Lokacin da ta shigo dakin Umaima zaune take a tsakiyar katifa, tana latsa wayarta.
Shigowar Fatiman ne ya dakatar da ita.
Suka zubawa juna ido , har sai da Fatima ta janye nata tare fadin "Lafiya?"
"Me Jamil ke fada miki?"
Cikin rike haba ta ce "Ikon Allah! Ɗan'uwana ne fa, au maganar tamu ma sai kin ji?"
Umaima ta mike tsaye "Please keep joke aside."
"Ba ruwanki." Cewar Fatima hade da shiga dakin sosai
"Kin san wani abu?" Umaima ta tambaya hade da mikewa tsaye.
"Sai kin fada."
Cewar Fatima tana kallon ta
"Jamil dan'uwanki ne. . .