Skip to content
Part 27 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Da misalin karfe biyu na dare wani irin matsanancin ciwon mara ya farkar da ita.

Duk wata addu’a da ta zo bakinta haka ta rika tofawa a ruwa tana sha.

Kasancewar dry labour take yi,a daddafe ta yi sallahr asuba sannan ta kira Aunty Hauwa.

Jin abin da Fatima ta fada mata, ya, sanya Aunty Hauwa tahowa da direban gidan Hakimi.

Koda suka iso ma basu bata lokaci ba, suka nufi asibiti, Ummi kuma ta hau kintsa gidan da nema masu abin da zasu ci ita da Hana.

Mintuna ashirin masu kyau basu hada a asibitin ba, Fatima ta sullubo kyakkyawan yaronta lafiyayye.

Cike da zumudi Aunty Hauwa ta kira No Mama don ta shaida mata haihuwar Fatima, saboda cikin Fatima na daya daga cikin abin da Mama kullum take faman magana da fatan a rabu lafiya.

Sai dai sakon da Maman ta fada mata ya yi matukar tada mata da hankali hade da yanke duk wasu na’urori da suke zirga-zirgar kai sako zuwa jikinta.

Sannu a hankali ta janye wayar a kunnenta, lokaci daya kuma tana maimaita kalmar da Mama ta fada mata yan sakanni baya. “Alhaji ya rasu Hauwa, Allah ya yi wa Alhaji rasuwa.”

“Alhaji ya rasu” Ta kuma fada a hankali hade da zama jagwab akan dandamalin da ke kusa da ita.

“InnaLillaHi Wa’inna ILaiHiRajiun” kawai take maimaitawa, kafin daga bisani ta fashe da kuka mara sauti, da ace ta san Alhaji zai rasu, tabbas da ba ta baro asibitin ba, da ta yi zaman ta ta ci gaba da ganin motsin shi hade da jin sautin muryarshi.

Ashe haka mutuwar mahaifa take, duk yadda kake ganin ba ka da bukata a wajensu, idan aka ce basu a doron duniya sai ka ji duniyar ta yi ma girma, tamkar kai kadai ne kake yawo a cikinta ba kowa.

Ta jima a wurin zaune tana kuka, kafin ta daidaita kanta zuwa wurin likitan, kai tsaye sallama ta nema ma, tun da Fatiman lafiyarta ƙalau daga ita har Babyn.

Gidan Mama Aunty Hauwa ta ce direban ya wuce dasu, sosai Fatima ta yi mamakin umurnin, amma sai ta tuna kila ko don ba Inna ne.

Tun daga nesa ta rika kallon mutane suna bullowa from every corner suna burki a kofar gidansu.

Abin da ya yi mata iyaka da duk wani kuzarin da ya rage a jikinta, ba ta tsinke da al’amarin ba, sai lokacin da ta ji ana mata sannu hade da gaisuwa, yayin da wasu ke fadin “Alhaji ya tafi, kuma Alhaji ya dawo.” wannan furucin shi tabbatar mata da ta yi rashin bango abun jingina a gare ta.

A wannan ranar ne ta san kuka ma rahama ne, don duk koke-koken da ake yi digon hawaye bai sakko mata ba, sai dai numfashinta da take ta kokawa da shi.
Gidan ya kara rikicewa da kuka lokacin da aka shigo da gawar Alhaji, amma digon hawaye bai sauka a idon Fatima, ajiyar zuciya kawai take sauke wa mai nauyi, yayin da take jin kukan ya ishe ta, ina ma kowa ya yi shiru, babu abin da take so, illa ta ji kamar duniyar ba kowa.

Tana kallon yan’uwanta na zuwa kan gawar Alhaji, amma ita ko yatsanta kasa dagawa ta yi, ba ma za ta iya zuwa ta yi masa kallon karshen da ake fada ba, shi ne karshen tashin hankalin da take ganin za ta iya fuskanta a duniya.

Alhaji kwance, baya motsi, ba zai iya fada mata abin da ya saba fada mata ba “Ki yi hakuri kin ji Fatima, duk a cikin yarana ke na fi tausayi.” ita ce kalmar da kullum idan zasu hadu sai ya fada. Ita kanta tausayin kanta take yi, saboda yanzu dai a cikin ƴan’uwanta ita kawai ce ba ta da madogara, amma su kam ko wacce tana da abun yi, tana cin gashin kanta.

