Skip to content
Part 65 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Ranar Juma’a da misalin karfe 11am Blessing ta iso Katsina da tawagarta, da yake ba Mustapha ne ya kawo su ba, a tasha Fatima ta ce ta jira.

Ga mamakin Blessing din sai ga Fatima a mota da kanta tana driving.

Daga lokacin mode dinta ya canja, kishi ya motsa, inda ta tara tambayoyi da yawa a zuciyarta, waye ya siyawa Fatima mota? Me ya sa Mustapha bai taba yi mata hirar Fatima na da mota ba? Da fara aikinta dai ba ta isa siyan wannan motar ba.

Hankalinta ya dan kwanta ne lokacin da suka isa gidan Fatima kuma ba ta ga wani abun a zo a gani ba sai a kitchen din ta, suma kayan kitchen din duk nata ne da.

Tarbar da ta samu a wurin Fatima za ta iya cewa ita ce tarba ta farko da ta taba kuma ta ji dadinta.

Bangaren Fatiman ma wannan ne zuwa Blessing na farko da ta ji babu irin zafin da take ji a zuciyarta, kila baya rasa nasaba da nan din gidanta ne, kuma babu Mustapha a tare dasu.

Sun ci sun sha, sun kuma yi hira cikin girmama juna, da yamma ne Blessing ke shaidawa Fatima gobe Sandamu za ta wuce.

Abun ya zo mata da mamaki kasancewar ba ta ji Mustapha ya ambaci Sandamu a zuwan Blessing din ba, amma sai ta share, saboda ita ma tana son zuwa Sandamu din.

Shi ya sa ta shaidawa Blessing din zasu tafi tare dama Jamil yana can sai ya dawo dasu.

Abin da bai yi wa Blessing dadi ba, so ta yi ta tafi ita kadai yadda za ta samu damar bugun ruwan cikin mutane da yawa ta ji ta inda motar Fatima ta fito.

Kamar yadda Fatima ba ta nuna mamakin jin tafiyarta Sandamu ba, haka ita ma ba ta nuna rashin jin dadinta na yadda Fatima ta ce su tafi tare ba.

Misalin Karfe takwas na safe suka dauki drop din mota har Sandamu kasancewar su da yara ne.

Farin ciki sosai Fatima take ji na ganin yaranta biyar cas a tare da ita cikin koshin lafiya kamar ba nata.

Tun ba Hana ba, wacce ke ta tsawo kullum kamar ba har shekara takwas zuwa tara ba.
To abu ne ya saka tsakiya, uwa tsawo uba ma tsawo.

Lokacin da suka isa Sandamu ana kiran sallahr karfe daya.

Don lokacin da suka shiga gidan Mama alwala take yi.

Cike da farin ciki take fadin “Oyoyo!”

Su Hassan da suka fi sabawa da ita suka yi kanta aguje, ta ko rungumesu cike da kauna.

Daidai lokacin Jamil ya fito daga sashenshi da alama masallaci za shi, cike da mamaki yake kallonsu amma bai tanka ba.

Kai tsaye Fatima bangaren Umaima ta wuce, yayin da su Blessing suka bi bayan Mama.

Lokacin Umaiman zaune take a gefen gado tana warware hijabin da za ta yi sallah.

Baki bude ta ce “Yaushe kika zo?”

Cikin dariya Fatima ta fada kan gadon tana fadin “Kai ina son gado in ji Aunty Hauwa.”

Suka yi dariya a tare kafin Umaiman ta ce “Mayyar Sandamu, ai wlh na san ba za ki iya hakura ba ki zo ba.”

“Ni da ke waye mayen Sandamun, ke fa kawai kin auri Ya Jamil ne don ki rika zuwa Sandamu kina kwanciya a tsakar gida.”

Suka kuma tuntsirewa da dariya a tare, hade da tafawa, daidai lokacin da Fatiman ta mike zaune hade da karewa dakin kallo.

Cikin tsokana ta ce” A nan ake kashe arna dubu idan dare ya yi ko? Ahhh filin yaki ya yi kyau, fatanmu dai ganima ta iso bada jimawa ba. “

Duka Umaima ta kai mata, ta yi saurin ja da baya, ganin ta kasa samunta ne ta ce” Allah Ya shiryeki wlh. “

“Amin. Tare da ke” Fatima ta amsa hade da sakkowa daga bisa gadon, ganin Umaima ta kabbara sallah.

