Skip to content
Part 62 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Lokacin da ta shigo dakin Umaima zaune take a tsakiyar katifa, tana latsa wayarta. 

Shigowar Fatiman ne ya dakatar da ita. 

Suka zubawa juna ido , har sai da Fatima ta janye nata tare fadin “Lafiya?”

“Me Jamil ke fada miki?”

Cikin rike haba ta ce “Ikon Allah! Ɗan’uwana ne fa, au maganar tamu ma sai kin ji?”

Umaima ta mike tsaye “Please keep joke aside.”

“Ba ruwanki.” Cewar Fatima hade da shiga dakin sosai

“Kin san wani abu?” Umaima ta tambaya hade da mikewa tsaye.

“Sai kin fada.”

Cewar Fatima tana kallon ta

“Jamil dan’uwanki ne, ni kuma kawar ki ce ta amana, ina da kawaye tabbas, amma ban taba jin na damu da wata kamar ke ba. Don Allah ina rokonki, da ki tsaya min da kafafunki ganin maganar da aka fara ta yau ba ta lalace ba.”

“Me ya sa kike tunanin za ta lalace?”

Cewar Fatima bayan ta kafe ta da ido.

“Alamun hakan nake gani, Jamil ne namiji na farko da ya san gidanmu, kuma ya tura a tambaya mishi aure na. Amma da yawan wadanda suke sona, da sun zo gidanmu magana take lalacewa.”

“Me ya sa?” cikin sauri Fatima ta tambaya.

“Cewa suke wai na fi karfinsu. Ban taba ganin inda yawan kudi suke zama kalubale a aure ba sai a kaina. Ba fa ni ce mai kudin ba, Babana ne da Mamata, amma duk wanda ya ga gidanmu wai sai ya ce na fi karfinsa, saboda idan ya aure ni bai san me zai ba ni ba, kuma wai zan, iya raina shi ko in raina ƴan’uwanshi.”

Ta dan tsahirta, kafin ta dora”Ina son in yi aure Fatima, ko don hutawa da gorin na ki aure, kin ga ko taron dangi ban zuwa, Ammy ma ba ta son in je, saboda sai ranta ya baci a kan maganar aurena, kin san dai halin mutanenmu idan mace ta isa aure, kuma ba ta yi ba. 

Lokacin Dadyna yana ambassador a Kasar Saudiyya, haka suka matsa muka baro Kasar ina tsakiyar karatu, wai a Saudiyya ina zan samu miji, ya fi in dawo gida. Ni da Ammy mu ka dawo ta shiga kasuwancinta, yayin Dadyna ta kan kawo mana ziyara muma kuma haka. 

Makaranta aka nema min mai kyau a Abuja, na fara jin dadin karatun nan ma yayan Dadyna ya ce wai a waccan makarantar ta ƴan karya ina zan samu miji, Abuja rayuwar karya ta fi yawa in dawo Katsina gidan Goggota. Haka aka kuma yanke min karatu na dawo nan, lokacin da na fara karatu a nan kowa ma haushin sa nake ji, karatun ma a rai bace nake yin sa, ba na ma jin dadinsa. Ammy ke karfafa min gwiwa ta ce in yi hak’uri, komai zai wuce, wani lokaci kuma ta kan tsokane ni ta ce kila mijin nawa a nan yake.

Lokacin da muka fara magana da ke ne na fara jin dadin karatun, ita kanta Ammy ta kan ce Umaima yanzu kam kin fara samun nutsuwa, wai jikina yana nuna hakan.

Lokacin da na kai ki gida rasuwa matar Jamil Familynku ya burge ni, nai ta jin ina ma gidanku ne gidanmu, da sha’awarku na taho a kirjina, kuma na sha ba Ammyna labarinku.”

Ta kuma tsahirtawa hade da kallon Fatima. Ganin hankalinta na a kan ta sai ta ci gaba.

“Lokacin da kika fara tsokanata da Jamil, sai na rika fatan hakan ya kasance, ba fa wai don ina son shi ba, kawai dai in yi auran, in kuma ganni kwance a tsakiyar gidanku, ni ma na zama daya daga cikinku.”

