Skip to content
Part 59 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Misalin karfe biyar na yamma ya iso, duk lokacin da ta jima ba ta gan shi ba, ta kan ga ya canja a lokacin da ta sake ganin sa

Kamar yanzu ma sanye yake da shadda brown color mai haske, dinkin ya zauna a jikinsa, hularsa hade da key don motarsa rike hannunsa, daga yadda yake tafiya zai shaida ma a gajiye yake.

Shigowarsa ta yi daidai da cika tsakar gidan da kamshinsa mai dadi.

Kasancewarsa dogo sosai, kibar da ya yi sai ta kara masa kyau sosai, fatarsa a goge kamar yana kwana a cikin inji.

Ba ita kadai ce take kallon canji a jikin Mustapha ba, shi kansa yana ganin wannan canjin a tare da ita, duk lokacin da ya jima bai sanya ta a ido ba.
Musamman yanzu da take sanye cikin atamfar Quali wax dinkin riga da siket, abin da ya fi kauna ya ganta a ciki, ko wane lokaci ya ganta a shigar sai ya ga kamar ba ta haifi yara biyar ba.

Fatima doguwa ce, saboda duk tsawonshi idan suka jera yana wuce ta da kafada ne kawai, tun asali dama ba siririya ba ce, ballantana yanzu da ta kara budewa ta zama babbar mace.

Yau kam ta tare shi, hade da fadawa jikinsa, abin da ba ko wane lokaci yake samu ba, musamman idan sarautarta na ka, ko magana ma a takaice take yin ta, kuma sosai take tafiya da shi idan tana a cikin irin wannan yanayin na kasaita.

“Na gode da wannan tarbar.” ya fada hade kissing din wuyanta.

“Ka cancanta ne.”

“Bayan haka ma da alama kina cikin farin ciki.”

“Of course” ta yi maganar daidai tana zama kan cinyarsa kamar yadda ya bukata. Saboda yadda ya zauna a kan 3sitter

“And what?”
Ya yi tambayar hade da kwantar da jikinsa a jikin kujerar, sosai a gajiye yake.

“So many things Ya Mustapha, amma ma fi girma shi ne yadda na samu gidanmu.”

Ya dago daga kishingiden yana fadin “Sosai ya yi kyau, har na yi sha’awar gyara namu ni ma, matsalar ni babu mai zama da zai kula da shi. Da ace Inna na nan tabbas da na gyara” yadda ya kai karshen maganar ne, ya kashe mata jiki.

Dalilin da ya sanya ta sauke ajiyar zuciya hade da fadin “Allah Ya jaddada rahama a gare ta.”

“Amin” Ya amsa, bayan ya koma ya kwanta jikin kujerar.

Ganin yadda jikinsa ya kara mutuwa ne, ya sanya ta mikewa daga jikinsa, tana fadin “Open your eyes, I have something very special for you”

“What?” ya bude idon hade da tambayarta.

Hannunsa ta kama zuwa bedroom tana fadin “Su ma suna da yawa, da farko dai ka ji ka kamar wani Ango, saboda na tanadarma abubuwa da yawa da za ka ji kamar hakan.”

Dariya ya yi kafin ya ce “OH Really?”

“Yes of course, for the first time, I want to tell you and show you how much I missed you”

Ya dakata da tafiyar da yake yi “Serious!”

Ta dan murmusa kadan “To Ya Mustapha me ye ya rage kuma, da ya wuce cin amarcin? Semister karshe fa nake, kuma ina da wurin aiki a hannu jira kawai suke in gama karatu, and Ina da yara har biyar, Kaga ko babu komai a gabana, just kawai soyayya”

Tare suka yi dariya wacce ke nuna farin cikin da suke ciki, lokaci daya kuma ta shiga rage mishi kayan da ke jikinsa.

Zuwan Mustapha wannan karon sai ya zame mishi, zuwa ma fi dadi da abubuwan da kwakwalwa ba za ta manta ba.

A duk lokacin da yake tare da Fatima yana jin kamar ita kadai ce matarsa, idan kuma yana tare da Blessing baya iya mantawa da Fatima, ko shi kadai ne hakan ke faruwa da shi, ko kuma duk wani mai mace sama da daya ya kan tsinci kan ji haka, shi ne abin da bai sani ba.

Amma a komai baya mantawa da Fatima ba dai wata soyayya suka yi ba kafin aure ba, amma yana jin ta sosai a kirjinsa.