Lokacin da ta isa dakin Mama Blessing ba ta nan, wai ta tafi gidan Aunty Hauwa.

“Eh kam. Ai da gaskiyarta, yadda na taho gidan tawa uwar, gara ita ma ta tafi gidan tata uwar.”

Mama da ke zubawa yara abinci ta ce “Yaushe suka zo ne?”

“Jiya.” Fatima ta amsa mata daidai tana zama kusa da plate din Ihsan da Beauty, idan har ta bar su, su kadai fada zasu yi.

Sabuwar gaisuwa suka sake yi da Mama, hade da tambayarta yanayin aiki, Fatima ta amsa da komai na tafiya lafiya.

“Yaran sun fara zuwa makarantar ne?”

“Sai dai 2nd term, Saura sati biyu a fara jarabawa, shi ya sa kawai mu ka bar su zuwa next term din Idan Allah Ya kai mu.”

“To Allah Ya kai mu. Fatima ki tsaya a kan tarbiyar yaranki, tarbiya akwai wahala sosai a wannan zamanin. Sannan ki tsare mutumcinki don Allah.”

“In sha Allah Mama, ina kokarin yi hakan.”

Shigowar Umaima ce ta sanya su dakatawa, da gudu Beauty ta makalkale ta, ita ma cike da kauna ta daga Beauty tana fadin “Oyoyo my lovely Dota I missed you.”

Beauty dai sai dariya kawai, bayan ta ajiye ta ne, ita ma ta saka hannu a cikin plate din suka ci gaba da cin abincin tare, bayan sun gama yaran duk suka fice idan ka dauke Ihsan da ta ki bin su, tana manne da Fatima.

Hira suke yi sosai har zuwa lokacin da Jamil ya shigo, bayan ya zauna ne Fatima ta gaishe shi, ya amsa hankalinsa a kan wayar da yake daddanawa.

Wurin ya dan yi shiru kafin Mama ta ce “Ya ci abinci ne?” ta yi tambayar ne lokacin da take kallon Umaima.

Girgiza kai Umaima ta yi ba tare da ta ce komai ba.

“To a zuba mishi, ko ba yanzu zai ci ba”

Umaima ta saci kallonsa kadan, idonsa a kan wayarsa kamar ba a kansa ake maganar ba.

Fatima da take ta raba idanu tsakanin su ukun ta ce “Ikon Allah! To su basu magana? Ke ce za ki rika yi wa shirunsu tafinta Mama?”

Harara Umaima ta aika mata, Jamil dai uffan bai ce ba, Mama ce ta ce “Ina na sani musu, zasu shekara a nan, to haka za mu yi ta zama shiru.”

Tabe baki Fatima ta yi kafin ta ce “Ban iya irin wannan zaman. Wlh ramewa zan yi.”

Karon farko da Jamil ya dago kai ya kalle ta, sai ta murguda baki a hankali hade da kawar da kai gefe.

Umaima kuma ta fice zuwa kitchen, ba jimawa ta dawo, daga kofa ta ce “Nan za a kawo abincin.”

Kafin Jamil din ya amsa Mama ta ce “A’ah! Kai mishi can sashenku.”

Bayan ta juya ne Maman ta mayar da hankalinta kan Jamil “Ka rika sakin fuska wa matarka, kullum ina fada ma wannan.”

Bai ce komai ba, ya mike zuwa waje.

Ba jimawa Umaima ta dawo dakin, tun kafin ta zauna Mama ta ce “Koma wurin mijinki, wai ban hana ki, idan yana gida ki rika zuwa nan kina zama ba.”

Narke fuska Umaima ta yi, kamar za ta yi kuka.

Mama ta kuma cewa” Wuce ki tafi. “

Fatima da ke zaune ta kwashe da dariya tana fadin” Kai gidanmu gidan shagali in ji Aunty Aisha. “

Bayan Jamil din ya fita ne ta kuma komawa sashen Umaima.

Lokacin kwance take kan kujera tana chat, a cinya Fatima ta daka mata duka, hakan ya sa ta yi hanzarin tashi hade da sosa wurin.

” Masoya kenan yan duniya. Kuna ta, wani shan kamshi wannan cikin na jikinki na uban waye?”

Murmushi Umaima ta yi kafin ta ce “Babu fa wani shan kamshi, shi haka yake, baya son magana.”