Sautin murmushin Fatima ya fita, ita ma Umaiman sai ta yi murmushin sannan ta ci gaba.

“Sai kuma Allah bai hada jinina da shi ba, kullum muna cikin sabani. Lokacin da na yi ciwo ne na samu kusanci da shi, saboda bayan tafiyarki, yana zuwa duba ni, sai ma ya karbi No ta ya rika kirana muna gaisawa hade da tambayar jikina. Ina jin a nan ne muka fara fahimtar halin juna, har ma ne nemi alfarmar idan zai je Sandamu zan bi shi saboda ina son yi miki ba za ta. Ya tambaye don ba za ta kawai. Na ce ina son garin ne. Ya kuma tambayata zan iya zama a can. Na ce mishi sosai ma. Ya ce min yana nufin da aure, na kuma tabbatar mishi. Sai ya ce to zai gwada ya gani. Zai turo wani ya aure ni, na ce mishi to. Rana ta farko da muka yi magana mai dan tsawo. Daga wannan matakin mu ka fara zuwa yanzu da muke magana.”

Ta ja numfashi a hankali, kafin ta ci gaba” Abin da na fahimta daga lokacin da magabata suka shiga maganarmu Jamil ya canja, kamar yana danasani. “

Fatima ta dan sosa kanta kadan kafin ta ce” Don Allah ki bar daga hankalinki, sha Allah komai ba zai faru ba sai alkairi, sannan komai da lokacinshi, sha Allah lokacin naki auran ya yi.

Kuma kar ki zargi mutane da abin da suke fada a kanki na kin fi karfinsu, mu kanmu mun fadi haka, kuma muna kan fada. Idan so samu ne mace ta yi aure inda ya fi gidansu ba wai koma bayan gidansu ba, idan tana sha shayi da bread da safe, to a gidan mijinta ta samu tea da har da karin kwai. Kin san shayi daban tea daban.” ta karasa maganar tata cikin dariya.

Ita ma Umaiman murmusawa ta yi, yayin da Fatima ta dora.

“So kin ga duk wanda ya zo neman auranki, ya kalli dukiyar da ke gidanku, jikinsa zai mutu, ya fara tunanin me zai ba ki, idan ya raba ki da gidanku. 

Saboda da yawan mata idan suka shiga gidan miji, suka ga abin da suke samu a gidan mijin bai kai na gidansu ba, za ki ga raini ya fara shiga tsakaninsu da mazajensu, sai rashin zaman lafiya ya kutso, ai ta tashin hankali kullum, daga karshe dai auran ya mutu. 

Wannan maza suke kallo a kanki su janye, kar su dakko ki, a zo abu ya ki dadi. Ko kuma su hare kansu wajen ganin sun yi miki abin da kike so. 

Mu ma kin gan mu nan to shahadar kuda mu ka yi, amma ke din ba sa ar auranmu ba ce. Kin san gidanmu, tuwo muke ci, da safe mu sha koko, don haka muna ba ki hakuri da abin da za ki taras idan Allah Ya kulla abun, ki yi hak’uri da abin da za ki gani. “

Shiru Umaima ta yi cikin nazarin kalaman Fatima, tabbas gaskiya ta fada, sai dai wannan tunanin na mutane zai shafi rayuwar wasu, da hukuntasu da laifin wasu.

“Sannan ina mai tabbatar miki Jamil mutumin kirki ne, ba wai don yana dan’uwana ba, in sha Allah idan ya kasance mijinki, to jinkirinki zai zama alkairi gare ki.” Fatima ta katse mata tunaninta.

“Allah Ya tabbatar mana da alkairi.” Cewar Umaima cikin mutuwar jiki.

“Amin.” Fatima ta amsa lokaci daya kuma tana kallon kiran Mustapha da ya shigo wayarta.

Shaida mata yake yi zai tafi dasu Hana gobe saboda school. Allah Ya kiyaye hanya ta amsa mishi.

