Yau ma kamar kullum ya shirya tsaf ya koma asibitin domin yana nan akan bakansa sai ya gano wanda yaba mahaifinsa koda.
Da gaske yake yi zai raba dukiyarsa biyu ya bashi rabi, zai kuma tambaye shi duk wani abu da yake so daga gareshi ya yi alkawarin bashi ko menene, duk mahimmancinsa.
Daga bakin kofar yake jiyo dukkan tattaunawansu, akan likitan yana cewa shi lallai zai gayawa Irfaan ko waye. Ayayin da shi kuma yake rokonsa ba yanzu ba, sai lokacin yin hakan ya yi.
“Wani lokaci ne wannan kake jira? Sai yaushe? Ko jira kake yi sai lokacin. . .