“To kenan haka za ku yi ta zama kamar wasu kurame. Ke kina jin dadin zaman?”

“Ba na wani ji, amma tun da haka yake ya zan yi.”

“Just change him, kawai ki canja shi zuwa yadda yake so.”

“Ta ya?” Umaima ta, tambaya.

“Ki zame mishi tamkar karamar yarinya, ta yadda no matter how wani abun Sai ya yi magana.”

Siririyar dariya ta yi kafin ta ce “Zan gwada. Yaushe za ku tafi?”

“Ku zamu bi?”

Cikin zaro ido ta ce “Lallai akwai cinkoso kenan.”

Hira suka ci gaba da yi su yi ta makaranta su yi ta gida, a nan ne Umaima ke fada mata wannan azumin mai zuwa zasu tafi Umra ita da Jamil, kiran sallah ce ta tayar da Umaima. Fatima kam dama ba yi take yi ba.

Sai da yamma ta shiga gari, ciki kuwa har da gidan Ummi, inda suka tattauna a kan tafiyarta registration Daura.

Daga can gidan Aunty Hauwa ta yada burki, sai dai ba ta samu Blessing ba, don ita ma ta shiga cikin garin wajensu Aunty Ayyo.

Duk yadda ta so jin waye ya siyawa Fatima mota ta kasa ji, saboda ba ta hausar da za ta bugi cikin, duk wanda ta so bugun ruwan cikin nasa ce mishi take “Maman Ziyad an yi mota?”

Sai su amsa mata ta da “Aikuwa.”

Ita kuma ta ce “Allah Ya sanya alkairi.”

Idan suka amsa da amin daga nan sai ta rasa me kuma za ta ce.

Safiyar Sunday suka dakko hanyar Katsina tare da yaran har da Maamah wacce rikonta ya dawo
hannun Umaim.

Ranar Monday da safe Blessing ta dauki hanyar Abuja. Amma ban da Ihsan don fir ta ki bin ta, Ziyad ma har da kukansa shi wurin Mamanshi zai zauna, da kyar suka yi mishi wayon idan sun yi exam za a maido shi Katsinan, kafin ya yarda.

Haka rayuwa ta ci gaba tafiya cikin nasara da kuma kalubale, nasarorin dai na daya daga cikin abin da Fatima take kirgawa, don a cikin shekara biyu ta samu ci gaba sosai a wurin aikinta, courses din da take yi wajen aikin jarida shi ke ba ta damar kara gogewa, yayin da gogewar ke ta daga ta zuwa matakai daban-daban, inda a yanzu take a matsayin shugabar shirye-shiryen gidan radio.

A cikin shekara biyun, babu abin da yake burgeta d sanyata farin ciki irin saukar alqur’ani da suka yi, ga kuma sauran litattafan addini, sai take jin ta a cike taf, saboda ko wane bangare aka taba ta, ba za aji ta shiru ba. Zuwa yanzu kam su juyo da maimaita saukar, inda za a yi bikin saukar bayan azumi.

Bangaren zama kuwa Ziyad da Ihsan suna wurinta, yayin da Hana ta zama yar Blessing, don ko hutu ba ta iya gamawa a wurin Fatima, to gara ma Hana tana dan zuwa, ita Ihsan ko zuwa hutun ma ba ta yi, sai dai weekend shi ma a daddafe.

A cikin shekarar ne kuma hukumar gidan radion ta biya mata aikin Hajji, domin dakko rahotanni a kan aikin Hajji da za a yi a shekarar.

Wannan ne ya ba ta damar tafiya dasu Aunty Lami, Aunty Hauwa da kuma Mama wacce Allah bai daga ta ba sai a shekarar, saboda yanayin hidimomi na rayuwa.

Rayuwar tafiya take cikin dadi, musamman yanzu take aiki, da ace za ta iya daga murya ko ina aji ta, to da za ta ce a ba ko wace mace damar yin karatu mai zurfi, don ta samu abun dogoro da kai, ko kuma dai a koya mata sana’o’i na hannu, babu abu ma fi dadi irin ace mace na da abun hannunta.

Kamar ita yanzu ta kan yi komai ne ba tare da ta jira Mustapha ba, tun daga hidimar cikin gida har zuwa ta waje, ko kudin makaranta ba ta jiransa, idan an koma school tana da kudi kawai za ta biya. Abin da ta sani shi ne duka yaran nata ne, kuma za ta fi kowa farin ciki idan rayuwarsu ta inganta.

