Skip to content

Daga Karshe | Babi Na Biyu

  • by
3
(2)

<< Previous

Yadda ta bar dakin haka ta same ta, ba ta bata lokaci ba ta shiga gyarawa cikin sa’a daya, ta gyare dakin tsab, kafin ta fito zuwa dakin mama da take zaune tana hada lissafi,

“Ina kwana Mama?”

“Sai yanzu ne kika ganni? To ni ma ban ga kwanan ba.”

Ta marairace,

“ki yi hakuri, dazu na gan ki tare da wancan dan sa’idon ne.”

“Waye dan sa’ido?” Mama ta tambaya hade da kallonta cikin daure fuska.

“Ki yi hakuri” Fatima ta kuma fada a karo na biyu.

“Ke bana jin dadin yadda kika dauki Jamilu, kodayake ba shi kawai ne kika raina ba, ni ma kin raini ni.”

“Kash!” cewar Fatima.

“Karya na yi?”

“Ki dai bar fadar haka Mama, amma duk duniya bayan Baba ina da wata kamar ke ne? Ni kawai bana jin dadin yadda kike goya mishi baya a kan komai Mama.”

“To bayanki kike so in goya?”

“Ko ba ki goyi bayana ba, kina nuna mishi so ya yi yawa wallahi.”

Wannan karon Mama sai da ta murmusa dalilin maganar Fatima.

“Dole in nuna wa Jamilu so, saboda ni kadai yake da. Mamanshi yayata uwa daya uba daya, ta nuna mun so da gata ita ta zame mun uwa da uba, ban nemi komai na rasa ba a lokacin da take raye. Ban yi kukan rashin uwa ba. Watarana suka kawo mun ziyara daga garin Daura, bayan zuwansu ne na ce ta bar mun Jamilu in yayeshi, ba ta yi gardama ba ta bar mun shi. A hanyarsu ta komawa suka yi hatsari, Baban Jamilu take ya rasu, ita ce dai aka kai asibiti, ita ma kwananta daya ta rasu. Jamilu bai cancanci in kaunaceshi ba?”

Fatima da jikinta ya yi sanyi ta gyada kai da kyar,

“ya cancanta, ai ban san haka abun yake ba. Allah ya jikansu, to wai dangin Babansu fa Mama, ni ban taba ganinsu ba?”

“Dalilin da ya sa nake kara linka son da nake mishi kenan, asalin babansu dan Nijar ne, ya shigo garin nan, mutumin kirki ne sosai, ga zuciyar nema, ya nemi auran yayata aka amince mishi bisa jagorancin tsohon hakimi. Yayata dai sau biyu tana zuwa garinsu, amma babu wanda ya taba zuwa nan har yanzu da nake ba ki labarin nan.”

Fatima da hannunta yake kan habarta, ta janyeshi a hankali hade da jeho wata tambayar,

“To dama a garin nan suke zaune ko a Daura?”

“A garin nan suka fara zama, bayan rasuwar hakimi sai ya koma Daura da zama, ya ci gaba da kasuwanci. Kuma Allah ya dafa mishi, ban da Allah ya yi mishi rasuwa da yanzu yana daya daga cikin manyan masu kudi a Daura.”

“Allah sarki! Wallahi na ji ina ma na san su, sosai na ji ina kaunarsu.”

“To ki kaunaci yaronsu, shi kawai suka bari a duniya, don dama sai da suka shekara 7 da aure ta samu ciki, ni kuwa a lokacin yarana uku.”

“Kin riga ta aure kenan?”

“A’a, amma dai shekara daya ne tsakanimu, a shekarar da na yi aure, shekarar Mamarmu ta rasu.”

“Allah ya jikanta, ya gafarta mata. Mama ba ki da hotonsu?” Karamar dariya Mama ta yi kafin ta ce,

“babu gaskiya.”

“To Mama Babana fa?” Fatima ta kuma tambaya.