Ya dauka za ta hana, ko sai an kai ruwa rana, wannan yana daya daga cikin halayenta masu wuyar Fahimta, abin da ake tunani xa ta daga hankali sai dauke shi da sauki, wanda kuma ake ganin ƙarami ne, ita kuma ta girmar da shi.

Kan katifar ta karasa hade da zama, suka ci gaba da tattaunawa da Umaima.

Wannan semister har gudu sai da Fatima ta ga ta yi mata, ko don babu wani conjunction a kanta ne oho.

Lokacin da time table ta fita, tattare hankalinta ta yi sosai wajen karatu, yadda ta fara successfully so take ta kare successfully, don yanzu babu wani bashin c/o da makarantar ke bin ta, c/o da take dasu ta gyara, shi ya yanzu ba ta fatan ta samu wata.

Dama Umaima karatu a wajenta ba sai exam ba, kullum cikin bincike take fiye da Fatima. Ta kan ce aikina yana bukatar bincike Momyn Ziyad, mutane zan rika dubawa, kar in je in kashe wasu.

Sucessfully suka fara jarabawa, wannan karon Umaima za ta riga Fatima gamawa, amma ta ce za ta jira ta. Hakan sai ya yi wa Fatima dadi.

Yau exam din karfe takwas na safe gare ta, shi ya sa tun 7:30am ta bar gida cikin motar Umaima, saboda Umaima yau ita hutu take yi, Fatima kuwa za ta shiga 8am, ta koma wata karfe daya.

Shi ya sa sai karfe hudu na yamma ta danna horn a kofar gate.

Maigadi ya bude mata, suka gaisa sannan ta silala cikin gidan a hankali.

Mustapha da ke jikin mota tsaye tare da Umaima ya bi motar da kallo, har zuwa lokacin da Fatima ta bude ta fito.

Kasa-kasa Umaima ke dariya tana kallon Mustapha.

Cikin siririyar dariya Fatima ta ce “Kallon ya isa haka mana, kar kasa in fadi.”

“Fatima! Driving, kuma da kanki. Mafarki nake yi ko a farke.”

Sai da ta juya ido kafin ta ce “Ba kama ko?”

Ya juya kan Umaima tare da fadin “How! Even in my dreams.”

Cikin dariya Umaima ta ce “Kawai tukuici za ka miko. Ba a mafarki ba, a zahiri Fatima Musa Sandamu na murza sitiyari.”

Ya girgiza kai cike da shauki ya ce, “Juya bayanki Aunty Umaima ina jin kunyarki”

Cikin dariya Umaima ta riga a guje tare da fadin “ni na ma baku wuri ma”

Cikin farin ciki ya janyo ta jikinsa ya rungume, ta shiga kokarin kwacewa hade da fadin “Akwai Maigadi fa, ko ka manta.”

Ya dan janye ta jikinsa tare da kissing dinta “kin yi min ba za ta, ba za tar abin da na jima ina fata, kullum na ga mace a mota na kan ji ina ma ace ke ce, yau sai ga idona ya yi kacibus da abin da nake fata, ban da abubuwa sun yi min yawa, da murnar gama makarantarki zai zo daidai da mallakar sabuwar motarki, amma sha Allah I will do that soon. “

Cikin dabara ta karasa janye jikinta daga gare shi ta ce” Na yi mamakin ganin ka”

“Kawai na yi kewa, kin san kwanakinmu a hotel din can sun ki bace min, zuwa na yi ki yi min kwana daya kacal, da safe zan sallame ki, Sandamu zan wuce”

Ta dan bata fuska “Ka san fa jarabawa nake yi”

“Sorry, just kwana daya fa.”

Ya yi maganar a marairaice.

Ita ma kyabe fuska ta yi, kamar za ta yi kuka, kafin ta ce “Gobe ma fa ina da exam din karfe goma”

Langabe kai ya yi tare da fadin “ba zan bata miki lokaci ba, ni ma da sassafe zan tafi.”

Ta juya zuwa hanyar daki ba tare da ta yi magana ba.