Hakan kuma ba karamin kara mata kima a idonsa ta yi ba. Duk da Blessing ma tana yi amma ita a kanta ne da kuma danginta, amma duk abin da ya shafi yara idan ta kashe sai ta lissafa mishi ya biya. Ita kuma Fatima kanta din ne ba ta faye yi ma wa ba, tana son abu za ta dakko ta ce ya siya mata, ita kam komanta shi ke yi.

Wannan yana daya daga cikin abin da ya fahimta daga bambancin mata biyu, wani lokaci shi kadai yake dariyar salon kishinsu, Blessing abu kadan yake taba ta, kuma ba ta iya shiru, ita kuma Fatima ba ta magana sharewa take yi, ta nuna kamar ba ta damu ba, wannan yake nuna mishi ta damun.

Zamansu daga nesa da junan ya fi dadi, musamman Fatima ya fahimci ta tsani ya kwana dakin Blessing ya kuma dawo dakinta ya kwana, shi ya sa ko hidima ake yi a Sandamu idan dukkansu suka zo, to Fatima ba ta kwana a can gidansu sai a gidan Mama, tun yana fushi har ya hakura ya kyale ta.

Blessing tana da dabi’ar ba ta yarda a fita ko a bar ta a baya ba, yayin da Fatima take i don’t care, idan ta samu daidai, idan kuma ba ta samu ba, ba ka taba gane yanayinta, ta ji haushi ko ba ta ji ba.

Lokacin da tafiya Saudiyyarsu ta gabato dole ta dauki hutu, saboda shirye-shiryen akwai yawa, ga na komawa sabon gidanta ga kuma na tafiyar, yawon sallama da take da ƴan’uwa ma kawai ya ishe ta.

Ranar da za ta daga zuwa Saudiyya har da kukanta, kukan da ta rasa na farin ciki ne ko kuwa dai na kewa ne? Don ma zasu hadu dasu Mama duk da ta riga su tafiya.

Shirye-shiryen komawarta sabon gidan a hannu Umaima ta bar shi da kuma Zainab.

Umaima kam a lokacin ta haifi Muhammad, wanda ake kira da Jawad, saboda sunan mahaifin Jamil ya ci, yanzu kuma tana laulayin ciki na biyu, duk da hidimomin da ke gabanta, kasancewar ita ta koma karatu, hakan bai hana ta dagewa wajen ganin komai ya tafi daidai ba.

Lokacin da jirgin su ya daidaita a sararin samaniya, take tsoron Allah ya cika mata zuciya, ta shiga tunano baya da yadda rayuwar ke tafiya yanzu, a duk abubuwan da ta lissafa a can baya tana son ta zama ko ta yi, babu daya da ya faru, kuma ga shi tana jin dadin rayuwar, komai yana tafiyar mata daidai.

Rayuwar bawa a tsare take bi kawai yake yi, tabbas akwai bukatar mutum ya yi planing, amma zabi mafi alkairi a wurin Allah shi ne ya fi.

Ya isa misali a kan ta, da yawan abin da babu su a jadawalin tsare-tsarenta sune suke faruwa da ita a yanzu.

Na farko dai ba ta kawo tsaure a jadawalinta ba bayan kare karatun secondary, amma sai auran ya fado bagatatan.

Abu ma fi ban mamaki a auran shi ne yadda ta auri Mustapha, wanda babu ko digon son shi a zuciyarta. Burinta zama nurse ne ko malamar makaranta, sai ga shi ta zama ma’aikaciyar gidan radio. Ashe a ta sanadiyyar aikin ne za ta samu damar cika daya daga cikin shika-shikan musulunci.

Burinta ta rayu a garinta, rayuwar wani gari daban ba ta burge ta, sai ga shi ta bar Sandamu zuwa Katsina. Ashe a nan ne za ta samu damar sauke alqur’ani mai girma.

Haka abubuwa ke ta zuwar mata sabanin yadda ta tsara su.

Bayan sallah da sati biyu suka baro Kasar Saudiyya zuwa gida. Misalin karfe biyu na rana suka sauka, inda Mustapha ya je dauko ta.

A sabon gidanta ta sauka, gidan cike yake da yan tarbata, sai ta ji a duniya kamar ranar ne ta fara sanin wani abu na farin ciki, Blessing, Hana ga Abdallah

Bangare daya ga Umaima da Jawad da Maamah.
Ummi da nata zuriyar guda biyu, ga Zainab ma da na ta. Sannan ga su Ziyad. Sai Mustapha da ya zama shugaban gida.

