Skip to content
Part 2 of 3 in the Series Dare Daya by Yareema Shaheed

Ko da suka bugama Salim wani sanda nan take ya zube ƙasa warwas, babu ƙarfi a tare dashi, sun sa masa hannu a aljihu sun kwashe duka kuɗin da ke ciki suna shirin ɗaukar wayan ne a ɗayan aljihu sai wasu mutane suka zo gurinsu da gudu suna ihu ɓarayi. Nan suka saki Salim suka ruga ana kare.

Ko da suka duba Salim sukaga basu ji masa rauni ba kaɗai buga masa sanda ne da suka yi akansa wanda har gurin ya ɗan kumbura. Ɗa gasa sama suka yi tare da bashi kayautar ɗari biyu ya je ya siya magani a kemis.

Jan jiki tare da jiri Salim yake ji, haka dai ya dinga tafiya cikin damuwa har ya isa gidansu, wanda ko ba a faɗa ba da ka ga gidan kasan talauci ya yi masu katutu.

Ko da ya shiga cikin gidan samun guri ya yi ya zauna yana hawayen baƙin ciki. Yana tunanin mahaifiyarsa da take kwance a asibiti tana neman taimakon gaggawa. Ya je duk inda yake tunanin zuwa ko zai samu amma shiru kake ji babu wani motsi.

Hannu ya sa a cikin aljihunsa ya ɗauko wayarsa domin kiran abokinsa Muhammad da suka haɗu gurin neman aiki. Kiran ƙin shiga ya yi domin bai da katin kira. Shiru ya yi can tunani ya zo masa sai ya shiga cikin yanar gizo tun da dama ya kan shiga lokaci zuwa lokaci, tun lokacin da suka haɗu da Muhammad suka fara chatin a yanar gizo-gizo. Tunowa ya yi yana da data kyauta da kamfanin sadarwa ke basa lokaci zuwa lokaci. Ako ya ci sa’ a yana shiga ya samu Muhammad akan layi bayan sun gaisa ne, shi ne sai yake faɗamasa mahaifiyarsa tana asibiti nan ya ce in Sha Allah yanzu yana wanka zai zo kuma zai faɗama mamarsa domin tun haɗuwarsu tasan Salim.

Sanin na shirin sauka daga yanar gizo-gizo kenan sai ya ga wani guruf (group) an rubuta idan kana cikin damuwa, kuma kana son ka yi kuɗi ka danna wannan bulun rubutun. Kai da talauci har abada, kuma ba ma amfani da jinin mutane ko abadasu ba. Kai dai in ka shirya fita da ga tauci to ka shigo cikin wannan group ɗin daga yau ka yi bankwana da talauci.

Mikewa tsaye Salim ya yi gumi na keto masa yarasa ya zai yi shin ya shiga ne ko ya hakura har randa Allah zai ya ye masu damuwar da suke ciki shida mahaifiyarsa.

Wata zuciyar ta ce masa ya shiga kawai in ba haka ba mahaifiyarsa za ta iya rasa ƙafafuwanta. Hakan ya sa ya danna bulun rubutun yana dannawa ya shiga ciki tsumdin, sunan sa ya ji ana kira tare da rushewa da dariya da wata iriyar murya mai ban tsaro. Wasu irin halittu ya gani masu ban tsoro da manyan haƙora kaco-kaco da manyan kai jini yana fitowa daga bakinsu. Hakan ya sa Salim ya yi saurin danna left (fita) daga ciki amma ina ko ya fita daga cikin group ɗin sai ya ƙara ganin an dawo dashi ciki. Gabansa ne ya fara bugawa duk ya bi ya shiga cikin ruɗani.
Ji ya yi an fara yi masa magana da wata irin murya mai amsa amo wanda tunda aka haifesa bai taɓa jin kwatankwacinsa ba ko da kuwa a fim ne.

“Ha..ha..ha kai ɗan saurayi idan an shigo cikin wannan gida ba a fita har abada. Hahahaha Muna yi maka barka da zuwa Salim nan ba dadewa ba shugaba za ta shigo domin tarbarka ha!ha!!ha!!!.

Kash masu karatu ku biyo mi domin jin cigaban labarin.

Ayi comments da sharhi mun gode

<< Dare Daya 1Dare Daya 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×