Skip to content
Part 24 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Tun Fatima na boye ciki, har dai ya fito fili kowa ya gani, musamman a wannan karon da cikin ya yi girma sosai fiye da na Hana.

Ko fita can da nan ba ta son yi, saboda wadanda basu iya ganin dan karuwa a gado sai sun tambayi ina ubansa.

Yau ma da misalin karfe 11am zaune take a tsakiyar daki, Hana na kwance a tsakanin cinyoyinta, tana kama mata kanta da band.

Kamar daga sama ta tsinci muryar Aunty Hauwa na sallama, ba ta tashi ba, Kasancewar Hana na son yin bacci amma ta amsa sallamar sai ta tsinci kanta da jin faduwar gaba.

Ba jimawa kuma Aunty Hauwan ta shigo.

“Bismillahi” ta fada a daidai lokacin da take zama a kan kujerar cike da gajiya, idanuwanta a kan Hana.

“Kitso kuke yi?”

“Kamawa dai Aunty, wannan ai ba kitso ba ne” cewar Fatima lokaci daya kuma tana gaishe da Auntyn.

“Inna ba ta nan ne, na yi sallama amma shiru?”

“Tana nan, sai dai ko idan bacci ne ya dauke ta, don tun jiya take ce min ba ta jin dadin jikinta sosai.

“To Allah ya sawake.”

“Amin.”

Fatima ta amsa, lokaci daya kuma shiru ya ziyarci wurin kafin Aunty Hauwa ta katse shirun da fadin
“Ashe kin siyar da tunkiyarki, ga shi jiya ta haihu ‘ya’ ya biyu sambala-sambala duk maza, sai kin gansu.”

Wani abu mai kama da mulmulallan dutse ya daki zuciyar Fatima, ta kawar da shi da kyar, tana fadin “Ma Sha Allah, Allah ya rayasu.”

“Amin” Aunty Hauwa ta amsa.

“Fatima!” ta kira sunan ta, da muryar da ke nuna magana mai muhimmanci.

Ba ta amsa ba, sai dai ta daga kai tana kallon ta.

“Da gaske kin siyar da fridge da injinki?”

Sai da ta sauke ajiyar zuciya a hankali, sannan ta daga kai sama alamar eh.

“Amma me ya sa?”

“Haka nan.” ta amsa Aunty Hauwan a hankali.

“To ina kudin?” Aunty Hauwa ta Kuma tambaya bayan ta kafe ta da idanu.

Yatsanta daya ta tura cikin kunnenta tana sosawa kafin ta ce “Na yi amfani dasu.”

“Me kika saya?”

“Kayyah Aunty!”
Kamar za ta yi kuka ta yi maganar.

“Hmmm!” Aunty Hauwa ta ce kafin ta dora

“Wato ke yar dadi miji ko, kina tsince kayanki kina siyarwa Fatima kuna kashe kudin a banza. Shi yana karatu ke kina zaune, ke ce za ki rike mishi gidan hade da daukar nauyin karatun na shi?”

Kamar ba za ta cewa Auntyn komai ba, kuma sai ta ce “Aunty kudin aikin Hana ne fa aka biya, kuma ni Ya Mustapha bai sanya ni sanya ni sayar da komai nawa ba, hasalima sai bayan na siyar yake sani. Don Allah kar ku dauki alhakinsa.”

“To ke ce za ki biya kudin aikin?”

“To Aunty idan baya dasu, zan bar yarinyar nan ta mutu ne?”

“Ba za ki bar ta ta mutu ba, amma ki dawo hankalinki, kada ki kuskura in kara jin kin daga wani abu kin sayar, ba a sabawa namiji da irin wannan. Ki natsu ki dawo cikin hankalinki. Kuma kin ga daga wannan cikin, to ki yi planning, ki samu ki koma makaranta, tun da shi ma Mustaphan ai daga wannan semister ya gama ko, saura bautar kasa. “

Kai kawai Fatima ta daga alamar eh.

“Dama abin da ya kawo ni kenan, kuma muddin za ki cigaba da salwantar da kayanki, wlh zamu zare hannunmu a lamarinki, sai ki je can ki yi fama.”

