Skip to content
Part 61 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Cike da mamaki take bin sa da kallo har ya fice.

Bayan fitarsa ne ta mike zuwa toilet, wanka ta yi hade da yin alwala.

Zanen da ta zo da shi ba ta yarda da tsarkinsa ba, shi ya sa ta dakko jallabiyarsa ta zura, hade da sallahya don gabatar da sallahr azhur.

Tana kan sallahyar ne, aka kwankwasa mata kofa, shiru ta yi ba tare da ta mike zuwa wurin kofar ba, ko yin magana.
Ita tsoro ma take ji, waye zai kwankwasa kofar bayan Mustapha ya tafi masallaci, kada ta bude wani katon ya fado mata, ta bani ta shiga uku.

Wayar da ke gefen gadon ce ta katse mata tunanin da take yi, cike da mamaki take kallon wayar, to waye kuma yake kiran wayar? Waye ya santa a nan da zai bugo mata waya.

Ganin ta ki daina karar ne ya sanyata daukar kan wayar hade da sallama.

Daga can aka amsa sallamar tare da sanar mata, ga abinci nan za a kawo mata.

“OK.” ta fada hade da komawa inda take. A zuciyarta tana fadin ikon Allah masu kudi na jin dadi fa.

Kan sallahyar ta koma ta zauna, ta saba duk ranar Juma’a tana karanta suratul-kahfi, yau da ba ta karanta ba, ji take yi kamar ta yi zunubi, to ba waya ba alkur’ani.

Kwankwasa kofar ya kuma daga ta, mika hannu ta yi hade da karbar babban tiren da mutum din yake miko mata bayan ta bude kofar.

A kan dankaramin tebur din da ke dakin ta ajiye hade da bude duk bowl ko plate da aka yi wrapping.

Jinjina kai ta yi hade bin komai da kallo, akwai fried rice wacce ta ji kayan hadi da pepechickens a sama ga kuma hadin coslow a gefe, akwai pepesoup na bindin saniya, don komai akwai sunanshi a jikin yar papern da ke danne a kasan kwanon.

Dan karamin fridge din ta buda inda ta ga Mustapha ya dakko ruwa, ruwan ne a jere hade da minerals sai fruit dangin kankana, lemu, apple, gwanda da ayaba.

Cikin ranta ta ce “Su ma duk a nan ake samunsu ko mutum ke zuwa da abun sa?”

Coke din ta dauko hade da zama a tsakiyar gadon, sosai ta ci abincinta ta dora da coke hade da ruwa. Abin da zai lalace irin coslow ta sanya shi a fridge.

Jallabiyar ta cire hade da mayar da zanenta, ta kwanta a kan bangajejen gadon.

Tun tana kallon TV har bacci ya dauke ta.

Kiran sallahr la’asar ya tashe ta.

Rigar Mustapha ta kuma sanyawa ta yi sallahr.

Ta idar da Azkhar din yamma ta kwanta cike da mutuwar jiki, har ga Allah zaman kuma ya ishe ta, ga ba waya a hannunta Mustapha kuma shiru kamar an aiki loma zagayar wuya.

Biyar saura ta ji ana kwankwasa kofa, zuwa yanzu kam ta gane kwankwasa kofar ba wai dole sai wanda ya san ka ba, ma’aikatan hotel din ma suna kwankwasawa domin isar da sako.

Dalilin da ya sanyata mikewa ta nufi kofar “Waye?” ta tambaya bayan ta rike handle din.

Daga can waje Mustapha ya ce “Nine bude.”

Ya shigo yana kallon yadda Jallabiyar tashi tayi mata kyau hade da yi mata daidai, duk dai shi ba ta saukar mishi kamar yadda ta saukar mata ba.

“Fatima kina da tsawo fa, kalli yadda rigar nan ta yi miki.”

Ba ta tanka shi ba, gefen gadon ta zauna, tana kallon yadda yake rage kayan jikinsa.

“I’m sorry na bar ki ke dai.” ya yi maganar hade da zama kusa da ita yana janyota jikinsa sosai.

“Ba a kawo abinci ba?”

“an kawo.” ta amsa a hankali, hade da mikewa ta tattara mishi komai gaban shi.

“Kin ci ai” ya yi tambayar lokacin da yake matsowa sosai kusa da tebur din.

Kai ta daga alamar eh.

Ya fara cin abinci da Bismillah, yayin da Fatima ke kallon TV

Sai da ya ƙoshi sannan ya shiga toilet.

Bayan ya fito ne, ya kuma nufar ta da kansa ya cire mata rigar, ya shiga sarrafata yadda yake so.

