Skip to content
Part 9 of 25 in the Series Duniyata by Fatima Dan Borno

Yau ma kamar kullum ya shirya tsaf ya koma asibitin domin yana nan akan bakansa sai ya gano wanda yaba mahaifinsa koda.

Da gaske yake yi zai raba dukiyarsa biyu ya bashi rabi, zai kuma tambaye shi duk wani abu da yake so daga gareshi ya yi alkawarin bashi ko menene, duk mahimmancinsa.

Daga bakin kofar yake jiyo dukkan tattaunawansu, akan likitan yana cewa shi lallai zai gayawa Irfaan ko waye. Ayayin da shi kuma yake rokonsa ba yanzu ba, sai lokacin yin hakan ya yi.

“Wani lokaci ne wannan kake jira? Sai yaushe? Ko jira kake yi sai lokacin da bani da ikon yin komai karfina ya kare sannan zaka bari insani?”

Irfaan ya yi kalaman nan bayan ya bude kofar ya shigo. Gaba daya sun nuna razanarsu a fili.

Ba haka kawai Allah ya dora masa son yaron ba, a ganinsa na farko ya ji a jikinsa akwai wani abu mai karfi da zai sake hadasu, sai dai bai taba tunanin irin wannan abun bane. Irfaan ya jawo shi ya rungume. Ya rasa abin da zai yi ya ji sanyi da ya wuce ya rungume shi din. Idanunsa sun kada sunyi jazir. Yana son yaron, zai ci gaba da sonsa har ya koma ga Mahaliccinsa.

Sulaiman ya kasa rike dauriyansa don haka ya fara shesshekan kuka.

Har cikin tsakiyan kirjinsa yake jin kukansa. Da ace Sulaiman zai bude kirjin Irfaan ya gani, da ya tausaya masa ya daina kukan da yake yi.

“Sulaiman… Ban isa inbiyaka ba, kayi min komai. Ka gaya min abin da kake so in yi maka ni kuma na yi maka alkawarin yi. Sannan tun kafin insan kaine na yi alkawarin raba dukiyata gida biyu domin inmallakawa wanda ya taimakeni ya ceto rayuwan wanda shi ne nawa rayuwar.

“Idan ma kana son dukiyata dukka zan baka Sulaiman.”

Sai yanzu Sulaiman ya zame kansa daga jikin Irfaan yana jin ciwon da zuciyarsa take yi masa tana raguwa. Jikin bangon ya jingine yana sauke numfashi. Shi dai Dakta Salis sai kallonsu yake yi yana jinjina halin Sulaiman.

“Yaya ba zaka iya yi min abin  da nake so ba.”

Irfaan ya dube shi sosai, bai kawo komai aransa ba, ya dawo kusa da Sulaiman,

“Dokto Salis ka zama shaida, ko menene Sulaiman kanina yake bukata zan yi masa na yi wannan alkawarin, duk wahalarsa.”

Sulaiman yana jin wani kwarin guiwa tare da natsuwa suna ziyartarsa. Sai da ya dubi Dokto Salis yaga ya daga masa kai alamun karfin guiwa, sannan ya sunkuyar da kansa ya ce,

“Na saki matata Ihsaan har saki uku. Ina so ka taimakeni ka auri Ihsaan. Zaka zauna da ita har sai ni da kaina nace maka ina bukatarta. Ihsaan ta rasa farin ciki ta rasa wanda zai kare mata idan ana dukanta. Na gaza samar mata da farin ciki. A wurinka ne kawai nake hasashen cikar burina. Zaka iya ba Ihsaan dukkan abubuwan da nake nema ta samu. Nasan Ihsaan bata da kyau, kuma ‘yar kauye sannan yarinya ‘yar karama.

“Wannan alfarma idan ka yi min ita ina tabbatar maka sai nafi mai kudi farin ciki. Ban bayar da kodana domin ka saka min ba, bana bukatan ko sisi daga gareka. Ina dai da tabbacin zaka iya taimakona nima. Abba kuma a matsayin mahaifi yake a wurina, har rayuwata gaba daya zan iya bashi.”

Sai yanzu Sulaiman ya dago ya dubi Irfaan. Ga mamakinsa sai yaga yana hada gumi. Gaba daya bayansa ya jike sharkaf da zufa. Hakan yasa jikinsa yin sanyi, ya sani ba karamin yaki ya tarowa kansa ba, sai dai kuma tuni ya shiryawa wannan yakin. Yana nan akan bakansa babu wanda yake so ya auri Ihsaan sai Irfaan, shi kadai ne yake da tabbacin zai iya mayar da Ihsaan dinsa wata abar alfahari anan gaba. Dokto Salis ya yi tagumi, domin kuwa yasan Ihsaan din da ake yiwa mai ji da kai Kaman Irfaan ta yi. Ko mai gadin gidansu yana da tabbacin ba zai yarda ya karbi Ihsaan ba, bare kuma Irfaan…

Irfaan ya sharce guminsa yana kakalo murmushi. Tabbas da yasan abin da zai faru kenan, da bai tsananta bincike akan wanda yaba Abba Koda ba.

“Sulaiman dan wannan ba komai bane. Na amince zan auri Ihsaan.”