Wannan karon ma ba ta ce komai ba, har zuwa lokacin da Aunty Hauwan ta mike tsaye, hade da bude posser ta kirgo kudi ta mika mata,” ga shi nan ko za ki siyawa Hana wani abun. “

“Mun gode.” ta karɓa da hannu biyu.

“Yauwa, kuma ya kamata ki fara shirin cire yarinyar nan a nono haka nan, kada ta sha cikin nan ya yi mata yawa.”

“Toh!” ta amsa a hankali.

A hankali ta zame kan Hana, ta bi bayan Aunty Hauwan, sai da suka kuma shiga bangaren Inna suka gaisa tare da taba yar hira sannan Aunty Hauwa ta tafi.

Tun da ta dawo bangarenta take tunanin maganar da suka yi da Aunty Hauwa, ta rasa ta yadda za ta iya kawar da kanta a matsalar Mustafa bayan tana da mafitarta.

Kenan sai ta zuba mishi ido yana cikin matsala ita ba za ta yi komai ba.

“Kai ina! Ba zan iya ba.” ta fada a zahiri.

Ranar haka ta wuni tattaunawa da zuciyarta a kan batun.

******

Yau Jumma’a tun misalin karfe 12:30pm Fatima suka kammala aikin gida, shi ya sa zuwa karfe biyu na rana ta gama shirin ta tsaf cikin doguwar rigar material mai kyau mara nauyi, wacce ba ta kama ta ba. Doguwar hijab ta sanya hade Plat shoe baki.

Ta yi kyau sosai, haka ma ta shirya Hana cikin doguwar riga yar kanti light purple mai kyau, a cikin rigunan da Zainab ke sawo mata ne, don ka’ida ne duk lokacin da za ta zo hutu akwai tsarabar Hana.

Kafafu da hannuwanta shar da kunshi, farin takalmin mai igiya sai ya kara haska kunshin nata, wanda Ummi ke daukar nauyin wannan bangaren, da wani ya fita take kuma yi mata wani. Ita Fatima nata kitso.

Ba ta dau komai ba, idan ka dauke hannun Hana da ta rike, don rabon da Baba ya zo ta kai mishi wani abu, kamar yadda sauran yan’uwanta suke yi har ta manta.

Haka take zuwa hannu na dukan cinya, to ita ma ta kanta take yi, wai an gayawa ma’auni biki. Sai da ta sallami Inna, sannan ta dauki hanyar gidan.

Kofar gidan nasu cike da mutane, wanda dama duk ranar Friday idan Alhaji Musa ya zo, hakan ne yake faruwa.

Ta gaishe da wasu, wasu kuma suka gaishe ta, a haka har ta isa tsakar gidan nasu, inda take dauke da yayyunta mata, da yaransu, don haka tsakar gidan a cike yake, Mama dai dama a irin wannan lokacin daki ne wurin zamanta, ko kuma kofar dakinta, sabanin su da suke masauki a kasan dalbejiyar gidan.

“Yo ina Hana din?” kusan tare suka hada baki wajen tambayarta, maimakon amsa sallamar da ta yi.

“Tana wajen Baba.” ta amsa su, lokaci daya kuma ta nufi daki inda Mama ke zaune cikin kwalliyar juma’a.

Sai da suka gaisa, sannan ta haye kan 3sitter ta kwanta ba tare da ta fita waje, wurin sauran yan’uwanta ba.

Haka kawai ba ta son zama cikinsu, gani take kamar suna yi mata wani irin kallo. Sannan ta san zuwa yanzu kowa ya san ta siyar da kayanta, ita kuma Sam ba ta son maganar, shi ya sa ta zabi da ta zauna a dakin.

“Lafiya kike?” Mama ta katse mata tunanin da take yi.

“Lafiya ƙalau.”

“To na ga kin kwanta, ga sauran yan’uwanki can a waje.”

Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba, dalilin da ya sanya Mama tabe baki, kafin ta ce “Mustaphan bai zo ba?”

“Eh. Zasu fara jarabawa ne ranar Litinin din nan mai zuwa.”

“Allah ya bada sa’a. Sai ki yi kokari yana kammala na shi, ke ma ki samu ko diploma ki yi, kin ga dai ga Zainab nan sauran mata shekara daya.”

“In Sha Allah!” cewar Fatima, Sam ba ta son maganar ta yi tsawo.

