A IDON MAKWARWA
Note
Haka kawai ba tare da wani dalili ba, a wasu lokutan mutum ya kan tsinci kansa cikin zulumi, ya riqa jin tsoro da faduwar gaba hade da taraddadin koma wane irin tashin hankali ne yake kusantoshi. A ire-iren yanayi irin wannan, bawa bai fiye samun kwanciyar hankali ba, har sai abinda ke shirin aukuwa ya afku har ma ya fara wucewa. Kamar dai fadin bature dayake cewa; “AFTER THE STORM COMES CALM “
Five Years Ago
Saturday Morning, Onike Road, Lagos, Nigeria
19/10/2018
08:00 AM
Tsaye take gaban kyamarar da lasifika a hannunta, amma kamar yadda ta kan burge mutanen gari ko abokan aikinta ‘yan jarida da irin nata salon wurin dauko rahoto, gabatarwa ko kuma ya’da labarai yau ta kasa wani kata6us. She looked disturbed.
“One! Two!..
“Action!..
Haka mutumin dake tsaye a bayan doguwar kyamarar sanye da wata sky blue rigar falmaran ta aiki an rubuta kalmar “PRESS” baro-baro a bayanta ya sake fa’da a karo na wurin biyar kenan duk a qoqarin team din nasu wajen ganin sun isar da zazzafan rahoton na hatsari da kuma qonewa qurmus da shahararren mawaqin mai suna PEDRO yayi a wannan safiyar ta asabar.
Sai dai kuma abin mamakin daya ‘daurewa ‘yan team din nasu kai shine, haziqar yarinyar da suke kira Zahra ta kasa nutsuwa ta maida hankali ga kallon kyamarar hade da rattabo bayanai kamar yadda ta saba a koda yaushe idan motar bus ta manema labaran, ta babban gidan rediyo da kampanin jaridar “Devine” din ta debo su ta kuma jibge su a wurin da suke sa rai da ji ko ganin kwakwaf a duk lokacin da buqatar hakan ta taso a ko inane cikin garin legas din.
“Me yake damun Zahra yau?
Tambayar da abokanan aikin nata suke wa kawunansu kenan tun lokacin da ma’aikacinsu wanda yake da alhakin daukar hoton bidiyo ma’ana camera man ya saita qafafun kyamarar tasa zuwa gareta da niyyar haskata amma gaba daya hankalinta da tunanin ta sunyi qaura zuwa wani wajen; ma’ana ba ta tare dasu.
A qwarewa da sanin makamar aiki irin nata, ta riga duka ‘yan tawagar su hada nata bayanan da kuma duk wani abu da take buqata cikin abin da bai fi mintuna goma sha biyar ba da isowarsu wurin. Tun suna kan hanya dama tayi qoqarin bugar cikin google a wayar salular ta a shafin yanar gizo na Lagos Today don tayi briefing kanta.
A ‘dan abin data karanta kuma, hakan yasa da mutane hudu kacal tayi ‘yar gajeriyar tattaunawa a wurin, saboda ta riga ta fahimci makamar zancen;
“Dukkan shedu na ido dake wurin sun taradda motar ne tana cin wuta a gefen titin bayan ta sheqo da mugun gudu sannan ta kwace ta daki wata qatuwar tsohuwar bishiya wanda hakan yasa ta riqa juyin waina ita kadai a gefen titin misalin qarfe biyar da rabi na wayewar garin.“
Tsirarun mutane ne suka shaida hakan kasancewar gari bai gama wayewa ba.
Bayan tayi bitar ra’ayoyinsu ne kuma ta nemi alfarma wurin shugaban tawagar tasu, Oga Isaac wanda yabata guntun break na mintuna biyar saboda shan iska, tayi hakan ne kuma saboda tana son komawa gefe don barin hayaniyar jama’ar wurin sannan kuma ta qagu ta kira asibiti taji yaya situation din qanwarta Aimana yake, wacce ke kwance a asibitin tsawon sati daya. A ranar ake sa ran yi mata dashen qoda (Kidney).
A ‘yar matsawar nan da tayine domin kiran waya, anan ne kuma labarai suka sha ban-ban. Da bata tafi yin kiran wayar nan ba, da kunnuwanta basu jiyo mata sirrin da suka jiyo mata ba, kuma da baza ta ta6a haduwa dashi ba.
“Pull your self together Zahra!..
Babbar muryar Oga Isaac ta sake fizgo ta daga duniyar tunanin data sake afkawa a karo na barkatai.
“Karki yarda abokanan aikinki su gane abinda ke faruwa, idan kikai haka everything will fall into place..
