Skip to content
Part 25 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Sai da ta daidaita kanta, sannan ta shigo gidan, bangaren Inna kawai ta wuce, a lokacin Inna da Ummi duk sallah suke yi, ita ma sai ta dauro alwala ta jona su.

“Wai har kin dawo Aunty Fati?” Ummi ta tambaya daidai tana warware fara kal din hijabinta

“Eh.” Fatima ta amsa, hade da gyara zaman ta tana kallon Inna da ke cire hijabin da ta yi sallah.

“Ina za ki je?”

“Yawon juma’a.” Ummi ta amsa hade da murmushi.

“A dawo lafiya.”

“Allah ya sa.”
Ummi ta kuma amsawa a lokacin da take fita.

“Kun sha maganin Inna?”

“Eh na sha.”

“Amma kina jin sauki ko?”

“Alhamdulillahi. Ya kika dawo tun yanzu, ina kuma Hana din, ko har yayen ya tashi?”

“Lafiya ƙalau, akwai wani aiki da zan yi ne. Ita kuma bacci take yi shi ya sa na baro ta.”

Hira suka shiga yi da Inna har Fatima ta manta da damuwarta.

Sai da aka kira sallhr magariba sannan ta koma bangarenta.

Abin da ya ba ta mamaki shi ne yadda har isha’i ba a kawo Hana ba, ita kuma ta ki kiran kowa.

Tana shirin kwanciya ta ji shigowar Inna, dalilin da ya sanyata sanyo hijabi ta fito, don idan har ka ga Inna a bangaren lallai abu ne mai muhimmanci ya kawo ta.

“Ke wai har yanzu Hana, ni fa na kasa bacci kodai an kawo ta ban ji ba.”

Murmushi Fatima ta yi lokaci daya kuma ta zauna a kan hannun kujera.

“Ba a kawo ta ba Inna.”

“To lafiya?”

“Ni ma ban sani ba.”

“To ko za ki kira su ne?”

Wani murmushi Fatima ta sake yi sannan ta ce “A’a. To me zan ce idan na kira su Inna?”

“To kodai yayen ne ya tashi?” Inna ta kuma tambaya

“To kila”

Duk suka yi shiru, kafin Inna ta ce “To Allah ya raya idan ma yayen ne.”

A zuciya Fatima ta amsa, lokaci daya kuma tana yi wa Inna rakiya.

Kamar wasa dai Hana kwana biyu ba a maido ta ba, wannan ya tabbatar masu da cewa lallai yaye Hana aka yi.

Sai kawai Fatima ta mayar da hankalinta a kan rainon cikin ta

******

Ba Fatima ce kawai take farin ciki da wannan ranar ba, duk wani masoyinta ma yana murna da ranar.

Ranar da mijinta Mustapha ya kammala karatunshi na degree a bangaren Islamic law.

Tana jin kamar lokacin tafiya nata karatun ya zo, bautar kasa kawai ya rage mishi, tana fatan daga nan ya samu aiki mai kyau, ta yadda zai iya daukar dawainiyar karatunta, ko ba komai zai taimakawa Alhajinta da wani abun.

Farar powder silver line ta Kuma murzawa a fuskarta, bayan ta daga a kan sallayar da ta idar sallahr la’asar.

Tana kokarin rufe kofarta don zuwa dakin Inna, Hana ta shigo gidan a guje.

Cike da mamaki take kallon Hanan, fes da ita cikin kwalliya, kwanaki goman da ta yi ba ta ganta ba, sai ta ga ta kara girma da wayau.

“Ke da wa kuka zo?” Fatima ta tambayi Hana bayan ta rike mata hannu.

Gwaranci ta shiga yi, lokaci daya kuma tana kallon kofar gida.
A lokacin ne Fadila ta shigo tana dariya.

Ita ma Fatima sai ta fara dariya, tare suka jera zuwa dakin Inna, tana tambayar Fadila mutanen gida.

“Oyoyo! Oyoyo!! Ga yar yaye!” Inna ta fada lokaci daya kuma tana tashi daga kwancen da take.

Hana ma fadawa ta yi kan Innan tana nuna mata Biscuit din da ke hannunta.

“Waye ya siya miki?”

“Abbah.” Hana ta ba ta amsa.

Cikin dariya Fadila ta ce “Ita fa kowa sunan shi Abba.”

Gaba daya suka yi dariya kafin Inna ta ce “Dama ai jira nake ta cika sati biyu, in bi bayan ta. Na gaji da karar da nake yi.”

Dariya suka kuma yi kafin Ummi ta ce “Wai ba ta kuka kuma?”