Yadda ta shiga dakin fuska cunkus ne ya sanya Umaima yanke wayar da take yi, tare da tambayar “Lafiya?”

Kamar kamar yarinya ta shiga bubbuga kafa a tsakiyar dakin, kamar za ta yi kuka take fadin “Ya Mustapha ne, yanzu ya tsiro da wani sabon abu, yay ta zuwa yana Jana hotel, fisabilillahi akwai mutumci a ciki.”

“To ba mijinki ba ne?” cewar Umaima tana kallon ta.

“Don mijina ne fa, kowa ne ya san mijina ne? Na rantse da Allah daga yau ni ba zan kara zuwa wani hotel ba kamar yar iska, idan kuma ya matsa min Mama zan fadamawa.”

Umaima da ta saki baki tana kallon ta, kan katifar ta fada hade yar karamar shewa tana fadin” Allah ya kawo rabon yan biyu. “

Cikin sauri Fatima ta ce” Ba amin ba. Ke yaran wannan zamanin, wanda aka yi cikinsu ba a daki bisa gadon sunnah ya aka gama dasu bare wanda aka samo a yawon bin hotel, don Allah rufa min asiri”

“Duk fa daya, saboda duk da aure aka same su.”

Jin horn din Mustaphan ne ya sanya Fatima nufar kofar rike da yar jakar da ta shirya kayanta.

Cikin tsokana Umaima ta ce “Don Allah Momyn Ziyad kada ki yi mishi rowa, ki ba shi dama ya mori kudin dakin da ya biya.”

Dawowa Fatima ta yi da sauri cikin dakin, hakan ya sa Umaima mikewa tsaye, suka shiga zagaye dakin a guje, Fatima na kai mata bugu suna dariya.

Horn din da ya kara ne, ya sanya Fatiman ficewa cikin dariya.

Key din motar ya mika mata tare da fadin” Ja ni in ji tukin naki ko da dadi. “

Duk da ba ta taba jan ko wace mota ba, sai ta Umaima karbar key din ta yi, da kwarin gwiwarta, yayin da ya bude front seat na kusa da ita ya zauna.

Daidaita nutsuwarta ta yi hade da murza key din, kamar dama can ta saba da tuka motar tashi haka ta fice daga gate din, tun yana dari-dari da tukin nata har saki jiki.

Ita ma tun tana jin tsoro har ta daina.

Lafiya suka shiga harabar hotel din, ta zare key din motar hade da mika mishi. Ya hada key din da hannunta ya matse yayin da ya zuba mata matsaikaitan idanunsa, cikin mutuwar jiki ta janye nata, dalilin da ya sanya shi janyo ta sosai zuwa jikinsa.

“A kwanakin wani sabon shauki na sonki ne yake damuna. Na kasa jurewa.”

Ba ta ce komai ba, illa jin yadda yake yamutsata kamar ba daki zasu shiga ba, da kyar ta samu suka shiga daki, a dakin ma duk yadda ta so ya bar ta, ta yi wanka kiyawa ya yi, dole ta kyale sa ya sauke abin da ke damunsa, kafin ta, samu ta yi wanka hade da cin abinci.

Wanshekare a school ya sauke ta sannan ya wuce Sandamu. 

Lokacin da ta dawo, haka Umaima tai ta, tsokanarta, wani ta rama wani kuma ta yi shiru. 

Ranar Laraba, rana ce mai dimbin tarihi a wajen su Fatima, rana ce kuma ta farin ciki da ba zasu manta da ita ba. 

A ranar suka kammala jarabawa kammala makaranta a matakin degree. 

Bayan kalubale da yawa, da tudu da gangare hawa da sauka. DAGA KARSHE dai an kai inda ake son zuwa. 

Rabuwa da Umaima na daya daga cikin abin da dama kullum Fatima ke juya, akwai shakuwa sosai a tsakaninsu, rabuwa da wanda ka shaku da shi kuwa akwai wahala. 