Aunty Sadiya ce ta shigo hade da kwantar da Affan da ya yi bacci, bayan ta kwantar da shi kuma sai ta samu wuri ta zauna hade da kallon Fatima

“Fatitti lafiya?”

“Ƙalau.” ta amsa a hankali

“Na ga kin kwanta, ko gaisuwa babu”

Shigowar Aunty Auyo ya hana Fatima amsawa.

“Fatima lafiya ko?”
Aunty Ayyo ma ta tambaya

“Lafiya ƙalau.” ta amsa hade da tashi zaune.

“Mustaphan bai zo ba?”

“Eh.” ta kuma amsawa Aunty Ayyo.

“Fatima!” Aunty Ayyo ta kira ta.

Ba ta amsa ba, amma ta dago kai tana kallon ta, yayin da gabanta ya fara faduwa, ba mamaki abin da ba ta so din ne za a yi magana.

“Me ya sa kika siyar da fridge dinki, fridge mai kyau da nagarta Fatima, me kika yi da kudin?”

“Amma dai ai na fadawa Aunty Hauwa ko.” cewar Fatima bayan ta hade fuska.

“Amma ai ba fridge din kawai kika siyar ba, hatta zannuwan da aka yi miki wurin haihuwar Hana an ce duk kin siyar.”Aunty Sadiya ta fada idanunta a kan Fatima.

Ba ta son bude baki ta yi magana, saboda maganar da ke cikin bakinta mai daci ce, shi ya sa ta yi shiru, har zuwa lokacin da Mama ta dora.

” Ita dai ta sani, mu dai namu ido, ban san ma me ya sa kuka damu ba, tun da ba ta saka daku ba ina ruwan ku?”

“Amma Mama ai dole ne mu yi magana, fisabilillahi ace duk wasu kaya nata sai tsincewa take tana siyarwa, kuma ni ban ga wani abu da ta siya da kudin ba. Ana yi wa namiji haka ne, idan ba ta da shi Allah ba zai waiwaye ta ba.” Aunty Sadiya ta kuma fada.

” To wai Aunty ya kuke son in yi ne, zan zauna ina kallon Ya Mustapha a cikin matsala ba zan taimaka masa ba? “

Aunty A’i ta ce” Hmmm! Ke yarinya ce, idan namiji yana son abu a wajenka dama kamar ya kwanta ma, ga dadin baki kamar talakan miji, da zarar ya samu ba yar iska irin ki. Mu gaskiya muke fada miki. “

” Ni fa Ya Mustapha bai taba neman na siyar da wani abu nawa ba, ni ce kawai nake siyarwa saboda hanyar ce kawai mafitarmu.”

“Koma dai menene kar ki sabawa miji da daukar kayanki kina siyarwa, saboda matsalar gidan shi.”

” To na gode ” Fatima ta fada cikin ko in kula.

“Don Allah ku kyale ta, idan ma kanta za ta siyar ta ba Mustapha ta siyar ta ba shi. Sai dai ta sani, wlh duk ranar da kwabarta ta yi ruwa kar ma ta nemi daya daga cikin mu.” cewar Mama a kufule.

“Ni dama ba zan nemi kowa ba” Cewar Fatima, don duk yadda ta so danne maganar ta kasa.

“Inyeee!” cewar Aunty Ayyo.

“To Aunty me kike so in yi? Zan kyale shi ya yi bara ko ya yi sata ne, yana yin iya bakin kokarinsa a kaina ni na sani…”

“Ke da Allah can!” Aunty Aisha ta katse Fatima cikin tsawa

“To don ubanki ba baki na yi miki ba, amma wlh sai kin yi kuka da idanunki a kan Mustapha.”

“In sha Allah ba zan yi ba. Aunty Aisha ku daina yi min mugun baki, to wlh ko na yi kukan bakinku ne ya ja min” Fatima ta fada cikin bacin rai, dalilin da ya sanya Mama kai mata duka a baki. Sai dai ba ta same ta ba, ta goce.