Wani abu da ya fahimta kuma shi ne ta fi sakin jiki gami da walwala idan tana a Sandamu fiye da lokacin da ta je Abuja. Kila ko don nan garinta ne, ko kuma ta fi sabawa da nan din oho.

Yau da ya kasance kwana biyar da zuwansa, bai taba tsammanin zai yi kwanakin ba, niyyarsa yana zuwa ya gama abin da zai yi kwana biyu su juya zuwa Abuja, amma shi kansa sai ya ji Abujar kamar takura ce, a nan din ya fi jin dadi.

Da misalin karfe daya na rana Fatima ce a kitchen tana shiryawa Mustapha abinci a kan babban tire, kamar daga sama ta ji muryar Hana tana fadin “Momy!”

Jim ta yi daga abin da take yi, kafin Hanar ta katse mata shirun da ta yi da turo kofar sashen nata.

Ta fadada fara’arta, hade da rungume Hana wacce kullum ke ta kara girma kamar ana janta.

Lokacin ne kuma Ziyad ya shigo tare da Ihsan yayin da Blessing ke bin bayansu.

Duk yadda Fatima ta so boye bacin ranta ta kasa yin hakan, don take fuskarta ta canja, wanda hakan ya haifar da mutuwar jikin Hana da katsewa Ziyad hanzari wanda dama bai karaso ba.

Ita ma Blessing canja fuska ta yi hade da juyawa ta koma baya zuwa dakin Inna wanda aka gyara mata a matsayin dakin saukarta idan ta zo.

Cike da takaici Fatima ta wuce zuwa daki, yayin da su Ziyad ke bin bayan ta jiki a, mace, saboda Beauty dasu Hassan suna gidan Aunty Ayyo.

Ta kasa fahimtar me Blessing ke nufi, da duk lokacin da Mustapha zai zo wajenta ya yi kwanaki sai ta tayar da hankalinta, ko ta rika damun shi ya dawo, to ita din ba mace ba ce, da zai shafe watanni a wajen Blessing din kuma ba ta damun shi, ya kamata ta taka ma wannan matar burki a wannan karon, ta nuna mata ita ma mace da ke bukatar mijinta a kusa da ita. Ta nuna mata ba ita kadai ce ta san dadin miji ba.
Sannan ta cire mata sha’awar biyo Mustapha a duk lokacin da ya zo wajen ta.

Tana tsaka da tunanin ne Mustapha ya shigo, cike da mamaki yake kallon su Hana, wadanda suka taso zuwa jikinsa , yana shafa kan Ziyad ya ce “Yaushe kuka zo?”

“Yanzu.”
Ziyad ya ba shi amsa.

“Tare da Auntynku?” ya kuma tambaya yana kallon Hana.

“Eh.” ta amsa hade da daga kanta sama.

A lokacin ne ya kalli inda Fatima take zaune, fuska kicin-kicin. Kamar yaki ya riga ta kofar gida.

Ganin ta mike zuwa bedroom sai ya bi bayanta, yayin da su Hana suka tsaya tsakiyar falon jiki a sanyaye.

“Ya Mustapha ba na son abin da kuke min?”

“Me muka yi miki?” shi ma ya tambaya da yanayin da ke nuna bai san me suka yi mata din ba.

“A cikin watanni hudu, kana kasancewa dani ne a kwanaki da basu fi sati biyu ba, to me ya sa a kwanakin sai ka kanga ni da wata. Ka san kana son ganin ta me ya sa ba ka tafi ba, sai ka kira ta zuwa nan, and you know I hate this” cike da bacin rai ta yi maganar ganin ya shigo cikin bedroom din sosai.

“Me kike son cewa?”

“Ina son fada ma ne, ni ba a yi min adalci, kuma ba na son kana hadani da matarka, tun da har yanzu ba ka gane hakan ba, don Allah ku bar ni in rayu cikin sauki mana.”

“Ah-ah! To hakan ya nufin Maman Ihsan ba za ta zo nan ba kenan .” ya yi maganar idanunsa a kanta.

“Yana nufin ta zo, amma ba a kwanakin girkina ba, me ya sa ba za ta zo lokacin da kake Abujar ba, ina nufin ta baro ka ta zo ta zauna a nan din. Sai lokacin da ta ga na zo, sannan ta kwaso jiki ta biyo ka, idan ma da sanenka ta zo, to ta zo wa banza wlh, saboda za ta rika hangen ka ne kawai idan za ka shiga ko za ka fita. Duk lokacin da ka baro Abuja ka zo Sandamu wannan yana nufin ranar girkina ne. Saboda haka ba zan raba shi da wata ba.”