Gidan bai tsagaita da jama’a masu shigowa yi mata sannu da zuwa ba sai magariba, Zainab ma a lokacin ta tafi gida.

Sai da safe ne ta samu damar zagaye gidan, ya yi mata
kyau sosai tun daga ginin har kayan da aka sanya ciki.

Dawowarta da kwana biyu jirginsu Mama ya sauka, kai tsaye gidan Jamil aka yi da ita, wai sai ta huta an kuma yi walimar saukar su Fatima za ta wuce Sandamu, hakan ba karamin dadi ya yi wa Fatima ba, ita da ko wane lokaci take kaunar ta gan ta a tsakiyar ƴan’uwa.

Yau kam ta samu ta kasance da Mustapha, saboda Blessing ta bi Aunty Hauwa zuwa sandamu sai lokacin walima za ta dawo. Amma a kwana biyun ba ta iya kebewa da shi, wani irin nauyin Blessing din take ji, duk da yana da dakinsa a gidan, wani iri take ji ta tsallake ta ta je wurinsa.

Da misalin karfe goma na safe ta samu da kyar ta kwace kanta daga gare shi, sannan ta fito zuwa babban falon.
Dama ta san Hana ba za ta bar yaran har zuwa lokacin basu karya ba.

Da alama tun a can Blessing ta saba mata, idan ba ta fito ba, to ta nemar musu abinci, abu ma fi burgewa shi ne a kananan shekarunta ta iya da yawan ayyukan gida, tsabta kalkale har na bala’i, halin Blessing dai kaf ta kwashe, har da ba ta son ta ga wani ya fi ta wani abu, ta fi son su zo daidai ko ita ta fi.

Lokacin Ihsan ce yar rigima kawai ba ta karya ba, Ihsan akwai rigima da rikici ita a komai sai an lallabata, shi ya sa take shan jibga tun ba a wurin Ziyad mai zuciya a kusa ba. Basu shan inuwa daya yanzu ka ji tim-tim. Hatta uwarta ma jibgarta take yi, shi ya sa ba ta son zuwa wurinta daga Fatima sai Hussaini shi ma yana biyewa shagwabarta. Kuma babu wani batun sangarta ita kawai haka take rigimammace.

Dukkansu kallo suke yi, sai ita ce kawai da kayan break din ta a gabanta tana kananan kuka.

Ku san a tare suka hada baki wajen fadin “Momy ina kwana?”

Ta amsa cike da kulawa tana kallon Hana da ta hakimce hade da fuska ita a dole babbar yaya.

“An kaiwa Mama abun kari ne?” ta yi tambayar hade da kallon Hanan.

“An kai mata bread da kwai.”

“Ba ki iya soya dankalin ba ne?” ta kuma tambayarta.

“Na iya. Ferewar ne akwai wahala kuma na ce Ziyad ya ta ya ni ya ki.”

A lokacin ne ta kalli Ziyad wanda shi ma a lokacin su yake kallo.

Tun kafin ta yi magana a shagwabe ya ce “Momy ni ban iya ba, yankewa nake yi.”

Ba ta kuma cewa komai ba, ta juya kan Ihsan wacce dama idonta yana kan Fatiman, tun kafin ta ce komai Ihsan din ta mike zuwa inda take hade da fadawa jikinta.

Hakan ya sa hijabin dake jikinta zamewa.

Ta daga ta sosai zuwa jikinta kafin ta ce” Me aka yi mata. “

Da alama Hana a cike take, ita ce ta fara magana cike da bacin rai ta ce” Wlh ni wannan yarinyar duk ta ishe ni ma, na kosa ma mu tafi. “

“Me ta yi? “Fatima ta kuma tambaya.

“Wai tea ita ba madara take so, na yi mata hakan wai kuma ba a cup din ba sai a wani, ni kuma na kyale ta. “cikin zumbura baki ta karasa maganar.

“Ihsan! “Fatima ta kira sunanta.

Ba ta amsa ba, ta dai dago kanta tana kallon ta.

“Je kitchen ki dakko duk cup din da kike so, ki zo ki zabi abin da kike so a hada miki tea din da shi. “

Sai da ta kalli inda Hana take kwance, Hana kuwa ta aiko mata da harara, sai ta daga hannu daga inda take kamar za ta doke ta.

