Umma ta ɗan musƙuta ta ce,
"Gaskiya ya yi yarinta."
Daga baya Sadiq ya fashe da dariya soaai, sannan ya ɗora da cewa,
"Ni Wallahi na yi zaton Aljanah ce. Gaskiya na yi nishaɗi yau sosai. Dama abin da nake hasashe kenan shiyasa na yi ta zumuɗi."
Zahra'u ta kwantar da kanta jikin Umma kamar za ta yi kuka, ta ce
"Ummana ni ƙilama sai na yi mafarki."
Iffaan dai bai ce komai ba, gaba ɗaya nazarin Ihsan ya sanya shi a dogon tunani duk da yana yaronsa.
Shi kuwa Irfaan ji yake surutansu yana matu. . .