Shiru ya yi yana kallon yadda take mayar da numfashi alamun ranta a bace yake sosai.

Ta dora da” Ita kadai ce ta san dadin miji ne? Yan kwanakin da kake zuwa kana min shi ne batta iya jurewa sai ta biyo ka, ta zo ta ga yadda nake rayuwata, ni ina shiga rayuwarta ne? “
Jin ta yi shiru tana mayar da numfashi a harzuke. Ya sanya shi juyawa zuwa wurin Blessing.

Zaune ya iske ta, ta tasa Ihsan gaba, yayin da fuskarta take a hade.

” Me ya sa za ki taho without my knowing “

“Because I’m tired Dadyn Hana.”

“Tired for what?” ya tambaya bayan ya kafe ta da ido.

“Na yadda kake mantawa da ni, a duk lokacin da ba ma tare”

“Na manta da ke kuma? Me kika rasa a can din? Ci ko sha, me ye babu a gidan?”

“Sune kawai nake bukata?” ta tambaya a harzuke.

Murmushi ya subuce mishi kafin ya ce “Yanzu ke idan an ce ina mantawa da ke sai ki yarda, mutane aka tara fa, daga nan har Maiduguri aka daura mana aure, and ina da yarinya tare da ke, ta ya zan manta da ke?”

“Yanzu da ka ganni ka tuna wannan, amma yaushe rabon da ka daga waya ka kira ni, sai dai ko idan ka ga missed call dina, ko wata bukata taka ta kanka.”

“So shi ne za ki taho, ki tayar min da hankali?”

Ganin ta yi shiru ba ta amsa ba ya dora “Abu ma fi soyuwa a wurina shi ne in ganku cikin farin ciki, ina bakin kokarina wurin ganin na yi adalci a tsakaninku, daga lokacin da na aure ki zuwa yanzu ku san shekaru uku kenan, za ki iya kirge kwanakin da na yi tare da Fatima, saboda kaso 95% cikin dari ina tare da ke ne. Kuma da kike korafin na fi kiranta idan ina tare da ke ko kuma nuna kulawata a kanta. Me kike so? Ba Ta tare da ni, abun da nake ci ya bambanta da nata, inda nake bacci ya bambanta da nata, ta bar yaranta ta hakura da zama kusa da ni, tana can tana karatu, karatun da na yi mata alkawarin tsayawa da kafafuna sai ta yi. Ni da kaina na san ban hidimtawa karatunta ba, kamar yadda na yi alkawari. Ke kuma kina tare da ni, hade da samun kulawa ta, shi ne kuma dan kiran da nake mata a waya ya tsone miki ido. Wane irin son kai ne wannan? . Me na tanadar mata na debe mata kewata, da ya wuce kiran? Ke ga shi nan ma kwana biyar kin kasa jurewa, kina fadin an manta da ke, a nan za ki gane ta yi matukar juriya na kwashe kwanakin da take yi, kuma ta san ina tare da ke.”

Shiru ta yi hade da nazarin kalamanshi, da gaske kamar ba ta kyauta ba, amma ta kasa mallakar zuciyarta ne, tana da kishi sosai, wanda idan ya motsa dole sai ta yi abin da daga baya za ta yi danasani, ita ba kamar Fatima ba ce da ta iya share abu kamar ba ta damu ba. Kuma ya kamata ya san haka. Ya gane bambancinsu ita ba ta da hakuri a kansa

“Ke ce kike ganin kullum ina kiranta, amma a zahiri ba haka ba ne, wlh na kan yi kwana biyu ma ban kira ta ba, ya kamata ki nutsu ki daina kawo abin da zai kawo mana tashin hankali muna zaman lafiya.”

Hannu ta kai hade da dauke hawayenta, ba tare da ta ce komai ba, dalilin da ya sanya shi fita zuwa dakin Fatima.

A lokacin zaune take kan kujera a falo, da alama su Hana sun fice, ya duka hade da daukar tiren abincin da ke tsakiyar falon.

” Ina za ka kai?” ta yi tambayar hade da kallon sa.

“Zan kai wa Maman Ihsan ne.”

“Aje min, ni ban girka da ita ba.”

Tsaye ya yi rike da farantin yana kallon ta, dalilin da ya sanya ta mikewa tsaye “Ka aje min, wlh cin abincin nan daidai yake da tashin hankalin kowa a gidan nan”

“Fatima!” ya kirata

Ba ta amsa ba, sai dai ta zuba mishi idanunta. Masu cike da bacin rai.