“Ba ki san haushinki nake ji ba? Mara kunyar yarinya, ana ce miki ga annabi kina runtse idanu, to ki sani, wadannan din dai sune naki wlh, kuma gaskiya suke fada miki. Yar banza mara hankali da tunani, sokuwa, ace kaf kayanki kin kwashe kin sayar kin ba miji, to na ga Uban da zai kara yi miki wasu kaya nan gaba bare ki sayar. Ni dai kwandalata ba ta ciwon kai wurin siya miki wani abu kuma, zan dai yi miki addu’ar haihuwa lafiya. “

Hawayen da ba ta shirya zubarsu ba, suka fara yi mata zarya, musamman yadda ta ji dakin ya kaure kowa na fadar mummunan kalamai a kanta, tare da yi mata albishir din nadama a nan gaba. Hakan ya sa sautin kukanta ya fara fita a hankali.

A daidai lokacin kuma Alhaji ya shigo gidan don yin alwalar la’asar.

“Lafiya waye ke kuka a nan dakin?”

Duk suka yi tsit, don basu ji shigowar shi ba ma.

“Ko ba kwa ji ne?”

“Lafiya ƙalau.” Aunty Ayyo ta amsa.

“Lafiya kuma ake kuka, wacece ke kukan?”

Shiru suka yi har sai da ya kara tambaya cikin tsawa, kusan a tare suka ce “Fatima ce.”

“Ina Fatiman?”

Fatima da ke zaune a kan kujera kuka ya hana ta amsawa.

“Tana ina wai?” ya kuma tambaya a tsawace.

Dalilin da ya sanyata mikewa ta fito tsakar gidan, har a lokacin kuka take yi.

” Me ya faru? ” ya tambaya hade da kallon ta.

” Ba komai. ” ta amsa cikin kuka.

” Ke Hajara! ” ya kwadawa Mama kira.

” Me kuka yi mata? ” ya yi tambayar hade da kallon Mama da ta fito tsakar gidan.

“To me zamu yi mata Alhaji. Gaskiya ce kawai aka fada mata, shi ne take kuka.”

“Wace irin gaskiya ce kuka fada mata?”

“Yanzu saboda Allah Alhaji, ace yarinyar nan da daya da biyu, ta tsince duk kayanta ta siyar ta ba Mustapha kudin. Yanzu haka fa tunkiyarta ta nan gidan ma ta siyar, fridge, inji, kai har zannuwan haihuwar Hana ta siyar dasu.”

Alhaji ya dauke idonsa daga kan Mama ya mayar kan Fatima, kafin daga bisani ya mayar dasu a kan Maman yana fadin” To shi ne kuke fada mata me? “

” To yanzu saboda Allah ya kamata ace tai ta siyar da kayan ta? ” Mama ma ta yi maganar hade da kallon Alhaji.

” Yanzu kamar ba ke ce kike cewa ba ki son Fatima ta auri wani a waje, sai dan gida , dana tambaye ki dalili kika ce min ba ta da hankali. Yanzu kuma ta yi hankalin nan ma ya zama abun fada. Ni ban ga wani abun damuwa don Fatima ta siyar da kayanta ta rufawa mijinta asiri ba, hasalima abu mai kyau ta yi. Allah ya yi mata albarka, na kuma godewa Allah da na ga wannan ranar da idona, Fatima har ta san ta rufawa kansu asiri Alhamdulillahi. “

” Alhaji ba ko wane namiji ake ba amana ba. “

” Hajara ina magana ne a kan Fatima ba Mustapha ba, idan Mustapha ya ci amanar Fatima shi da Allah, amma ita ta yi abin da ya dace, kuma ina alfahari da ita. “

Mama ba ta kuma cewa komai ba, ta koma daki, dama sun Aunty Ayyo sun yi shiru kamar basu a gidan.

Ya mayar da hankalinsa kan Fatima da take duke tana kuka.

” Ki share hawayenki kin ji, abu mai kyau kika yi, kar ki damu da maganarsu, ke dai kin yi ne don Allah, to Allahn ya gani, kuma sha Allah ba zai tabar da ke ba. Ni mahaifinki ne, daga yau idan kina da matsala kai tsaye ki zo wurina, zan magance miki sha Allah. Sannan idan har ina da rai, zan cika miki burinki na yin karatu in Sha Allah. “

” Na gode ” ta fada cikin muryar kuka.

Jin an kira sallah ya sa shi saurin nufar sashen shi don yin alwala.

Ita ma daga nan sai kawai ta nufi kofa, ba tare da ta nemi Hana ba

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 23Daga Karshe 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×