hadu da Aunty Hauwar.

“Ban gan shi ba.”

“Allah Ya ba ki hakuri Mamanmu, ai an ce babbar ya Uwa. Allah Ya kara miki kwarjini gidan Hakimi ki yi ta yin yadda kike so. Kamar yadda nake yi a gidan Ya Mustapha.”

Aunty Aisha da ta san abun da ya faru, dariya ta yi, ba tare da ta ce komai ba.

Aunty Hauwa ma komai ba ta ce ba, illa nufar dakin Mama da ta yi.

Ita ma Fatima bin bayanta ta yi don gaishe da Maman.
Sannan su dan kafsa, an dade ba a yi ba.

Haka suka ci gaba da hira, a yi dan karamin fada a shirya tun ba da Fatima ba, abin da yake burge Umaima , ace yawa ba shi da dadi? Ji take ina ma ace ita ma a nan gidan take, amma ita kam a gidansu kullum cikin kadaici.

Sai da aka yi isha’i sannan Fatima ta yi shirin tafiya gida, fir Umaima ta ki biyo ta, wai ga gida mai tiles yaushe za ta bi ta.

Cikin dariya Fatima ta ce “Ku yi ku gama, Abuja ce dai ban zuwa, gidana mara tiles ya fi min dadin zama.”

Sai da ta shiga gidan Aunty Hauwa wajen Zainab, sannan ta wuce gida.

Ranar Sunday suka yi shirin tafiya ita da Umaima Jamil ne zai ta fi dasu, inda Fatima ta bar Beauty a gida, Umaima kamar za ta yi kuka, ba ta so yayen ba.

Lokacin tafiyar dukkansu a baya suke, motar tsit kamar an yi mutuwa, sun kusa Daura ne Fatima ta ce “Wai haka kuka taho dunkum tun daga Katsina har Sandamu ba kwa magana.”

Jamil dai bai yi magana ba, Umaima ce ta dan murmusa.

Ta kuma cewa “Tun da ba a magana a sanya mana waka, ni wannan zama haka shiru ya ishe ni, kamar mun dakko gawa, ko gawa muka dakko masu kuka ai zasu taya mu tafiyar, ni fa ban so in ji wuri shiru.”

Nan ma Jamil bai tanka ba, har sai da ta ce “Ya Jamil don Allah ka sanya mana waka”

“Ba ni da ita.” ya amsa a taikace.

“To gaskiya ni ba za a tafi da ni a haka har Katsina shiru ba.”

Yadda ta yi maganar ne ya sa Umaima murmusawa kadan.

Yayin da Jamil ya Parker gefen hanya alamun ta fita.

Suka kalli juna da Umaima, kafin ta yunkura da zummar fita, Umaima ta rike ta tana fadin” Allah babu inda za ki je” haka su kai ta kowa, ita tana kokarin fita Umaima kuma ta hana.

Ganin abun nasu ba na kare ba ne, sai ya ja motar, idan suka hadu kamar yara haka suke.

Sun shiga cikin garin Daura Fatima ta kuma cewa “To dai a sai mana wani abu gaskiya”

Wannan karon kam sautin dariyar Umaima ya fita kadan.

Shi kuma bai ce komai ba, sai da ya isa wurin da akwai shagunan da kuma abubuwan sayarwa da yawa, ya Parker Motar hade da mika musu kudi ya ce “Ku siyo abin da kuke so”

Fatima ce ta amsa suka fita da Umaima a kan hanyarsu ne Fatima ta ce “Wai don Allah haka kuka taho kamar kurame?”

“Eh mana.” cikin dariya Umaima ta fada.

“Tsaya ma, wai ya aka yi har kuka taho tare?”

Umaima ta rike haba alamun mamaki “Ke kuwa ina ruwanki da jin kwaf.”

“Gara dai in ji kwaf din, kar ki fada min wai kun daidaita?”

“To dama ɓatawa muka yi.”

“Inyeee!” cewar Fatima tana kallon Umaima kafin ta ce,

“To ai kun yi gwari, Mama ta yi mishi mata, ni ma da na zo na samu zancen.”
Ta karasa maganar tana kallon Umaima.

Ga mamakinta Umaiman ba ta ce komai ba, kuma ta kasa gane yadda ta dauki maganar

Koda suka dawo Umaima komai da suka sawo ba ta ci ba, Fatima ce kawai take sipping din coke a hankali hade da biscuit din datebass.

Har gida ya ajiyesu hade da mika musu kudi 20k ya ce su sayi abin da zasu yi amfani da shi kafin gobe.

Daki suka shiga gyara, sai da suka gyare ko ina sannan suka yi wanka, hade da dora indomie.

Basu kwanta ba sai wajen karfe goma na dare.

Wannan semister kam, Fatima za ta iya cewa tana daya daga cikin semisters ma fi dadi a gare ta, ba ciki ba goyo, ga shi babu lectures sosai sai project.

Wannan ya ba ta damar zuwa wurin aikinta, ko wane lokaci kara gogewa take yi hade da yin suna, yanzu kam duk karshen wata suke san mata wani abu, hakan kuwa yana kara mata kwarin gwiwa sosai.

Jamil da Umaima soyayya suke, sai dai soyayya ce kamar ta kurame, shi ba ya son magana Umaima ma ba ta so.

Ba karamar dariya suke ba Fatima, musamman idan suka samu sabani, sai dai Sui ta kunci, kuma karshe kowa ya kan hakura ne ba tare da ya fadi abin da aka yi mishi ba.