“Kuna son ku kure hakurina.” ya yi maganar cikin bacin rai.

“Ni ma hakurin nawa aka kure Ya Mustapha, kwanciyar hankali kowa shi ne matar nan ta koma inda ta fito.”

“A kan me? Kar ki manta nan gidana ne, kuma dukkanku matana ne, ko wacce tana da ƴancin zama a inda take so, and kar ki manta ni ne mai tsarawa ba ke ba.

“To shi kenan. Ta zauna ni kuma zan tafi, saboda ba zan zauna da ita ba.”

Ta yi maganar hade da juyawa zuwa bedroom, yayin da Mustapha ya bi bayanta da kallo cike da mamakin abin da ke faruwa, cikin mintuna talatin kowa ranshi ya baci, kai mata matsalolinsu yawa ne dasu.”

Ya kai karshen maganar zucin na shi hade da nufar dakin Blessing rike da tiren a hannunsa.

Har lokacin kuka take yi, yayin da Ihsan ke zaune a gefen katifa cikin rashin kuzari.

” Ki ci abinci mu je gidan Aunty Hauwa. Kuma ba na son wata magana mara dadi ta shiga tsakaninki da Fatima.”

Ya yi maganar hade da aje tiren da ke hannunsa.

Daidai lokacin kuma Fatima ta shigo hade da dukawa ta dauke tiren, bangaje Mustapha ta yi yayin da take fita.

Ya bi bayanta da kallo cike da mamakinta.” Abun ya girmama ” ta fada a zuciyar sa.

Kaf abincin ta juye a cikin katuwar kula ta wuce gidan Mama.

Aunty Aisha ce tsaye a tsakar gidan sai Mama dake daki tana tattare shara, magana suke yi, shigowar Fatiman ce ta katse su.

Ganin yadda ta shigo ne ya sanya Aunty Aisha fadin “To! Lafiya?”

“Da sauki dai.” cewar Fatima hade da aje kular a tsakar gida ta zauna a kai.

Mama ta fito hannunta rike da tsintsiya tana fadin “To me ya faru?”

Cike da bacin rai ta ce “Ni da Ya Mustapha ne da kuma matarshi”

“Wace matar kuma?” cewar Mama tana kallon ta.

“Matarshi mana”

“Yo ke a ina kika ganta?”
Aunty Aisha ta yi tambayar cike da mamaki.

Kwashe abin da ya faru Fatima ta yi ta fada masu kafin ta dora da “Ni kuma wlh Ya Mustapha zai ga danyen kaina, idan har matar nan tana gidan nan ba zan koma ba”

“Uhhh! Abun naku Azeemun ne. To yanzu dai duk ba wannan ba, abincin ne kika juyo a cikin wannan kular?” Aunty Aisha ta yi maganar hade da nuna kular.

Da kwarin gwiwarta ta ce “Shi ne, don wlh ba za ta ci shi ba.”

Aunty Aisha ta juya kan Mama da ke rike da tsintsiya tana jin su hade da kallonsu ta ce “Kin ji fa inda ake abun Mama, yaji da kular abinci, don Allah ana haka yaushe za ka hana mutum tahowa.”

Mama dai ba ta ce komai ba, illa bin Aunty Aisha da kallo da ta yi , wacce ta shiga kitchen hade da dakko plate.

“Fatima dan tashi in diba, da fatan dai kin zubo har da naman”

“Duka na juyo shi.” cewar Fatima lokacin da ta mike hade da budewa Aunty Aisha kular.

“Uhhh! To ban da dai ba abu mai kyau ba ne, Fatima ai da na ce duk ranar da za ki kara yi yajin ki taho gidana” Aunty Aisha ta fada lokacin da take yagar tsokar naman kaza fara sol.

“Anya Aisha kina da lafiya kuwa?” cewar Mama tana kallon Aunty Aisha.

Cikin dariya ta ce “Ƙalau nake, to fadan masoya me za ka ce, ba gara ma in ci abincina in more ba, su kuma sui fama. Fatima da Mustapha ne fa. Tabbb wanda ya shiga ma ya ji kunya, gara ma ki kyale su Mama. Na ki ido “

Daidai lokacin Aunty Hauwa ta shigo a fusace tana fadin “Ina Fatima din?”

“Ga ni.” Fatima ta amsa daga zaunen da take.

“To sannu isasshiya.”

“Me na yi?”

