Duk da Irfaan baya son barin mahaifinsa, amma tafiyar nan tafi komai faranta ransa. Nan da nan ya hau shirye-shirye. Cikin abin da bai wuce sati biyu ba, jirginsu ya daga sai London.
Bayan tafiyar Irfaan ne ciwon da Abba yake ta dannewa ya taso masa gadan-gadan. Hankalin Umma a tashe a lokacin da Abba yake magana da kyar,
“Kiyi hakuri. Ina fama da ciwon koda. Likitana ya gaya min idan ba ayi min dashen koda ba komai yana iya faruwa. A dalilin hakanne na tura su Sadiq karatu a waje domin bana so hankulansu ya tashi har. . .