Wanda yake ta kokarin tallafa mata don ita ma, ta samu ta tsaya da kafafunta yau ga shi kwance a matsayin gawa.

Babu wanda ya kula da ita, kowa ta kansa yake, ruwan wanka ma sai bayan la’asar Aunty Lami ta dora mata, ita ce kuma ta kama ta zuwa bayi, hatta wankan ma ita ta yi mata.

Sai a lokacin ta fahimci Fatiman Sam ba ta cikin hankalinta.

Dakin Jamil ta bude ta kwantar da ita, lokaci kankane kuma ta damo mata kunu mai zafi, da kanta ta rika ba ta kunun har sai da ta shanye dan ƙaramin cup, sannan ta kwantar da ita.

A hankali jikinta ya fara rawa, har kuma abun ya zarce hankali, dalilin da ya sa Aunty Lami fita a hanzarce ta kira Aunty Hauwa, dandanan suka cika dakin, ganin yadda yadda take jijjiga gadon kamar za ta raba shi da kasa, shi ya kara rudasu, suka kira Ya Bashir da kuma Kabir, basu bata lokaci wajen daukarta zuwa asibiti ba.

A can asibitin dai an tabbatar masu da tsinkau-tsinkau ne ke damunta, saboda yadda jininta ya hau sosai.

Daki na musamman aka shigar da ita, wanda babu hayaniya ko kadan, yayin da suka daure kafafunta da hannuwanta a jikin karfen gadon saboda gudun fadowa.

Ranar dai ku san duk yan’uwan Fatima a asibitin suka kwana.

Ita kuwa ko motsi ba ta yi, saukar numfashinta kawai yake bambanta gangar jikinta da gawa.

Kwananta daya a asibitin Mustapha da Jamil suka iso

Karon farko da Jamil din ya zo gida, tun bayan tafiyarsa da shekaru uku da yan watanni.

Mustapha dai karamin yaro ya zamewa su Mama, don kuwa kuka yake yi sosai, gani yake a ko wane lokaci Fatima za ta iya tafiya ta bar shi.

Don ko yanzu abin da ya raba dambe da fada, kawai zage-zage ne.

Jamil bai zauna ba, shi ma ya nufo asibitin, ba karamin tashin hankali ya shiga ba, ganin yanayin jikin nata, dalilin da ya sanya shi shige da fice a cikin asibitin har ya samu damar da zai iya duba Fatiman shi ma.

Jamil da kansa ya shirya zuwa Katsina ya sawo duk magungunan da yake bukata, daga shi har Mustapha babu wanda ya zauna tun da suka iso. Basu asibiti, basu wurin zaman amsar gaisuwa.

Ba ma su kadai ba, duk wasu dangi na jini babu wanda ya zauna, hatta Mama kullum sai ta zo asibitin. Asibitin ma shi ne ya koma gidan zaman makoki. Saboda mutane sun fi taruwa a nan, gami da shiga zullumi, duk wanda ya zo ya ga jikin Fatima, jiki a mace yake fita daga asibitin.

Har aka yi bakwai Fatima ba ta san ina take ba, ta kan dai dan bude ido wani lokacin, ta rika kallon mutane, duk da ba wani gane su take yi ba, hasalima bishi-bishi take kallon su.

Jariri kuwa Aunty Hauwa da Zainab ke kula da shi, madara ake ba shi, Hana kuwa da Ummi dama sun dawo wurin Mama da zama, dakin Fatima na da suka gyara. Mustapha kam dama zamanshi a asibitin ne, idan ya je gida to sai dai ko zai dakko wani abu ne da za a yi amfani da shi.

Karfe biyu na rana Jamil ya shigo gidan, a kan dutsen da suke zama don yin alwala ya zauna, hade da sadda kansa kasa.

Mama da ta fito dauke da goyon Hana wacce ke fama da zazzabi, ba ta san ma Jamil din ya shigo ba.

Tun da ya diro, bai yi zaman minti talatin gidan ba, ko wane lokaci yana asibiti, tsawon kwana biyar har ya dan rame.

“Jikin Fatiman ne?” Mama ta tambaya jiki a mace.