Bayan ya dawo cikin nutsuwarshi ne ta ce “Wai abun da ya kawo mu nan Kenan?”

Cikin dariya ya ce “Eh mana. Ba da bakinki kika ce yanzu ba sauran komai sai soyayya ba. Ita na zo mu yi.”

Shiru ta yi kamar ba za ta ce komai ba, sai kuma ta ce “To ni yaushe zan tafi, ban taho da ko wayata ba, kuma wanki nake yi ma, sannan na baro Umaima ita kadai, babu dadi.”

Ya janyota jikinsa,”Ba na ce miki sai Sunday ko Monday ba. Kuma Umaima mijinta ya je ya dauke ta.”

A shagwabe ta shiga kokarin janye jikinta tare da fadin “Ni ba zan zauna a nan ba har wannan lokacin, kamar wata yar bariki.”

Ya matse ta gam a jikinsa yana fadin “To sai ki tafi in gani. Da sunanki na kama dakin, har da hotonki, kuma na ce sai ranar da zan tafi za a biya kudin. Kina fita zasu rike ki, su ce za ki gudar musu da kudinsu.”

Dagowa ta yi da sauri, tsoro ya bayyana a kan fuskarta, “Amma me ya sa za ka min haka. Kama daki da sunana, kuma har da hotona, idan wanda ya sanni ya gani fa.”

“Sai ki yi mishi bayani mana.”

Ta yi shiru tana jimamin abun, yayin da Mustapha ya kuma mayar dasu ruwa.

Sai da aka kira magariba ne ta samu kanta dakyar, shi ma ya tafi masallaci.

Bai dawo ba sai da aka yi sallahr isha’i, zuwa lokacin kuwa har an kawo musu abincin dare, shi Fatima ma ke ci.

Shi ma sai ya zauna suka ci gaba da ci tare.

Ya katse shirunsu da fadin “Kin san me ke faruwa?”

Girgiza kai ta yi alamar a’a

“Jamil ne ya kira ni, in ga wasu filaye da ake yankawa ko zan saya. Shi ya sa da aka sakko masallaci ban dawo ba. Na wuce can wurin. Filayen sun yi kyau da kuma saukin kudi, gasu kuma awon gwamnati ne, an fitar da centers sosai da hanyar ruwa.”

Kallon sa kawai take alamun tana sauraro.

“So shi ne nake son in tambaye ki, tsakanin Katsina, Sandamu da Abuja ina kike son zama? Idan Abujan ne kuma ba kya son zama da Maman Ihsan sai in yi miki naki ginin, duk da zai dau lokaci gaskiya. Idan kuma za ki zauna da ita, sai mu sayi wannan filin mu ajiye, a matsayin kadara. Idan kuma za ki zauna a Katsinan zan gina miki, idan kuma Sandamun kike son zama zan gyara miki wancan gidan irin ginin da kike so. “

Ba tare da dogon na zari ba ta ce” Zan zauna a Katsina, amma zan rika zuwa Sandamu hutu. “

Ya bi ta da kallon mamaki, ya dauka za ta ce Abuja amma gidanta daban, yanzu kam ya fahimci zaman Abuja ne ba ta so, ya kuma kara fahimtar soyayyarta da Sandamu, bayan ta zabi Katsinan dole kuma sai da ta jeho Sandamu.

“To me ya sa kika zabi Katsinan, ba kya son zama kusa da nine?”

Shiru ta yi hade da nazarin maganarsa, ba ta yi tsammanin zai yi mata wannan tambayar ba.
Cikin yanayin sanyin jiki ta ce “Ina so.”

“Amma kuma ba ki zabi kusa da ni din ba.”

“Ban taba tsammanin akwai ranar da za ta zo, in zabi yin nesa da kai ba, a yanzu da muke haka, sai nake jin ina ma mutabbata a haka har karshen rayuwa. Kila ba ka taba jin na furta kalmar So a gare ka ba, amma ina sonka Ya Mustapha, son da ban taba yi ma wani namiji ba”

Ya zuba mata ido, kalamanta sun ratsa ko wane lungu da sako na jikinsa. Ya tsame hannunsa daga cikin miyar egusin yana fadin “Kuma dai kin zabi nesa da ni, ina son yake a nan, abin da kake so, za ka so kasancewa da shi ko wane lokaci. “

“Ina da kishi sosai a kanka, zuciyata ba ta iya jure ganin ina shiga wurinka wata na fita, ni kadai na san irin ciwon da nake ji, shi ya sa na fi son yin nesa, ya fi min dadi ka zo, mu rayu na kwanaki ba tare da ina ganin wata na shiga da kuma fita tsakaninmu ba.”