“Babanki? Babanki ai dangata ne, cikin gata ya taso da kuma dangi. Yayanshi ne hakimin Sandamu, bayan Yayanshi ya rasu sai ka nada d’anshi, shi ne kuma ke auran Auntynki Hauwa, ai kin san wannan?”

Murmushi ta yi “Na sani kam.” Yau dai Mama da Fatima ‘yar dadi a ka yi. Duk ayyukan gidan Fatima ce ta yi, har girki duk ita ta yi. 4:13pm Mama ta leka dakin Fatima in da take kwance tana karasa karatun littafin Rayuwar Raihana. “Islamiyar fa?” “An koremu ni da Zainab.”

“Kora kuma? To me kuka yi?”

“Ba komai fa.”

“Karyarki, dole akwai dalili.”

“Mama daga tambaya ne fa.”

“Ku dai kuka sani. Ita kuma Zainab din ta ci gaba da biye miki.”

Sallamar Jamil ce ta dakatar da ita,

“Har ka dawo? Wallahi yanzu na gama tunaninka a zuciyata.”

Ya dan yi siririn murmushin da ya sa gefen kumatunshi lotsawa gaba daya.

“Na dawo Mama. Ya gidan? Kin wuni lafiya?” Ya fada tare da risnawa Ta mika hannu ta karbi ledar da yake mika mata, bayan ta amsa gaisuwar,
“Muruci ne na sawo miki na san kina sonsa.”

“Aiko dai na gode, ai sosai nake son muruci.”

Murmushi ya yi lokaci daya kuma ya nufi dakinshi. Ita ma falonta ta koma, ta zauna don cin murucinta. Mintuna talatin ya fito sanye da kananan kaya, jar riga da farin wando tas, ya cika riga ta ko ina ta zauna das a jikinshi. Gashin kanshi bakikkirin me santsi irin na fulanin Nijar ya kwanta a fatar kanshi. Kamshi me dadi yana fita a jikinshi ya shigo falon. Sai da ya kara gaishe da Mama sannan ya zauna a daya daga cikin kujerun, a daidai lokacin ne kuma Fatima ta shigo da daurin kirji hannunta rike da littafi ta duka hade da daukar muruci daya ta bare tana ci. Tun da ta shigo Jamil ke kallonta, har zuwa yanzu da ya ce,

 “Yau ba islamiya ne?’

“An kore ni.” Ta ba shi amsa kanta tsaye tana tauna murucinta.

“Je ki kawo mishi abinci.” Mama ta fada ba tare da ta kalleta ba Jamil ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce,

“Me ta yi aka kore ta daga islamiyar?”

“Sai Allah. Wai ita da Zainab aka kora, na san dai banza ba ta kai zomo kasuwa dole wani abu ya faru.”

Fatima ta shigo dauke da faranti ta aje a gabanshi. Ruwan da ke cikin kofin silba, ya dan zuba kadan saboda yadda ta aje tiren. Ya ja siririn tsaki,

“Wai ke ba kya abu a natse ne? Komai aka ce ki yi sai kin yi kuskure.”

“Kuma ka sani sai ka yi magana, tun da ka san haka nake me ye na magana, ku bar ni a haka, a hankali Allah zai shirya ni. Kowa dai ban yi daidai ba.”

Duk yadda Mama ta so rike dariyarta ta kasa.

“Wai yaushe hutunku zai kare ne?” Mama ta tambaya har lokacin tana dariya.

“Saura sati uku.”

“Gara dai ya yi ya kare, ko zuciyar yarona ta huta, ki fita ki koma dakinki sai na neme ki.”

Bayan fitarta ne Jamil ya sauka kasa hade da janyo tiren abincin a hankali, ya fara kokarin bude kular,

“Mama ni wai shekarar yarinyar nan nawa ne?”

“Sha bakwai”

“Amma shi ne har yanzu ba ta natsu ba.”