Fatima ta yi saurin cewa” Sauke hannun ita yayarki ce, kar ki kara cewa za ki dake ta. Wuce ki dakko cup din. “

Ba jimawa ta dawo dauke da Cup din, ganin katon cup din ne ya sanya duk yaran falon dariya har da Hana da take ta cin magani.

Fatima ta amshi katon cup din tana fadin” Mu je ki zabi abin da kike so a hada miki tea din da shi. “

Tana hada mata tea din ne Mustapha ya shigo falon sanye da jallabiya, bayan ya amsa gaisuwar yaran ne ya juya kan Ihsan yana fadin, “Kan mota sarkin rikici, garin ya waye ne, an dora daga inda aka tsaya.”

Duk suka yi dariya har da Fatima kafin ta ce “A duniya Ihsan akwai rigima. Za ta iya wuni tana yi, ba ta ko jin ta gaji.”

Ya yi dariya tare da fadin “Kin je kun gaisa da Mama ne?”

“Yanzu zan tafi dai.”

“Je ki shirya mu tafi.” ya yi maganar hade da dauke Beauty daga Saman kujera ya zauna, kafin ya dora ta a kan cinyarsa.

Ta fito sanye da doguwar rigar atamfa blue, dan madaidaicin gyale ta yi amfani da shi wajen lullube kanta, ya mike rike da Beauty a hannunsa, suka jera zuwa gidan Jamil.

A lokacin Mama rike da Maamah wacce Umaima ke ta fama da ita wajen sanya mata cannula a hannu.

Dalilin da ya sanya ansar Maamahn daga hannun Mama ta rike ta hade da fadin “Yar likitoci kullum ciwo.”

Cikin dariya Umaima ta ce “Wlh. Maamah na son ciwo”

Mama ta yi dariya tare da fadin “Au! Wai son ciwon ma take yi.”

“To ai ba ta yin sati lafiya ƙalau ita haka take” cewar Fatima lokacin da take lallashin Maamah bayan an sanya cannula.

Sai a lokacin suka gaisa da Maman.

“Umman Jawad za fa mu yi rashin mutunci a gidan nan, sai in kawo ma uwata abu ki hana ta ci, sai na ki” cewar Fatima tana kallon tiren da Hana ta kawo breakfast

“Amma sau nawa zan fada miki ki bar kawowa idan ba abun gargajiya kika yi ba” Cikin dariya Umaima ta yi maganar.

“to miko min abuna, dama bamu karya ba.” Fatima ta yi maganar hade da sauke Maamah daga jikinta.

Umaima ta janyo farantin tana fadin “Dama kyautar ba ta kai zuci ba.”

“Ba ta kai din ba” Fatima ta amsata lokacin da take yankar soyayyan kwan ta kai baki.

Umaima kuma kitchen ta nufa ta hadowa Mustapha breakfast.

Suna tsaka da ci ne Ihsan ta shigo gidan tana kuka. Mama ce ta fara cewa “To ga wannan a koken nan, gaskiya tun kafin ta iso ku tashi ku tafi na gode da gaisuwa. Ni ba za ta zo ta cika min kunne ba.”

Duk suka yi dariya hade da kallon kofar shigowa.

Kai tsaye wurin Fatima ta isa hade da fadawa kan jikinta, ta rungumeta tana tambayar” Me ya faru?”

“Me ko ya faru, yanzu haka barna ta yi, kin san kuma Hana ba ta da hakurin yaro. Kuma ta tsani ta gyara wuri a bata.”Umaima ta amsa Fatima

“Ai rabawa aka yi, Blessing ba ta haifi kanta ba, amma ga shi nan Fatima ta haifar mata, halin Maman Ihsan kaf Hana ta kwashe shi. Yayin da Ihsan ta dauke na Fatima har da rikicin. “

Cikin dariya Umaima ta ce” Wlh kuwa Mama gaskiyarki. “

Haka suka ci gaba da hira, har suka shiga tattauna yadda walimarsu Fatima za ta kasance, inda Mama ta ce ana gama walima gida za ta tafi, ba za ta iya zama a nan ba.

Ana gobe walima kuwa ƴan’uwan Fatima da na Mustapha suka cika gidan Aunty Lami, Zainab, gidan Fatima da kuma gidan Jamil.