“Ban sani ba.” Aunty Hauwa ta fada a fusace, ta kuma dorawa

“Ta ya za ki hana mata zuwa wurin mijinta? Haka ake yi?”

“Haka suka ce miki?” Fatima ta tambaya tana kallon Aunty Hauwa.

“To karya aka yi miki. Tun asali ubanwa ya ce ki sakar mata miji, tun da ke ba ki iya kula da shi ba, ba sai a nuna miki yadda ake yi ba. Yanzu kuma ba ki isa ki dagawa mutane hankali ba, a kan wani dalili naki na banza. Blessing matar Mustapha ce, da Abuja da Sandamu duk gidan Mustapha ne, don haka Blessing tana da damar zuwa a duk lokacin da take so. Ke ba ki isa ki shata mata layi ba. “

” Ikon Allah! ” cewar Aunty Aisha bayan ta mayar da hankalinta a kan cin abincinta.

“To ba shi ya sa na bar musu gidan ba, me ye kuma na za a biyo ni gidan ubana.”

“A toh!” Aunty Aisha ta kuma fada.

Harara Aunty Hauwa ta aika mata kafin ta juya kan Fatima tana fadin “To da kika baro gidan wa kika yi ma wa?”

Jin Fatima ba ta amsa ba ya sa Aunty Hauwar dorawa “Idan ban da iskanci yarinya nata bin ki kamar ke ce uwarta, ta rike miki yara ba kyara ba tsangwama, amma kina neman zubar da mutuncinki a idonta.”

“To yara ni na ce ta rike? Ba fa taimakona ta yi ba, kuma ba don ni ta yi ba, don mijinta ta yi, idan don ni ce kar ta kara komawa dasu, ta bar min abuna, ba ga ku ba, ai kun rike min. Kuma maganar tana bi na Aunty Hauwa, ke ma fa ana bin nan naki, gidan Hakimi waye bai bin ki, har Hakimin ma bin ki yake yi, tun da abin da kika ce shi ake yi. Aunty A’in ai sau da kafa take bin ki. “

Dariya sosai Aunty Aisha ta fashe da ita, Mama dai jin su take yi, uffan ba ta ce ba.

” Ta shi ki wuce gidanki. Mara kunyar banza” Aunty Hauwa ta yi maganar cikin bayar da umarni.

” Ai na fadawa Ya Mustaphan ba zan koma ba, muddin akwai wannan matar a gidan. “

” To kuma ba za ki zauna a nan ba don ubanki, tun da ke babu wanda ya isa ya sanyaki”

Cikin kasa da murya ta ce “Ni da gidan ubana, wa ya isa ya, kore ni”

A harzuke Aunty Hauwa ta yi kanta, hakan ya sa ta mike a guje.

Mama da ke tsaye ta ce “Me ye na bugu kuma? Ba gidan Mustapha ba ne, to ta ce ba za ta koma ba, me ye na ki na jin haushi tun da wacce kike so da shi ga ta can a gidan.”

Sororo Aunty Hauwa ta yi tana kallon Mama kafin ta ce “Mama goya mata baya za ki yi.”

“Eh.” Mama ta amsa kai tsaye.

Aunty Aisha ta mike hade da tuntsurewa da dariya tana fadin “Gidanmu gidan shagali”

“Amma Mama kin san dai abin da Fatima take yi ba daidai ba ne ba ko?” cike da bacin rai Aunty Hauwa ta yi maganar.

“Ni ban sani ba.” Mama ta kuma amsawa.

Aunty Aisha ta kuma tuntsirewa da dariya daidai tana wanke hannunta.

Cike da jin haushi Aunty Hauwa ta juya kanta tana fadin “Wlh ranki zai yi mugun baci, ubanwa kike wa dariya?”

Cikin kumshe dariyarta ta ce “Allah Ya ba ki hakuri uwar Amarya, uwar Ango kuma uwar, uwar gida, ni kin ga ma, tafiya ta. Fatima na ce miki dai next time idan za ki yi yajin ki taho gidana ko? To kar ki manta don Allah” ta kai karshen maganar cikin dariya hade da ficewa daga gidan.

Daidai lokacin kuma Mustapha ya shigo.

<< Daga Karshe 58Daga Karshe 60 >>

2 thoughts on “Daga Karshe 59”

  1. Abin da mama take yi I don’t think is right, ya kamata tana dubawa tana wa Fatima maganan gaskiya, Ina goyon bayan Fatima din wannan karan amma dai ya kamata mama na fahimtar da ita kurakuran ta kuma ta sahirta wa Mustafa.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.