“Ba kukan da take yi.”

Sai Ummin ta janyo Hana jikinta ta rungume cike da kauna tana fadin “Na yi kewarki yarinyata.”

A daidai lokacin Mustapha ya kuma shigowa gidan, ganin Hana ya sanya shi kara fadada fara’arshi.

Ita ma a guje ta fada jikinsa, ya rungume ta tsam, yana jin kaunar yarinya a jininsa.

Hira sosai ya zauna suka yi ta sha a dakin Inna, cike da farin ciki gami da nishadi. Kiran sallahr magriba ne ya tashe shi, tare suka fita da Fadila yayin da ta bar Hana a gida.

Ita ma Fatima bangarenta ta wuce ta bar Hana wurin Inna.

Sai da aka yi sallahr isha’i sannan Mustapha ya shigo gidan.

Kamar ko wane lokaci dakin Inna ya fara wucewa, ya yi mata sannu da dare, sannan ya shigo nasu bangaren.

Fatima zaune a kasa tana shirya kayan Hana da Fadila ta kawo, wadanda duk a can aka yi mata su.

Bismillah ya yi hade da zama a gefen ta.

“Uwar biyu!”

Murmushi ta yi kafin ta ce “Allah ya kawo masu albarka.”

“Ba kya jin tsoro?” ya yi tambayar bayan ya tsare ta da ido

“To tsoron me, bayan ga ka.” suka yi dariya a tare, lokaci daya kuma ya janyota zuwa jikinsa.

“Hana ta yi wayau Fatima, ta yi saurin girma”

Murmushi ta kuma yi, kafin ta ce wani abu ya dora

“Kin san me?”

Kai ta girgiza alamar a’a

“A kullum na kalli Hana, na kan cika da mamaki wai ƴarki ce da ni, abu kamar wasa ga shi kina dauke da cikina na biyu, Fatima ban taba kawo wannan a raina ba.”

Ajiyar zuciya ta sauke hade da gyara kwanciyarta a kan jikinsa.

Hannunsa ya dora a kan cikin ta yana shafawa a hankali,” Fatima ina rokon Allah ya ba ni ikon kyautata miki, ta yadda kowa zai yi alfahari da ni a matsayin mijinki. “

” Ya Mustapha ka yi min koma…”

“Ban yi miki komai ba, ban yi komai ba Fatima ina fatan dai in yi” ya yi saurin katse ta.

Jin taba kofa ne ya, sanyata saurin janyewa daga jikinsa, hade da kallon agogon da ke manne a jikin bango. Karfe goma da yan mintuna “To waye?” ta tambaya a zuciyarta, a zahiri kuma bin Mustapha ta yi da kallo wanda ya fita hade da tambayar waye.

Jin muryar Ummi ya sa Fatima mikewa da kyar zuwa kofar, sai dai kafin ta isa wurin, har sun nufi dakin Inna. Dalilin da ya sa ta bi bayansu.

Yanayin da ta ga Inna a ciki ba karamin tayar mata da hankali ya yi ba.

Mustapha ne kawai ke iya yin wani abu, amma ita da Ummi sai ido, ko sannu da jiki ma basu iya bude ba ki su yi wa Inna.

Misalin 11pm Mustapha ta fita neman likita, ba jimawa suka dawo tare ya ba Inna taimakon gaggawa har ta samu bacci.

Su duka ukkun basu runtsa ba, sun tasa Inna gaba ne, har zuwa lokacin da ta farka.

Kan Fatima ta fara sauke idonta “Me kike yi a nan ba ki je kin kwanta ba?”

“Ba komai, sannu Inna ya kike jin jikin?” karon farko da ta yi magana.

“Akwai sauki. Ina Yar yaye?”

Murmushi ya subucewa Fatima lokaci daya kuma ta nuna mata Hana da ke kwance a kan cinyar Mustapha tana bacci.

“Ummi fa?”

Cikin kuka ta amsa “Ga ni nan Inna”

“To kukan me kike yi?” inna ta tambaya hade da kallon Ummi

“Ba komai”

Yunkurawa Inna ta yi da kyar hade da tashi zaune.

“Ummi damuwarta kar in mutu in bar ta.” sai kuma ta yi murmushi kafin ta dora
“To ya za a yi idan hakan ya kasance, ga yayanki nan ai, sannan ga Fatima na tabbata Fatima za ta zamu uwa a gare ki Ummi, ki daina damuwa.”

Maimakon Ummi ta sausauta kukan, sai ta kuma fashewa da kuka, kukan da ya sanya Mustapha mikewa ya bar dakin, don zuciyarshi karyewa take kamar yadda yara suke karya kara idan zasu yi wasan mota.