Idan suka hadu, ba za ka taba cewa akwai wani abu tsakaninsu ba, ko a canjin kallo, magana ma wahala take yi musu.

Shi ya sa idan ta so tsokana sai ta ce “Wai Umaima idan kuka yi aure da Ya Jamil ya za ku rika yi?”

Ta kan ce mata “Yadda kuke yi mana.”

Idan kuma tana son ta ga Jamil ya hade fuska, idan ta shiga asibitinsu ta gan shi tare da Umaima sai ta ce “Sannunku masoya.” yanzu zai hade fuska kamar bai taba dariya ba, abin da ita kuma yake ba ta dariya sosai.

Yau Juma’a, da misalin karfe goma na safe Fatima ce tsaye ta gaban washing machine din Umaima tana wanki, yayin da Umaima ke kwance a tsakiyar katifa tana duba wani littafi da Jamil ya ba ta.

Cikin tabe baki Fatima ta ce”Soyayyarku a bayar da littafai ku kuma za ta kare. Babu wani nishadi sai dai ai ta hadaki da manyan littatafai kina karatu ni ba zan iya ba.”

Umaima ta yi dariya hade da mikewa zaune tana fadin “Wlh ni ma na gaji. Kuma yanzu sai ya yi min tambayoyi a kai”

“Uhh!” cewar Fatima hade da rike Haba alamun mamaki.

” wai don Allah kuwa kuna maganar soyayya Umaima? Irin dai yan kalaman nan na masoya”

Cikin dariya Umaima ta ce “ba ma yi fa, ko whatsapp sai mu fi sati ma bai ce min komai ba.”

“Uhhhh! Sannunku da kokari.”

” ina abin da kike bukata kenan dama, tun da ke ce kika hada .”

“Kuka dai hada kanku, lokacin da na so ku hadu ai kin haduwar kuka yi, don haka ni yanzu ba ruwana wlh.”

Shigowar kira a wayar Fatima ne ya yanke hirar tasu.

Umaima ce ta daga kiran hade da mika mata.

Ba ta yi magana ba ta sauke wayar tana fadin “Wai kin ji Ya Mustapha yana waje.”

“Ni fa dama na ji kamar karar mota wlh, karar machine din nan ne ya hana ki ji.”

“Ni ban yarda ba, amma bari in leka”cewar Fatima lokaci daya kuma tana daukar doguwar hijab din Umaima ta dora a saman daurin kirjinta.

Cike da mamaki ta karasa wurin, ya bude mata seat din kusa da shi yana fadin” Shigo mana. “

Sai da ta daidaita sannan ta ce” Na yi mamakin ganinka”

“Na yi kewarki ne.”

“Sosai ko kadan?” ta tambaya tana kallon sa.

“Bari in tabbatar miki.”
Ya yi maganar hade da murza ke din motar ya nufi kofa fita.

“Ina za ka kai ni?” cikin sauri ta tambaya.

“inda na sauka mana.”

“Innalillahi! Ya Mustapha ba dai hotel ba, ni fa ban san zuwa hotel din nan, wlh ji nake kamar ina aikata zunubi.”

Bai ce mata komai ba, illa tukinsa da yake yi.

A harabar katon hotel din ya Parker motarshi yana fadin “Let’s go.”

“ina? Ni fa zane ne kawai a kirjina”

“Daidai kenan.” ya fada yana fita daga cikin motar.

Ganin ba ta da niyyar fitowa ya sanya shi dan dukowa, “Za ki fito ko sai a dakko ki”

Cikin zunbura baki ta fito, hade da bin bayan shi. Har ga Allah ba ta son zuwa hotel din nan kamar wasu yan iska.

Yanayin yadda aka kawata dakin da sanyinshi sai ya dan sanya mata nutsuwa hade da kashe mata jiki.

Daga tsayen da take ya zare hijab din da ke jikinta, ya bi jikin nata da kallo tare da fadin “Wane mai kike shafawa ne? Kullum jikinki kyau yake yi, ko mu da muke Abujar kin fi mu kyan jiki.”

Harara kawai ta manna mishi, hakan ya sa ya yi dariya, don ya san ya kai ta karshe a bacin rai.

Ya kwanta sosai kan gadon bayan ya zare kayan jikinsa.

“Madame Bismillah.” ya yi maganar hade da nuna kusa da shi.

Ganin ba ta da niyyar zuwa ya mike hade da janyo ta, ta fada kanshi, ya shiga warware zanen jikinta yana fadin “yau sarautar ta motsa ne”

Ga mamakinsa sosai ta ba shi hadin kai, dama a gado kam baya shakkarta.

Bai bata lokaci wajen shiga wanka ba, don lokacin masallaci ya yi.

Tana daga kwance take kallon yadda yake shirya kansa cikin farin yadi cotton mai kyau.

Yana fesa turare ne ya yi mata alamar me ya faru da gira.

“Ba komai” ta amsa.

“Kodai na yi kyau ne?”

Cikin murmushi ta ce “Sosai.”

“idan na dawo za mu yi magana.”

Cikin sauri ta mike zaune “Ban gane idan ka dawo ba, nufin ka nan za ka bar ni?”

“Eh. Sai ranar Sunday za ki koma.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 59Daga Karshe 61 >>

1 thought on “Daga Karshe 60”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×