A natse ya miƙe yana faɗin yana zuwa. Tunda ya fita bai sake dawowa gidan ba, sai cikin dare. Abin mamaki da al'ajabi, kayan kallon falon a kunne suke, hakan yasa ya fara tunanin ko Zahra ce da Iffaan basu yi barci ba. Sai dai yana shiga ya yi turus, daga irin burin da ya ci akan yi masu faɗa akan abin da ya hanasu yi yau suka karya dokarsa.
Ihsan ce a zaune a ƙasa ta kafe tv da idanu babu ko ƙyaftawa. Kallo ɗaya zaka yi mata ka fahimci tana cikin damuwa. Har zai. . .
Gaskiya yayi