Jin yadda Inna ke ta hira dasu Fatima sai ya koma daki ya kwanta, haka nan ya kwanta, amma ba ya jin wani abu mai kama da bacci.

Misalin karfe uku ciwon Inna ya kuma tashi, a, daddafe suka kai asuba.

Ana fitowa masallaci suka dauki hanyar Katsina.

Daga Ummi har Fatima tamkar an zare masu dukkan wasu lakokin jikinsu, haka suka wuni ba mai umm bare uh-uh-uh. Wani lokaci kuma Ummi sai ta fashe da kuka, Fatima ke lallashinta.

Basu samu Mustapha ba sai bayan sallahr la’asar, da kanshi ya kira su.

In da yake shaida masu jikin Innan da sauki, amma Baba Azumi za ta zo gobe nan Sandamu daga nan ta wuto Katsina, saboda gado aka basu.

Koba komai sun dan samu natsuwa, duk da su biyun babu wanda ya samu ya runtsa sai gab asuba.

A firgice Fatima ta farka, saboda mafarkin da ta yi, ta jima a gefen gado zaune bayan ta karanto addu’ar da ake yi, yayin da aka yi mummunan mafarki.

Jiki a mace tayo alwala, tana sallame sallah kiran Mustapha na shigowa.

“Ya Mustapha!”
Ta kira shi da muryar da ke nuna ba ta jima da tashi ba.

“Ya kuka kwana?” Daga can bangaren ya tambaya

“Alhamdulillahi!” ita ma ta amsa, kafin ta ce “Ya jikin Inna?”

“Alhamdulillahi. Ta ji sauki, zamu taho ma yanzu, don haka idan Baba Azumi ta zo ki ce mata ba sai ta zo Katsinan ba.”

“Ma Sha Allah! Allah ya kara sauki, Ya kuma tsare maku hanya.”

“Amin” ya amsa hade da yanke kiran.

“Ya Mustapha ne, ya jikin Inna?”

Ummi ta tambaya, don tun lokacin da Fatima ta fara amsa waya ta tashi.

“Akwai sauki, ya ce ma an jima zasu taho”

“Alhamdulillahi” Ummin ta fada lokaci daya kuma ta koma ta kwanta, don tana fashin sallah.

Zuwa karfe takwas sun gama kintsa gidan, Ummi ta yi wa Hana wanka ta gyara ta fes gwanin sha’awa.

Fatima na kara gyara dakin Inna su Baba Azumi suka iso mota guda, wai sun zo duba jikin Inna ne.

Dole Fatima ta dakata da gyaran dakin ta basu wuri bayan ta gaishe su, saboda yadda suka cika dakin.

Ummi ma gaishesu kawai ta yi, ta koma bangaren Fatima suka ci gaba da zamansu hade da hira jefi-jefi.

Da misalin karfe sha daya na rana ne motarsu Mustapha ta Parker a kofar gidan, wanda ya yi daidai da fitar sautin koke-koke zuwa kunnuwan Ummi da Fatima.

A tare suka yi waje zuwa tsakar gidan, wanda ya yi daidai da shigowar gawar Inna nade cikin tabarma.

Ummi dai faduwa ta yi a sume, Fatima kuma ta zama kamar zane, ba ta yi gaba ba, bare baya.

Sai da aka kama ta zuwa daki, duk abin da ake yi Allah ya hana ta bude baki ta yi magana, haka idanuwanta a bushe suke.

Kamar kuma wacce aka tsikara ta nufi dakin Inna, yanayin yadda take tafiya zai tabbatar maka da ta manta da cikin da ke jikinta.

Kai tsaye bedroom din ta nufa, Inna kwance ana shirya ta cikin kayan da sune karshen ado ga ko wane mummuni, komin talauci ko tarin dukiyarka.

Ba za ta iya tantance su waye a kan Inna ba, abin da ta sani kawai ta kutsa ta tsakiyarsu zuwa gaban Inna. Tsugunnawa ta yi hade da zubawa fuskarta ido.

Lokaci daya tsoron Allah ya shige ta, shekaranjiya sune tare cikin farin ciki, idan za a fada mata a daren jiya Inna za ta mutu lallai za ta musa, gaskiya ne babu abu ma fi dadi a duniya kamar rashin sanin ranar mutuwarka.

Tana jin Inna tamkar Mama, samun irin ta a matsayin suruka lallai ba karamin sa a ba ce ga ko wacce mace.