Ya dago kai yana kallon ta, maimakon ya amsa ta, sai ya ce “Wa kuka goya?”

“Hana ce.”

“Lafiya ko?”

“Kamar zazzabi ne a jikin nata”

Hannu ya mika alamun ta ba shi ita.

Sannu a hankali ta dora mishi ita a kan cinyarsa, ya dan tattaba jikin nata yana fadin “Akwai zazzabi kam.”

“To wai Jamilu haka zamu ci gaba da kallon yarinyar nan ita a mace, ita ba a mace ba?”

Sam baya son maganar amma dole ya ce “Ai haka dama cutar take, amma sha Allah muna sanya ran nan da kwana biyu za ta fara motsawa.”

“To Allah ya sa” cewar Mama da karyayyar zuciya.

Shigowar Mustapha ne ya sanyata mayar da hankalinta a kansa, lokaci daya kuma suka amsa mishi sallamarshi.

Har kasa ya duka ya gaishe da Mama, ya kuma mikawa Jamil hannu suka gaisa

A lokacin ne Hana da ke kwance kan kafar Jamil ta bude idonta, ganin Abbanta, sauka ta yi zuwa wajen sa.

Ya rungume ta yana jin yadda jikinta yake da dan zafi.

“Dama wurinka na zo?” Mustapha ya yi maganar yana kallon Jamil.

Bai amsa ba, amma ya mayar da hankalinsa a kansa.

“Na ce kodai zamu canjawa Fatima asibiti ne, ni na kasa gane ana ci gaba ne ko kuwa dai har yanzu a tsaye ake wuri daya.”

Mikewa Jamil din ya yi, hade da tura hannayensa cikin aljihu, tsawon minti daya bai ce komai ba.

Har sai da Mama tace “Ni ma ina goyon bayan Mustapha gaskiya, abu jiya I yau, ni dai kullum yadda na bar ta jiya haka nake samun ta gobe. Gaskiya ina ga a canja mata asibiti zai fi, hankalina ya kasa kwanciya a kan yarinyar nan, ace abu tsawon kwana takwas ba ta san wa ke kanta ba. “
” To ai abun ne an yi sakaci ya shiga jikinta sosai”

Mama ta kalle shi “Kamar ya an yi sakaci?”

“Tun ciki yana 20wk ake gane alamun ciwon, a kuma dauki matakin dakile shi, ban san me ya sa ita ba a yi hakan ba, har abun ya ci karfin ta.”

“Kai ni raba ni da wannan lissafe-lissafen naku na likitoci ka ji, Fatima ba ta taba tsallake ranar awo ba, sannan ba a taba ce mata akwai alamun wannan ciwon a tare da ita ba. Ni dai kawai maganar Mustapha ita ce abun dubawa.

“Shi kenan, mu jira nan da kwana biyun, idan babu wani ci gaba sai a canja.” cewar Jamil yana kallon wani sashi daban.

“Har kwana biyu?” karon farko da Mustapha ya sanya baki “gaskiya sun yi min nisa, ba zan iya jira har kwana biyu ba, gobe zan canja mata asibiti sha Allah muddin babu wani canjin da aka samu a daren yau.”

“To.” Jamil ya yi saurin amsawa lokaci daya kuma ya nufi dakin sa.

Sam Mama ba ta jin dadin abin da Jamil din ya yi wa Mustapha ba.

Sosai Mustaphan ke ba ta tausayi, ya fita a kammaninshi, Sam baya cikin hayyacinsa. Ya kara tsawo hade da yin baki.

Ta juya zuwa sashen da yake tsaye, da alama ma hankalinsa baya wajen

“Mustapha!” ta kira sunan shi, ba ta jira amsawarshi ba ta dora

“ka yi hak’uri, cuta ba mutuwa ba ce, na san ya kake ji, ka yi mata addu’a sha Allah za ta warke ka ji.”

Kai kawai ya daga alamar gamsuwa.

“Jikin Hana ma na ji kamar akwai zafi ba ta jin dadi ne?”

“Eh zazzabi ne, dama yanzu kawunta Jamil zai duba ta.”

Kwanciyarta ya gyara a kan kafadarsa sannan ya ce “Ba damuwa bari kawai in kai ta chemist”

Bai jira cewar Mama ba ya fice.