Ya fada a lokacin da ya kai dufadukan shinkafar manja da wake hade da kifi a bakinshi. Ya lumshe ido yayin da yake taunawa.

“Ban san ya kike girkinki ba, idan kin sanya kifi baya karni.”

“Wannan ma ba ni ba ce Fatima ce, amma ina matsa lemon tsami ne.”

“Ba karya kam, indai abinci ne ta iya. A duniyarta ma ina jin abun kirkin da ta iya kenan.”

Sosai mama ta yi dariya.

“To girki ai shi ne mace Jamilu. Kuma Fatima tana da kokari fa.”

“Eh tana da kokari, amma shiririta ta fi kokarin yawa.”

“Haka yawancin masu kokari suke ai.”

“Gara da kika ce yawanci, ni ba gani ba, ina da rawar kai ne irin nata?” Mama ta kuma murmusawa

“Sannu magori, wasa kanka da kanka. Amma kai du ka hada, natsuwa, hankali, basira da kuma tarin ilmi”

Suka yi murmushi a tare. Haka suka rika yin hira har ya gama cin abincin ya fice.

*****

Alhaji Musa Sandamu, mutum ne da shekarunshi suka tasar ma 65 ma’akaci ne a ma’aikatar aikin gona. Mutum ne mai dattako, hakuri da kuma jajircewa a kan abin da ya sa gaba Ya sa muhimmanci ilmi sosai, shi ya sa ba ya ganin kyashi ya kashe ko nawa ne a kan ilmi Allah ya azurtashi yara sha bakwai (17) tare da matarshi Hajara wacce kowa kan kira mama. Duk da Allah bai raya mishi su duka ba, goma ne a raye, shida mata hudu maza yawansu bai hana ya wadatasu da ilmi ba. Ya aurar da bakwai, mata biyar maza biyu uku suka rage mishi mace daya Fatima sai maza biyu Kabir da Abdullahi. Sai ko Jamilu da yake riko Alhaji Musa ba shi da zafafa abu, idan aka ja, ya ja, ba’a saki ba to shi sai ya saki. Baya son hayaniya. A halin yanzu yana aiki ne a Daura, a can kuma yake zama sai jumu’a yake zuwa gida.

Kamar yau ma da ta kasance Jumu’ar ya iso tun misalin goma na safe. Haka yaranshi da suke aure a kusa duk suna gidan, sun zo gaishe shi. Shi ma haka ya basu lokaci ya rika ganawa dasu daya bayan daya yana jin matsalolinsu, har dai lokacin masallaci ya yi. Bayan fitarshi ne suka shimfida manyan tabarmi a bishiyar dalbejiyar da ke tsakar gidan Hirar tasu duk a kan matsalolin zamantakewar aure ne. Aunty Maryam ce ke fada masu wata matsala da take damunta ta karashe zancen nata da,

“wallahi a ranar Aunty Hauwa ranar ko bacci kasawa na yi. Na yi kuka kamar raina zai fita.”

Fatima da ke can gefensu kwance tana sauraren hirar tasu, fashewa da dariya ta yi,

“Wallah ni mamaki kuke ban, idan kuka ce kun kasa barci don wani abu. Ni fa bacin rai ko tashin hankali bai taba hanani bacci ba, sai dai idan ban kwanta ba”

“Mtswww!” Aunty Aisha ta ja tsaki.

“Ke idan ana maganar masu hankali wa ke sanyaki. Kuma me kika sani a cikin duniyar?”

“Wai sai kui ta ce mun ban da hankali. Wai me nake yi na hauka ne?”

“Yo Fatima mahaukaci ai ba sai ya yi duka ko ya ya tafi tsirara yake mahaukaci ba.” Cewar Aunty Hauwa.

“Ina fa jin kunyarki. Ita me cewa ban da hankalin ai ba fi na hankalin ta yi ba.”