Tsawon zaman da suka yi, ba za ta iya fadin wani laifi kwaya daya jal da Inna ta yi mata ba.

Karon farko da ta dauke hawayen da suka wanke mata fuska, tun tana boye kukan har ya bayyana, dalilin da ya sa aka kama ta, zuwa dakin ta.

A can ma kukan kawai take yi, a yanzu dai ba ta da komai sai kukan, da shi ne zuciyarta ke rage nauyin da ta yi.

Inna wani bango ne mai karfi a gidan, ta ya zasu tayi su uku kacal ba wani babba a tsakaninsu, duk da Inna ba ta taba raba su fada ba, amma ganin idon ta, shamaki ne ga abubuwa da dama.

Bayan dawowa daga jana’iza, a hankali mutane suka fara raguwa a gidan, zuwa la’asar dai sai ma fi kusanci da Inna da kuma Fatima.

Don dakin Fatiman a cike yake da ƴan’uwa, abinci kam daga gidan Aunty Hauwa gami da gidansu Ya Bashir aka kawo.

Ba ta samu ganin Mustapha ba, sai karfe 11pm, a lokacin ya shigo wurin ta.

Ita kadai ce sai Hana da ke kwance tana bacci, Ummi kuwa tana dakin Inna, don rabon ta da bangarentun da rana.

Tun da ya shigo take bin sa da kallo, har ya zauna a kan kujerar hade d kwanta da kansa, hannunsa daya kuma a kan goshin sa.

Sosai ya rame ya kuma kara tsawo, ba ta yi mamaki ba, rayuwa za ta yi masa wahala ba Inna, yanzu dai su biyu suka rage daga shi sai Ummi, tsakanin shi da Ummin ba ta san wa ta fi tausayi ba.

“Ya karin hakurinmu?” ta yi maganar a tausashe

Ba tare da ya dago da yadda yake ba ya ce “An gode Allah”

Ta kuma daidaita muryarta hade da danne kukan da yake kokarin fin karfin ta

“Allah ya jikanta, Ya kyautata makwancinta, Ya gafarta mata dukkan laifukanta.”

“Amin na gode.”

Har zuwa lokacin bai dago ba, dalilin da ya sanya shiru ratsa falon, kafin Fatima ta yunkura zuwa kitchen.

Koko (kamu) ta dama mishi, har ta gama dama kamun kuka take yi, sai lokacin da za ta dawo falon ne ta yi kokarin tsaida hawayen nata.

Kamar tun da ta tafi bai motsa ba, domin a yadda ta same shi bai yi kama da ya motsa din ba.

“Ya Mustapha don Allah ka dan sha kokon nan, saboda na san ba ka ci komai ba. Don Allah kar ka ce min a’a” ta karasa maganar da kyar saboda kukan da yake yi mata kutse.

Karon farko da ya sauke ajiyar zuciya hade da gyara zaman shi.

“Ba na son cin komai”

“Na sani, kawai alfarma ce za ka yi min don Allah”

Wannan lokacin dagowa ya yi hade da zuba mata cikin hasken touch light din da ya gauraye dakin.

“Yau na rasa Inna Fatima, ta tafi ta bar ni ni kadai ba kowa, ina jin duniyar nan ta yi min fadi, kamar wasa na rasa ta.”

Yanayin yadda ya yi maganar sai ya kashe jikinta dalilin da ya sanya ta yin shiru.

“Ke kawai, Ummi da kuma Hana suka rage min yanzu a duniyar nan ma fi kusanci da ni, ko ya zan fara rayuwa ba Inna? Ita ce mai dora ni hanya idan na kauce, ta gyara min idan na ɓata, ta tuna min idan na manta…”

“Please Ya Mustapha don Allah ya isa haka, ka yi mata addu’a, ita ta fi bukata a yanzu, ita ce hanya daya tilo da za ka nuna mata soyayyarka, hade da nuna mata cewa kai din ɗa na kwarai ne a gare ta.”

Bai tanka ba, illa kansa da ya sadda kasa, wannan ya tabbatarwa da Fatima kuka yake yi.

Da kansa ya daga kan hade da share hawayen nasa, lokaci daya kuma ya karbi cup din kokon, ba wai don yana jin dadi ba, kawai dai yana sha ne don Fatima.

Zufa ce ta keto mishi ko ta ina, yayin da jikinsa ya mutu, bai san lokacin da ya zame a kan kujerar ya kwanta ba.

Tun yana jin buruntun Fatima har baccin da bai shiryawa zuwan shi ba, ya yi awon gaba da shi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 24Daga Karshe 26 >>

1 thought on “Daga Karshe 25”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×