Ita ma Maman dakin Jamil ta nufa, zaune yake gefen gado, ya dafe kansa da duka hannayensa biyu, yayin da kansa yake kasa, ya zubawa lallausan carfet din ido, kamar yana jiran fitowar wani abu.

Shigowar Mama ne ya sanya shi dagowa, ba tare da ya janye tagumin ba.

“Me yasa ka yi wa Mustapha haka?”

“Me na yi masa?”

Ta bata rai sosai, sannan ta ce
“Furucinka bai dace ba Sam.”

“To Mama me kike so a yi masa, ya fadi zabinshi, kuma matarshi.”

“Duk da haka Jamilu, Mustapha abin a tausaya mishi ne, baya cikin hankalinsa, Fatima matarshi ce, tsawon kwanaki takwas tana kwance a asibiti kamar gawa ta ya hankalinsa ba zai tashi ba.”

Hannayensa ya sauke yana fadin “Amma ai yana ganin kokarin da ake yi ko?”

“Jamilu ka yi wa Mustapha uzuri, kar ka kara yi mishi furucin da bai dace ba ka ji na fada ma.”

“Ina Hana din?” ya kawar da waccan maganar.

“Babanta ya tafi kai ta chemist.” daga haka ta fice.

Tabe baki ya yi, lokaci daya kuma ya mike, ya shiga zagaye dakin kamar mai dawafi.

Shi kawai ya san yadda yake ji a kan ciwon Fatiman, haushin ma Mustapha yake ji, gani yake kamar sakacinshi ne ya haddasa mata ciwon.

Sai yanzu yake jin haushin kanshi da bai yi fada a wancan lokacin ya same ta a matsayin mata ba, ya rasa abin da ya hana shi daga hankalin kowa, sai yanzu yake ganin lallai ya yi wauta da ya bari Mustapha ya aure ta.

Tun daga lokacin da ya duro kasar, ya kuma ci karo da Fatima kwance a gadon asibiti hade da yaranta biyu, bai kara samun natsuwa ba, ya rasa abin da ya fi tsaya mishi a zuciya tsakanin mutuwar Alhaji da kuma Fatima.

Kiran wayar da ya shigo wayarsa ne ya katse shi, Dr Balarabe ne ke fada mishi Fatima ta motsa har ma ta tashi da kanta, amma ba ta magana.

Lokacin da yake jin karshen maganar tuni ya kai soron gidan, mashin ya tara a gurguje ya kai sa asibitin.

Allura da magungunan da ya ajiye wanda dama sai ta farka cikin hankalinta za a yi mata amfani dasu, ya kwasa zuwa dakin da take.

Sai da ya gabatar da duk abin da ya dace, sannan hankalinsa ya kwanta, don kuskure kadan kwakwalwarta za ta iya tabuwa.

Fatima kuwa duk abin da yake tana ji da kuma kallon shi, sai dai ba garai-garai take gani ba, shi ya sa take ganin kamar dai ba Ya Jamil ba ne, amma tsayuwa da yadda yake hada magunguna da yanayin allurar kamar shi.

Tun tana ji da kallon masu shigowa bayan fitar Jamil har bacci ya kuma dauke ta.

Ba ta farka ba, sai ana kiran sallahr magriba, wannan karon Mama ce zaune a gefen gadon, fitar Ummi ba jimawa da Hana, yayin da Mustapha ma bai jima da barin kofar dakin zuwa masallaci ba.

Ganin bakinta na motsi, sosai Mama ta matsa kusa da ita “Zan sha ruwa na ce” ta kuma maimaitawa a hankali.

“Alhamdulillahi! Allah mun gode maka.”

Yadda ta ga tana kokarin tashi, sai ta taimaka mata ta tashi zaune hade da jingina bayanta da filo, yadda za ta ji dadin zaman.

Kadan ta sha ruwan, amma ba ta koma ta kwanta ba, ai tuni Mama ke kiran wayoyin mutane tana fada masu Fatima ta farfado har ma ta yi magana.

Cikin 30mns kofar dakin ya cika da ƴan’uwa, don da kadan-kadan suke shiga har kowa ya shiga ya ganta, duk kuma wanda ya yi mata sannu tana amsawa kawai dai ba ta ganinsu sosai ne. Sai dai ta kan gane wasu da muryoyinsu.