Fatima dai cike take da farin ciki, ita ma ta sauke alqur’ani mai girma, lallai gemu baya hana ilmi.

Ranar Walima ankon omo blue din hijab suka yi dukkansu hade da nikab.

Filin taro kam ya cika tab da manyan mutane da mashahuran malamai. Misalin karfe goma aka fara walimar, inda aka saurari karatu daga dalibai masu sauka, daga bisani aka gabatar da kyaututtuka da kuma certificate.

Wajen karfe biyu aka tashi walimar, inda tawaga ta sauka a gidan Jamil, a nan ne kuma Jamil ya dankawa Fatima makullin sabuwar mota kirar camry irin ta Umaima.

Kyautar da ta faranta ran Fatima matukar farantawa, ko ba komai ya cika mata ragowar burinta.

Wanshekaren walima baki duk suka kama gabansu, ciki kuwa har da Mama. Blessing dasu Hana, Ummi da su Aunty Hauwa.

*****

Misalin karfe goma na safe Umaima ta shigo gidan, hannunta rike da dan karamin bowl yayin da take tura cikinta haihuwa yau ko gobe.

A lokacin Fatima zaune take cikin doguwar riga ash color wacce ta ci adon stone masu walkiya, kofin tea ne a hannunta tana kurba a hankali.

Cikin tsokana Umaima ta ce “Mai ciki!.”

Harara ta aika mata kafin ta ci gaba da sipping din tea din a hankali.

“Ga abun kwadayi na kawo miki. Na san dai kina so.” cewar Umaima lokacin da ta aje mata ƙaramin bowl din a gabanta.

Fatima ta bude bowl din ganin wainar fulawa sai ta dan fadada fara’arta, amma ba ta yi magana ba.

Cikin dariya Umaima ta ce “Wai ba yau za ki koma aikin ba ne mai ciki?”

Sai da ta harare ta sannan ta ce “sunan nan ya fita a bakinki.”

“Ai sunanki kenan. Sai kin haihu.”

Sai da ta dan ja tsoki kafin ta ce “Cikin nan ban so shi ba. Wlh kunya nake ji, wajen shekara bakwai rabonka da abu. Ranan Ziyad cewa ya yi Momy cikin ki ya yi kato kamar mai ciki. Wlh duk sai kunya ta kama ni.”

Dariya sosai Umaima ta yi, kafin ta yi magana ne wayar Fatima ta shiga kara. Ganin Mustapha ne sai ta daga tare da fadin” Gani nan tahowa.”

Cikin sauri ta aje wainar fulawar hade da daukar dankaramin milk color din baby hijab ta sanya. A kan stand ta dauki key din motar tare da fadin” Jirginsu Ya Mustapha ya sauka bari in dakko shi. “

Umaima ta bi bayanta da fadin” Ya zo ba shuka ruwa ne? “

Dariyar gefen baki Fatima ta yi tare da fadin” Wlh ke ma kin zawaye kafafunki. “

Umaima ta zaro wayarta lokacin da Fatima take sauka daga entrance din zuwa wajen motarta tana mata video.

Cikin mintuna kalilan ta gyara shi yadda zai yi kyau, sannan ta tura a WhatsApp din Mustapha, daga kasa ta ce ka nunawa Matarka wannan shi ne mafarkinta.

Lokacin da ya zauna a seat din kusa da Fatima ne wayarsa ta yi kara alamun sako ya shigo, dalilin da ya sanya shi saurin janyo ta daga aljihunsa. Ganin sunan Ummu Jawad sai ya bude, ya zubawa videon ido yana murmushi, kafin ya janyo Fatima jikinsa ya kanga mata wayar fuskarta, ta zubawa videon ido tana kallon wata kasaitacciyar mata ta fito daga dakinta zuwa farfajiyar gidanta mai matukar kyau, cikin salo mai ban sha’awa ta bude motarta ta shiga, sannan ta juya kan motar zuwa waje cike da kwarewa.

Bayan videon ya kare ya dago fuskarta suka hada ido kafin ya ce “Wannan shi ne mafarkinki wai in ji Umaima?”

Ta daga kai alamar eh.

Cikin murmushi ya ce “Mafarkinki ya zama gaskiya.”

Ita ma murmushi ta yi hade da kwantar da kanta a kirjinsa ta ce “Alhamdulillahi!.”

Karshe

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 64

2 thoughts on “Daga Karshe 65”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×