Aisha da take kwance ta yi saurin tashi zaune,

“Ta shi ki bar gurin nan, bana ciki da rashin kunyarki, wallahi yanzu sai in lakada miki dukan tsiya, shekaru hudu masu kyau tsakanina da ke.”

“Amma hakan baya nufin kin haife ni.”

Fatima ta fada a hankali duk da wasu sun ji me ta fada ciki kuwa har da Aisha. Aishar ta rarumo takalmi me tsini ta wurgawa Fatima Cikin rashin sa’a sai a goshin Malam Mustafa da ya shigo, don yi wa Alhaji Musa sannu da zuwa. Suka dauki sallallami gaba daya. Wanda hakan ya sa Mama da ke cikin daki fitowa, hade da tambayar,

“Lafiya?” Aunty Hauwa ce ta yi mata jawabi.

“Subhanallah!” Mama ta fada lokaci daya kuma tana kallon Mustafa da ya ga wani duhu hade da katsewa jijiyoyin da ke kai mishi sako lungu da sakon jikinshi. Gurin ya dafe da tuni ya kumbura, ya karasa kan wani dutse ya zauna. Yayin da su kuma suka yo caaaa a kanshi suna mai sannu Fatima da ke can gefe daya tana kallonsu sosai abun ya ba ta dariya. A zuciyarta kuma cewa take an rama mun dukana. Aisha ta juyo kan Fatima,

“Wallahi yau ko cikin uwarki za ki koma sai na fito da ke na yi miki duka.”

“Idan kin zagi uwata ta ki kika zaga, tun da dai uwarmu daya.” Cewar Fatima tana tabe baki. Aisha ta harzuka ta yi kan Fatima a guje. Ita ma kamar jira take sai ta yi hanyar waje da gudu. A daidai lokacin ne kuma Jamil da Alhaji Musa suka dawo daga masallaci. Fitar Fatima a guje suka rafka karo da Jamil sosai ta bugu, shi ma sosai ya ji zafin karon da suka yin.

“Subhanallah! Ya da gudu haka?” Alhaji Musa ya tambaya.

“Aunty A’i ce za ta buge ni.” A tsakar gida ya ga Aishar tsaye, tana ta huci kamar za tai aman wuta.

“Ya kuke haka da girmanku Aisha?”

“Baba Fatima raininta ya yi yawa, ga ni take kamar ni sa’arta ce, a dalilinta har na buge Ya Mustafa da takalmi. Allah rashin kunyar yarinyar nan ya yi yawa.”

“Addu’a za ku rika yi mata, ba aibata ta ba.”

 “A toh! Ni ma haka na ce.” Caraf! Fatima ta karbe maganar.

“Wallahi sai na nemi maganin baki me kyau na rika sha, kar bakinsu ya kama ni.” Cewar Fatima tana kallonsu daya bayan daya.

Murmushi kawai Baba ya yi, ya wuce falonshi, in da Jamil da Mustafa suka bi bayanshi Mustafa na ta luluya goshinshi. Sai a lokacin ne Aunty Maryam ta tuntsire da dariya tana fadin,

“Kai Allah ya kyauta. Wallah Mustafa fa ya ji jifan can.”

Aunty Hauwa ma ta kwashe da dariya,

“Yo ba dole ba, ai bai san da zuwanshi ba.” Aishar ma dukawa ta yi tana dariya.

“wallahi ya ba ni tausayi. Ai wallahi yarinyar nan ban da Allah ya kawo Baba da na ci ubanta da duka.”

“Ki kyaleta, kika biye ta sai kui ta yi, ai ba’a biyewa Fati.” Cewar Aunty Hauwa har yau tana dariya.

“Abin da ya sa kenan kullum raininta da rashin kunyarta ke gaba. Saboda ana kyaleta.” Cewar Maryam “Kin san me? To ranar cewa Bilkisu ta yi, wai ko ta tsinewa Bilal, tsinuwar ba za ta kama shi ba, tun da ai ba haihuwarshi ta yi ba, C.S aka yi mata aka cire shi.” Aunty Hauwa ta fada cikin dariya.

