Ya zuba mata ido yana kallon fararen hokaranta da suke shirye a cikin bakinta, wanda bakin dasashi ya kara kawatasu.
Yau sosai ya ga fuskarta ta canja ya rasa dalili, tsawon minti biyu yana kallon ta a lokacin kuwa ta fara tsagaitawa da dariyar muguntar tata.
Ya dauki tsintsiyar ya nufi inda Mama take tsaye, gaishe ta ya yi kafin ya mayar da hankalinshi kan Fatima.
"Sau biyu kenan ake hukuntani da zunubinki, kar ki bari a kara na uku."
Hannu ta kai hade da rufe bakinta tana karamar dariya.
"Ai dama abun arziki bai gaji kare ba, ba yadda. . .
Hausa