Daga ita har Umaiman dannewa suke yi suna nuna ba komai. DAGA KARSHE dai sai da zuciyarsu ta karyata su, lokacin da Jamil da kuma Mustapha suka bayyana a harabar gidan da zummar rabasu ta hanyar kai Umaima Kaduna Fatima kuma Sandamu. Rungume juna suka yi, hade da fashewa da kuka, kuka sosai suke yi. Mustapha ne kawai ke aikin lallashi hade da rabasu daga yadda suka rungume juna. Don shi Jamil tsaye kawai ya yi rungume da hannayensa yana kallonsu. 

Dakyar Mustapha ya yi nasarar sanya Fatima cikin mota, kuma bai bata lokaci ba ya fice daga gidan, don shi ma zuciyarsa tuni ta karye, idan zai jima, a, wajen zai iya yin kukan shi ma. 

Lokacin da ya daidaita a hanya ne ya ce “Kin bi kin hade fuska, ranar da ya kamata ace kina farin ciki fiye da ko wane lokaci, Umaiman nan fa ba kun rabu kenan ba, musamman da aure zai kawo ta gidanku, bayan wannan ma ke da ita makota ne idan kika tare a Katsina.” 

Ta share sabbin hawayen da suka gangaro mata a hankali tare da fadin” Ya Mustapha ka zauna da mutum tsawon lokaci, sannan ace an rabu akwai taba zuciya. Umaima ita ce kawata ta farko, wacce babu wata alaka ta ƴan’uwantaka a tsakaninmu. Ta yi min abin da ba zan iya biyanta ba, sunan kawai na haifi Beauty ne, amma rainonta daga haihuwa zuwa yaye Umaima ce ta yi kaso tamanin cikin dari. Kudin da ta kashe mata ni ban kashe mata ba. Mun sabu sosai, idan ba ta gidan sai in ji kamar ba kowa, a school ma muna jone, lokuta da yawa ta sha raka ni lecture, har yan department dinmu sun santa. Yanzu kam sai nake ji na kamar dai na rasa wani bangare ma fi muhimmanci a jikina. “

“To ni din fa? “

Da jikakkun idanunta ta aika mishi da harara, ba tare da ta ce komai ba. 

Ya dan yi dariya” Yanzu idan aka ce an kara maku shekara daya za ki so”

“Sosai ma.” 

Ya dan murmusa kadan tare da fadin “Ita makaranta dama haka take, lokacin da kake yi ka ji ka kosa ka gama, idan kuma ka gama ka ji ina ma a koma baya.” 

“Lokacin da na gama secondary ban damu sosai ba, kila ko don wacce na fi shakuwa da ita tana tare da ni oho?”

Ya amsa mata “Da haka ne ma, kuma kin ga ikon duk zaku sake haduwa waje daya, tun da ita ma Zainab din tana Katsinar.” 

Haka suka ci gaba da hira, har ta dan fara warwarewa, ba sai ya tambaye ta ba, ya san za ta ce gidan Mama zai dire ta, shi ya sa kai tsaye kofar gidan ya tsaya. 

Sai kuma wani sabon farin ciki ya lulllubeta, yau dai ga shi ta dawo gida ba da sunan hutu ba, da gama karatun degree gabadaya, ina ma ace Alhaji na da rai lallai yau da ya yi farin ciki da murna mai yawa. Lokuta da yawa yana fadin “Tausayinki nake ji Fatima, duk cikin ƴan’uwanki ke ce ba ki yi karatu mai zurfi ba, ga shi ba ki iya sana’a ba. Na so ace kin yi karatu kuma kina da aiki mai kyau. Yau dai ta samu daya daga cikin biyun da Alhaji ke burin ya ga ta samu. 

Ta fuskanci kalubale, mutanen da basu goyawa karatunta baya su suka fi yawa, kowa gani yake tun da ta yi aure kuma ga yara ba za ta iya ba. 

Daga karshe dai ta kore wannan tunanin na mutane, duk da ta san ta sha wahala karatu da aure kuma da raino ko ciki akwai kalubale, amma da zarar ka sanya a zuciyarka za ka iya, to za ka iya din. 