“Yo sun fi kusa da Bilkin ai, ko Yaya Bashir din bai isa ya shiga tsakaninsu ba.” Aisha ta fada hade da gyara zamanta.

“Wani lokaci sosai shirmenta ke ban dariya.” Maryam ta fada hade da dariya.

Haka suka yi ta hira sai yamma suka watse. Sannan gidan ya koma shiru. Daga Mama, Jamil sai Fatima da Baba. Don Kabir yana Birnin Kebbi a can yake aikin police da mukamin Asp. Abdullahi kuwa ya fi zama gidan Bashir. Kwanan Alhaji Musa uku ya koma gurin aikinshi cike da kewar iyalanshi. Ba shi kawai ne ya yi kewa ba, Fatima ma sosai ta yi kewarshi, don kuwa shi ne yake tsaya mata a komai, shi bai taba kallon komanta shirme ba, sai ya ce kuruciya ce, watarana ba za ta yi ba. Shi kullum yarinya yake kallonta sabanin yan’uwanta da kullum suke kallon ta girma amma tana halim yarinyata.

*****

A zaure suka ci karo ya kalleta,

“Wai ke ba za ki koma islamiya ba ne?”

“Ba ka kore ni ba?” Ta ba shi amsa ta na hararrashi kasa-kasa.

“Sati biyu na koreku, kuma satin biyu ai ya cika Zainab tuni ta koma. Ke me ya sa ba ki koma ba?”

“Haka nan.” Ta kuma ba shi amsa hade da jefar da kanta gefe guda.

“Kin yi ma kanki.” ya fada lokacin da yake rabata zai wuce.

“Mun yi wa kanmu dai.” Ta fada kasa-kasa.

“Ki ka ce?” Ya tambayeta bayan dakata da tafiyar da yake.

“Ba komai.” Ta ce a lokacin da ita ma ta fara tafiya son shiga gida.

“Na ji ki ai, me ya sa mu ka yi wa kanmu? Wallahi sai kin amsa wannan tambayar. Dariya ta kama ta don jin ya ji abun da ya fada.

“Ba haka na ce ba fa?”

“Just answer me.” Ya fada hade da bata rai alamar ba wasa Ita ma sai ta dakatar da dariyar tata hade da fadin,

“To idan ka kara mun kai ma ai lada za ka samu, ka ga ka rasa ladan kenan kai ma.” Ya zuba mata ido yana kallonta, tun tana jure kallon, har ta yi kasa da idonta tana wasa da yatsun hannunta. Ta kasa fassara kallon na shi. Bai yi magana ba, ya fice, ita ma sai ta shige cikin gida tana fadin,

“Idan ma haushi ka ji, can ta matse ma, ba kai ne ka matsa sai na amsa ba, na kuma amsar sai ya zama damuwa, ni an fada ma jan ido na tsorata ni ne.”

“Ke da wa kike ta surutu ko sallama ba ki yi ba, kika fado mun.”

“Ni da Ya, Malam Mustafa.” Mama ta dan yi murmushi jin yadda ta kira sunan.

“Kun fi kusa ke da shi. Yauwa wai me ki kai, ake nemanki a police station? Dazu wani police ya zo wai ki zo aka ce ba kya nan ya ce zai dawo”

Ta dire maganar hade da kallon Fatima, wacce sam maganar ma ba ta; ba ta tsoro ba. Illa tabe baki da ta yi ” Yo ko ina nan ma zuwa zan yi da waccan uwar ranar, ai sai dai idan da mota suka zo.”

Sallamar da aka yi ne ta katse Mama daga maganar da ta yi niyyar yi. Tare suka amsa sallamar, yaron ya shaida masu wani police ne a waje yake neman Fatima Gaban Mama da dama tun dazu yake faduwa, sai ta kuma jin dasssss!

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×