Ta sake tuno wani kashedin daya yi mata a daxun.
Wani gwauron nannauyan numfashi ta sauke daga nan ta shiga zuba bayanai cike da qwarewa cikin zazzaqar muryar ta mai kamar sarewa, karyewar harshenta a turancin da take zubawa tamkar ‘yar Mungo Park.
“Earlier today morning about three hours ago, there was a serious car accident here in Onike Road five kilometers from the mainland. This accident is the type of accident that is called a single car collision.
The driver went out of control as the vehicle somersaulted several times before it caught fire and burnt to the ground when the accident happened.
Shortly after..
Cut!..
Muryar Oga Isaac ta ratso cikin kunnuwan mai daukar hoton bidiyon wanda a take ya yanke iya abinda ya dauka na daga rahoton kai tsaye da Zahran ke gabatarwa.
Oga Isaac yayi hakan ne bayan la’akari da cewa Zahra yarinya ce mai kwazo, ba qaramin al’amari bane zai hana ta tafiyar da aikinta yadda ya kamata ba. Duk da muryar tata na fita ra’dau amma akwai rashin nutsuwa da tsoro a yanayinta. Yana kyautata zaton condition ‘din qanwartane yake bothering dinta.
He’ll have a word with her immediately when they get back to the station.
Yayin da Oga Isaac yake qoqarin canza mai daukowa nasu gidan jaridar rahoton hatsarin ne, wasu gidan jaridun suka cigaba da dauko nasu rahotannin kamar haka;
“Masu bincike na hukumar ‘yan sanda sun tabbatar cewa qonanniyar motar dai mallakin PEDRO ce. Wannan shine babban dalilin dayasa mutane shiga rudu da kuma tunanin anya mutuwar mawaqin bata da nasaba da mutuwar budurwarsa Yvonne Ajayi, matashiyar budurwar da aka yiwa kisan gilla sati biyu da suka wuce?
“Mawaqin dai ya kasance daya daga cikin musical duo watau mawaqa biyu kuma tagwaye masu amsa sunan P- Square; 2nd Wave (sunci sunan ne daga aro suna na asalin daga mawaqan P-Square) kuma wadanda akafi sani da 2nd Wave a gajarce.
“Labarin hatsarin, qonewar hade da mutuwar mawaqin ya gigita dubban masoyansu a fadin qasa ba jihar legas kadai ba. 2nd Wave mawaqa ne masu farin jini kwarai da aniya, kuma wannan mutuwar tazo ne a lokacin da tauraruwarsu take tsananin haskawa a fadin duniya.
******
Bayan kammala daukan rahoton nasu ne, akan hanyarsu ta komawa babban ofishinsu na “Devine Media”, Zahra ta sake zurfafa cikin tunani.
Mintina talatin da suka gabata
07:30 AM
Tsofaffin shaguna ne na haya two storey buildings guda uku jere da juna. Sararin wurin yayi mata yanayi da ‘dan qaramin parking space irin na plaza, ba kowa a gurin sai wani mutum daya dake zaune kan dakalin wani shago riqe da ‘dan qaramin littafi a hannunsa yana nazari.
Daga gefe ka’dan kuma wani dan madaidaicin teburi ne ta gani a gefen wani shagon wanda da gani zaka san irin teburan nan ne da masu kayan masarufi kan kasa kaya akai ne. Sai dai kasancewar lokacin safiya ce, shagunan wurin duka a rufe suke, hakan ya bata damar zama kan teburin, sai dai kuma zaman ta kan teburin ke da wuya tun bata kai ga zaro wayar salularta domin yin kira ba kamar yadda tayi niyya, kunnuwanta suka jiyo mata abin da yafi qarfin tunanin ta, abinda ya girmi yar qaramar duniyarta;
“Asche zu Asche, Staub zu Staub.. Sie können nun mit dem fortfahren, was auch immer Sie planen.
“Ashes to ashes, dust to dust.. You can now proceed with whatever it is you are planning..
“Die Person, durch die wir ihn ersetzt haben, ist nicht mehr. Wir haben ihn im Fahrzeug angezündet.
“The person we replaced him with is no more. We set him ablaze inside the vehicle..
“Es gibt keine Spuren, nicht einmal eine einzige Spur. Das forensische Team wird darin nichts finden können.
“There are no trails not even a single trace. The forensic team won’t be able to find anything inside..
Ita tasan ba haka kawai ta tsinci kanta a aikin jarida ba. There’s a reason for everything.