Sai da mutane suka rage sannan Mustapha ya shiga, shi kam yana shiga ta gane shi, shi ya sa ma ta zuba mishi ido har ya karaso, ya ja kujerar da ke saitinta ya zauna.

Suka zubawa juna ido, kafin ya kamo hannunta na dama ya saka cikin nasa, ya rika murzawa a hankali, hawayen da bai san ko na menene ba, suka rika sauka silently.

Kamar 2mns suna a haka, kafin ya bude baki ya ce “AlhamduLilLaH!” kalmar da ya rika maimaitawa kenan, Fatima kuwa ko sau daya ba ta dauke idonta a kansa ba.

“Sannu Fatima, Allah ya ba ki lafiya, Allah ya sa ciwon nan ya zama kaffara”

“Amin” ta amsa a hankali, kafin ta ce “Ina Hana?”

“Ba jimawa Ummi ta dauke ta zuwa gida, saboda tana jin bacci.”

“A ina Ummin take kwana” duk a hankali take maganar alamun dai ta ji jiki.

“Tana gidan Mama.”

Duk suka yi shiru, kafin ya ce “Me ya fi damunki yanzu?”

Ta dan yi jim sannan ta ce “Ba ko ina. Kawai dai jikina ya yi min nauyi.”

“Sannu Allah ya sawake.”

“Amin” ta kuma fada, har zuwa lokacin hannunta na a cikin nashi, tabbas da ace ba ta farfado ba, da gobe babban asibiti zai kai ta, loan ya cika, kuma ya tabbatar zasu ba shi a cikin satin nan. Ganinta kwance kamar gawa shi ne babban tashin hankalin da ya taba shiga a kaf rayuwarshi.

Shigowar Jamil baisa ya saki hannunta ba, ya dai juya yana kallonsa har ya karaso.

Kamshinsa ya cika wajen, wannan karon bakin wandon jeans ne a jikinsa da light blue din riga t-shirt, sumarsa a, kwance, a nutse yake takowa har ya karaso inda suke.

Hannu ya mikawa Mustapha suka gaisa, kamar wanda ke rowar maganar ya ce “Ya mai jikin?”

“AlhamduLilLaH!” Mustapha ya amsa a gajarce.

Shi ma bai kara tankawa ba, illa ya rika bude file dinta da ke kan tebur. Kafin ya juyo sosai zuwa inda take.

Ita dai mamaki ne ya kashe ta, don tabbas wannan Ya Jamil ne, shi ma ta gane shi ne a yanayin dabi’unshi.

” Me ke damunki yanzu?”

“Ba komai.” ta amsa shi a hankali lokacin da take zare hannunta a hankali daga hannun Jamil.

Sai ya juyo sosai hade da tsayawa a kanta.

“Ba komai fa. Ba kya jin wani canji?”

Shiru ta danyi kafin ta ce “Kawai dai jikina ne ke min nauyi, kaina ma haka da kafafuna. Sannan idona ma bana gani mai kyau, bishi-bishi nake gani”

Hannayensa duk biyun ya zuba cikin aljihu yana sauraronta, har ta kai karshe. Ya dan yi jim kafin ya kara cewa “Shi kenan?”

“Sai numfashina, sometimes sai in ji yana rikewa, musamman idan ina magana.”

“Shi kenan?” ya kuma tambaya

Kai ta daga alamar eh.

Ya juya kan file din ya yi rubuce-rubucensa, sannan ya juya ya fita.

Ba jimawa kuma nurses suka shigo dakin da keken tura mara lafiya suka fita da ita.

Dakin gwaje-gwaje suka kaita, hatta likitan ido sai da Jamil ya kira a duhun isha’i ya haska idon, daga karshe dai ya tabbatar mishi da babu matsala sha Allah za ta warware, kawai yanayin da ta shiga ne, rikewar numfashi kuwa ulcer ce. Dama wannan ya san ulcer ce, maganar idon ce ta fi damunshi.

Sai karfe goma na dare aka dawo da ita daki, ya ce a hada mata tea mai kauri ta sha, yana tsaye har ta shanye tea din hade da magungunan da ya ce a ba ta. Sannan ya fita.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 26Daga Karshe 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×