Ledar tsarabar da ta yi wa yara kawai ta dauka, sauran kayan kuma Mustapha ta wuce dasu gida. 

Kai tsaye dakin ta dosa inda Mama ke amsa mata sallama tana fadin “Barka! Barka Fatima, na taya ki farin ciki, Allah Ya albarkaci abin da kika karanta, Ya sa ki amfani al’uma da shi. Na ji dadi, na yi farin ciki.” 

Bakin Fatima ya ki rufuwa, ga wasu guntayen hawaye da tana gogewa take amsawa Mama da amin-amin. 

Daya daga cikin kujerun dakin falon ta zauna, suka gaisa daya bayan daya, suka kara yi mata murna, sannan ta mikawa Mama ledar tana fadin” a rabawa yara.”

“Suna islamiya, sai idan sun dawo” Mama ta amsa tana kallon agogo da ya nuna karfe biyar saura na yamma. 

“Ina Mustaphan?” Mama ta tambaya

“Ya wuce gida.” 

“Ai tun shekaranjiya Ummi ke gyara miki gidan.” 

“Eh dama haka ta ce.” 

Aunty Bilki ta tsoma baki da fadin “Sai ki zo ki tattare yaranki zuwa wajenki, ki ji abun da ko wace uwa take ji. Saboda wadannan yaran ko tsine musu kika yi ba kama su za ta yi ba. Tun da ba wahalarsu kika sani ba”. 

Dariya Mama take yi sosai saboda ta san ina maganar Aunty Bilki ta dosa. 

“Ai dai uwata ce ta rainanmu ba wani ba” Fatima ta ba ta amsa cikin harara. 

Haka su kai ta kafsawa har yaran suka taso makaranta, amma babu wanda ya leko gidan Mama duk gidan Aunty Hauwa suka wuce, wai sun tafi islamiyar ne sun bar Zainab za ta yi wainar fulawa, shi ya sa suna dawowa suka zame can. 

Fatima da Aunty Bilki ma sai suka nufi gidan, gidan kuwa cike da yara, har da nasu Aunty Ayyo wai sun zo cin wainar fulawa. 

Fatima ta ce “Ai tsiyar yawa kenan, mutum bai isa ya ci dadi ba, ko ya kirkiri abun kwadayi. Wlh ta fi miki ki zo ki koma gidan mijinki. Wannan irin gayya, sai ka ce kin soya ta rabin buhu.” 

Cikin dariya Zainab ta ce “Wlh kuwa, ba damar ki yi dan abun kwadai, sai a lullubeki kamar wata uwar zuma. Kin ga mai dan banzan surutun da ta fada musu nan” , ta yi maganar hade da nuna Nusaibar Aunty Sadiya. 

“a sirrin ce muka yi magana da yarinyar nan, amma duk wanda ta hadu da shi sai ta fada mishi zan yi wainar fulawa.” 

Aunty Bilki ta yi dariya hade da fadin “To muma ba ga shi rabo ya rantse ba.” 

“Goggo Fati Congratulations, na taya ki murna Allah Ya sa alkairi.” 

Cewar Zainab 

“Amin.” amma na fada miki ban son Goggon nan fa. 

Duk suka yi dariya inda Fatima ta juya kan Aunty Hauwa tana fadin “Mamanmu ke ba ki taya ni murnar” 

“Yi ai ni za a taya murna, kin gama makaranta zan huta ta hayaniya, ko ba komai za ki kwashe yaranki ni ma in rika yin baccin rana, na gama haihuwa amma kamar ban gama ba.” 

Dariya Fatima ta yi tare da fadin “Ai Aunty Hauwa sai dai ki yi fatan cikawa da imani, amma hidima da yara ai yanzu kika fara.” 

A nan ta yi sallahr isha’i kuma ta ci abinci, Mustapha kam gidan Mama ya ci abincin dare suka sha hirarsu sosai, sannan ya taho gida, don Fatima ta tura mishi sako ta wuce gida. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 61Daga Karshe 63 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×