Ya kafe ta da ido, kamar tana ba shi darasi. Dalilin da ya sanya ta dauke idonta, wanda ya cika da hawaye, tausayin kanta take ji, ta yadda wata ta sanyata nesanta kanta da abun da take so.

Tissue ya yago, hade da goge musu hannayensu, kafin ya ja ta zuwa toilet ya tara hannayenta a fanfon da ya bude, sai da ya wanke hannayen su tas, sannan ya sakar mata nata, yayin da zuwa lokacin hawayen sun fara zirya a kan fuskarta.

Kafadunta biyun ya dafa suna fuskantar juna “Kina kishina da gaske?”

Kai ta daga alamar eh.

Ya shiga dauke mata hawayen da hannunsa yana fadin “Wannan hawayen kishina ne kike zubarwa Fatima? Su din masu tsada ne, ban taba tunanin na kai haka a zuciyarki ba. Na dauka kina zaune da nine kawai saboda yaranki, kasancewar ba kya nuna damuwarki a kan komai da ya shafe ni. Rashin nuna damuwarki a kan komai nawa yana tayar min da hankali, in ji kamar ni din ba ni da wani muhimmanci a gare ki. Da gaske kina kishina, wannan hawayen kina zubar dasu ne don kishina?”

Kai ta kuma dagawa alamar eh.

“wannan rana ce da ba za ta gushe a zuciyata ba” ƴa yi maganar a hankali hade da janyota jikinsa ya rungume sosai, kamar wani zai kwace ta.

“Ina sonki Fatima, ban taba jin son wata diya mace kamar ke ba, kila shi ya sa abokiyar zamanki kullum take ganin ba na yi mata adalci, abin da kike so shi nake yi. Ni kaina na tsinci kaina a haka ne, duk abin da kike so muddin bai sabawa addini ko al’adaba koda zan cutu shi nake so. Idan ba kya kusa da ni, komai nake tunaninki yana a kirjina. Ina tsoron kar hakan ya kai ni wuta, na yadda na kasa daidaita sonku a zuciyata ke da ƴar’uwarki, bayan tana min komai na kyautatawa” ya dan tsahirta kadan

“Shi ya sa na tambayi wani malami a kan hakan, sai ya ce min yana faruwa a kan ko wane namiji mai mace sama da daya, in dai tabbatar ina boyewa hade da yin adalci a tsakaninku. Boyewar ma wani lokaci banna iyawa har sai ta gane, kwanaki can da ta taso ni gaba a kan bana mata adalci, na so in sauwake mata, saboda ni da kaina na san wani lokacin bana mata adalcin.”

Suka sauke ajiyar zuciya a tare cikin mutuwar jiki ta ce” Ba za ka rabu da ita ba, tana da hankali game da kawaici, ita din sa’a ta ce, samun abokiyar zama irin ta akwai wahala, tana kokarin danne kishinta, ta rike min yara ba tare da cutarwa ba, ka daina biye min a komai.”

Ya janyeta daga jikinsa hade da zuba mata ido.” Zan gwada, idan zuciyata za ta iya. “

Daga haka ya janyota zuwa bisa gadon, suka kuma fadawa cikin duniyar masoya.

Kamar wasa Fatima sai ranar Sunday ta koma gida da misalin karfe biyar na yamma, saboda Mustapha Sandamu ya wuce, ba ta taba tsammanin za ta ji dadin kwanakin ba, har sai ta ji.

Kamar kar su wuce.

Lokacin da koma Umaima ba ta nan, dama ta san ba za ta zauna ba, cikin fulawar da suke boye key ta duba, sai kuwa ga keys din gaba daya Har da na dakin Umaima.

Dakinta ta fara shiga komai tsaf, kafin ta koma dakin Umaima, wayarta ta samu kasan filo, ganinta a kashe sai ta kunna.

Bayan komai na kan wayar ya daidaita Mama ta fara kira, bayan korafin Mama a kan an kira wayar a kashe, ta shaida mata an tura tambayar auran Umaima Bauchi wajen dangin Babanta. Kuma da alama sun amince da shi.

Cike da ihu ta ce “Da gaske Mama, Allah ubangiji ya tabbatar da alkairi.”

“Amin” Mama ta amsa.

Kafin Fatima ta ce wani abu, ta ji ihun Beauty da Maamah, da alama fada suke yi, don tana jiyo Mama na fadin “Maamah, ba ta takalminta, ba na ki ba ne.”