Ba tare da wani kokwanto ba, a hankali ta miqe daga inda take zaune sadaf-sadaf tai tiptoeing ta dan leqa su, Allah Ya kiyaye ta sun bata baya saboda haka basu ganta ba, sai dai kuma mostin da sukaji ne yasa tayi wuf ta koma kan teburin da take zaune.
Su uku ne suke zaune suma akan wani benchi, sai dai kuma su sun dan shiga cikin wata yar kusurwa ne (corridor) kuma ba magana suke ba a lokacin da taxo wurin shiyasa bata gane akwai wasu a wurin ba bayan wancan mutumin farkon data gani, kuma shima yanzu baya wurin da yake zaune, ba taji motsinsa ba bare kuma tashinsa a wurin. Gaba daya abinda kunnuwanta suka jiyo mata ne ya tafi da hankalinta.
Ji tayi kamar an sauke mata guduma a tsakar kanta lokacin da taji suna qoqarin fitowa, domin ta tabbatar sunji motsinta ne, sa’ar ta daya kafin ta baro set dinsu ta cire ‘yar top falmaran din nan tasu ta ‘yan jarida, kuma idan tayi qoqari ta nutsu tayi composing kanta ba zasu ta6a ganewa taji ta kuma fahimci abinda ‘daya daga cikinsu ya gama fada a wayar salular ba tunda ai da harshen Jamus akayi maganar, kuma duk cikinsu tasan insha Allah babu wanda zaiyi tunanin tana jin yaren jamusancin bare har su tuhumeta, ilai kuwa suna gama fitowa daga qaramar kusuruwar ginin duk suka dube ta duba na tsanaki; yarinya ce zaune kan tebur tana latsa waya a hannunta, so innocently babu alamun rashin gaskiya tattare da ita, haka suka zo duk suka wuceta sukayi tafiyarsu.
Gashi dai lokacin safiya ce, amma kuma akace rashin sani yafi dare duhu. Basu sani ba, amma fa sunyi shuka ne A IDON MAKWARWA!
“Nasan kinji su kuma kin san duk abinda suka fada..
A razane ta ‘dago da kanta ta kalle shi, wannan mutumin ne dai na farko data fara gani yana duba littafi, sai dai kuma yanzu instinct dinta yana bata cewa ba haka kawai ya zauna a wurin ba. It is not a coincidence, bibiyar wadancan mutanen yakeyi shiyasa daxu data juya taga baya wurin, to amma..
“Yanxu ba lokacin tunani bane ‘yanmata..
Husky voice dinsa ta katseta daga nazarin data fara na nemarwa kanta mafita.
“Here’s a deal..
Ya fada yana mai kafeta da idanunsa masu shegen kaifi.
“Zaki maimaita min duk abinda suka fadi, bayan ni kuma zakiyi qoqari ki riqe maganar a matsayin sirri for your own sake.
Haqiqa ni Zahara’u na shiga tsaka mai wuya ta ayyana a ranta.
Tunda take a rayuwa bata ta6a haduwa da mahaluqin dayake mata magana with total authority irinsa ba.
Sannan bata buqatar a fahimtar da ita cewa wannan mutumin dake tsaye a gabanta means everything he just said.. Bata gama farfa’dowa daga kaduwar datayi ba ta sake jin muryarsa
“Here take this..
Ya miqo mata compliment card mai kyau kalar ruwan gwal
“Bar beach, qarfe biyar na yamma. Give me a call for further directions..
Daga haka ya juya yayi tafiyarsa ya barta tana qoqarin rarrabewa, mai yiwuwa ta samu kanta ne cikin ru’da’d’den mafarki mai firgitarwa, sai dai kuma jin kaifin wani abu a tafin hannunta wanda ba komai bane face wannan compliment card din daya bata kasancewarsa na qarfe hakan ya tabbatar mata cewa ba mafarki take ba, a farke take tun qarfe hudun asuba lokacin da kiran wayar Oga Isaac ya tashe ta a barci daga sannan kuma bata sake runtsawaba.
Sai yanxu premonitions din data riqa ji tun yammacin jiya zuwa wayewar garin yau yake bayyana ma’anarsa a gareta.
“Bar beach, qarfe biyar na yamma. Give me a call for further directions..
Maganarsa ta qarshe ta cigaba da ansa kuwwa a kunnuwanta. Allah Ya sani she dreads zuwan qarfe biyar na yammacin yau, dole tayi sauri taje taga Aimana kafin lokacin.
I’m very interested
Am grateful. Thank you.
Very good
Thank you. Name sake
Allah Ya karo basira
Ameen yar uwa
Gaskiya you re doing a good job here.
Godiya sosai
Da kyau