Jin haka ya sa Fatima yanke wayar ta kira Umaima

“Kun gama Honeymoon din?” cike da tsokana Umaima ta tambaya.

“Eh mun gama yaushe za ku je naku?”

Cikin kasa da murya Umaima ta ce “Yana jin ki wlh.”

Ita ma cikin kasa da muryar ta ce “Haba don Allah, kuna tare ne?”

“Eh. Yanzu ya shigo Zai maido ni gida ne.”

“To sai kun kara so.”

“To.” Umaima ta amsa hade da yanke wayar

Kan katifa ta fada cike da farin ciki, kwanakin abubuwa masu dadi ne suke faruwa da ita.

Data ta bude hade da shiga whatsapp, wannan ne ya dauke mata hankali, jin karar shigowar motarsu ne ya sanyata mikewa cikin sauri.

Fitar ta yi daidai da fitowar Umaima daga front seat, yau kam riga da siket din atamfa ne a jikinta, hade da dogon hijab ash color haka ma takalmin kafarta ash ne flat.

Duk abin da ta fito da niyyar fada sai ya bace mata, saboda yadda ta gansu, kamar basu da kuzari, ga kwarjini da Jamil din ya yi mata. haka ta karaso a nutse, lokacin kayan Umaima yake fitarwa daga boot din mota.

“Ya Jamil ina wuni?”

Bai Kalle ta ba ya amsa da “Lafiya.”

“Allah Ya sanya alkairi, Ya kuma nuna mana lokacin.”

Ta dauka ba zai amsa ba, ga mamakinta sai ya amsa da “Amin.”

Umaima ce dai uffan ba ta ce ba, illa daukar jakarta da ta yi zuwa daki, shi kuma ya koma cikin motar.

“Kun yi waya da Mama ne?” ya tambaya, bayan ya daidaita zaman shi.

Ita ma karasowa ta yi sosai kusa da shi hade da amsa mishi tambayarshi “Eh mun yi”

“Me ta ce miki?”

“Ta ce an tafi Bauchi, tambayar auran Umaima, kuma da alama an bamu.”

Ya dan yi shiru kamar yana son yin wata maganar.

Dalilin da ya sa ta ce “Akwai wani abu ne?”

“Har yanzu hankalinta bai kwanta da maganar auran nan ba.”

“Me ya sa?” cikin sauri ta tambaya

“I think kin san dalilin.”
Ya yi maganar yana kallon ta.

Ta dan yi shiru kafin ta ce “Kun yi magana da Aunty Lami ne ko Aunty Hauwa?”

“Eh.” Ya amsa mata

“To sun fada ma Mama ta dauka da zafi, kamar lokacin aurena da Ya Mustapha.”

Girgiza kai ya shiga yi alamar a’a.”

Tsayuwarta ta gyara tana fadin “To kuma, da kanta fa ta kira ni tana shaida min abin da ke faruwa. Kuma ni ina ganin dalilinta da take kallo ba zai kawo matsalaba, ko kana ganin zai kawo? “

“Ke zan tambaya ai, tun da ke ce kika santa sosai.”

“Ni bana jin wancan dalilin zai zama matsala, kuma na fadawa Maman ma tun a lokacin.”

Ya gyara zaman shi tare da fadin “Kowa yana fadin yanayin gidansu yarinyar nan, da irin tarbar da aka yi musu jiya, suna ganin kamar dai bamu aje ƙwarya a burminta ba.”

“Ya Jamil idan suna ganin ƴarsu ta fi karfinmu, to bana jin zasu karbe mu, har ma su sanya ranar biki ai.”

“Ba sune abun ji ba, yarinyar ce, saboda ba lallai ta samu abin da take samu a gidansu ba a wajena, da ban damu ba, amma yadda mutane suke ta magana daga jiya zuwa yau, na ji jikina ya mutu”

Daga yadda ya yi maganar ta tabbata har cikin zuciyarsa haka abun yake.

Da alama abun na damun shi sosai, kuma ba ta jin zai iya tattauna maganar da kowa, gara ma Aunty Lami kila.

“Sha Allah komai ba zai faru ba, Umaima za ta yi hak’uri da duk yadda ta same ka, matukar za ka nuna mata kulawa, na tabbata za ka gasgatani bayan auran, ita din mutuniyar kirki ce.”

Shiru ya yi kafin ya dage kafadunsa du biyun sama.

A hankali ya juya kan motar yana fadin “Sai da safe.”

Ita ma tsaye ta yi a wurin, ba za ta iya cewa ga abin da take tunani ba, ta jima a wurin, kafin ta koma daki wurin Umaima.

<< Daga Karshe 60Daga Karshe 62 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×