Irfaan ya bada amsar nan ba tare da ya shirya fitowan kalaman ba. Ya dade yana yaki da zuciyarsa sannan ta bashi hadin kai ya furta su babu shiri.

Sulaiman ya gigita.Farin ciki yasa ya zube kasa yana godewa Irfaan Kaman wanda aka biya masa aikin Hajj. Mamaki ya kara kama Irfaan. Ya dan bubbugi kafadansa.

“Ka wuce komai a wurina. Zan wuce Office akwai abin da zanje in yi.”

Sulaiman ya fahimci Irfaaan baya cikin hayyacinsa, don haka bai matsa masa ba, suka rabu. 

Sulaiman ya nufi gidansu Irfaan domin samun mahaifinsa. Bayan sun gaisa ne ya yi masa iso wurin Abba.

Kansa a kasa Abba yake yi masa fada mai kama da nasiha. Ya dora da cewa,

“Sulaiman kana da hankali kana da wayo kana da tausayi me ya sa za ka yi haka? Zan yi wa wani alkali magana saboda lamarin sakin da kayi akwai bukatan a dubi abin ta fuskar addini. Tunda sau daya ka furta saki ukun akwai yiwuwar saki daya ne. Alkali zai duba dalilan sakin zai koma saki daya tunda kayi ne a cikin fushi. Duk da lokacin mulkin Sayyidina Umar ya maido saki uku a matsayin saki ukun nan ba saki daya ba, kamar yadda a zamanin Annabi (S. A. W.) da zamanin Sayyidina Abubakar suka ce saki uku a kalma daya saki daya ne ba uku ba. Da yake abin na malamai ne kuma hurumi ne na alkali sai muje. Insha Allahu matarka zata dawo gareka a matsayin saki daya ne ya taba shiga tsakaninku ba uku ba. “

Nan da nan fuskar Sulaiman ta sauya. Ya dago ya dubi Babansa, shima din shi yake kallo fuskarsa tana nuna farin ciki muddin auren Sulaiman da Ihsaan ya dawo.

” Abba a gafarceni. Idan saki uku a kalma daya yana nufin saki daya to ni Sulaiman… “

Sai kuma yaji nauyin abin da yake son furtawa don haka ya sunkuyar da kansa.

Abba da Baba Sani suka kafe shi da idanu. Abba ya ce,

“Ina saurarenka Sulaiman.”

Muryarsa tana rawa yace,

“Ni Sulaiman na saki matata Ihsaan saki daya, na saki matata Ihsaan saki biyu, na saki matata Ihsaan saki uku. Abba ku gafarceni.”

Ya dago hawaye suna bin fuskarsa. Shi kadai yasan asalin dalilinsa na yin hakan. Ko kadan dalilan da ya gayawa Irfaan basu daga cikin dalilan da yasa ya saki Ihsaan har yake so Irfaan ya aureta. Daga shi sai zuciyarsa suka san dalilansa.

Gaba daya jikin Abba ya yi sanyi. Baba Sani ya tashi zai duke shi Abba ya yi saurin dakatar da shi,

“Kada ka hukunta shi da abin da bakasan dalilinsa ba.”

Dole Baba Sani yabi umarnin ubangidansa zuciyarsa kamar zata fashe. Gani yake wannan babban rashin kunya ce Sulaiman ya yi. Haka suka rabu Sulaiman ya koma gida zuciyarsa babu dadi kamar ta faso waje.

Shi kuwa Irfaan da kyar ya isa Office ya yi wasu rubuce-rubuce ya mikawa Admin sannan yasa kai ya fice yana ji kamar zai fadi kasa saboda jiri da ke kwasarsa.

Kai tsaye gida ya nufa, ya kulle kansa a daki yana jin tabbas idan ya auri Ihsaan zai iya mutuwa. Ya zai yi da iyayensa? Ya zai yi da abokansa da mutanan gari da suka kosa suga irin matar da zai aura? Hankalinsa ya kara tashi da ya tuna da kamannin Ihsaan.

Tirkashi! Ya tashi zaune daga kwanciyar rigingine da ya yi ya sake mikewa tsaye kamar wanda aka tsikara,

“No ba zai yiwu ba. Tayaya? Ta ina zan fara wannan abu? Ba zan auri wacce zata yi sanadin mutuwata ba. Hakoran Ihsaan kadai idan ya kwana biyu yana yawan kallo sai ya kusan zama zararre, yadda suka dafe suka zama wasu kala. Banda gefen bakinta da wani farin abu ke taruwa saboda kazanta. Bare har ya ce zai zauna da ita zaman da bai san lokacin da Sulaiman zai zo ya karbeta ba.

‘Kuma sai ka dora mata idda dole kafin Sulaiman ya iya karbarta.’

Wata zuciya ta hankado masa wannan maganar, wacce ta sanya shi murmushi sosai. Murmushin da ya yi ta nema a lokacin da Umma take yi masa magana ya rasa.

Komawa ya yi ya zauna dabas! “Ba zai taba yiwuwa ba, bana jin akwai wanda ya isa ya sanyani in aikata hakan ko da kuwa na sha kayan mayen duniyar nan ne.”

Ya furta a zahiri yana jin ciwo a zuciyarsa.

Dole sai su Umma sun san zancen nan, duk daren dadewa dole za su sani.

A lokaci guda tunaninsa ya tsaya akan ya koma London ya karasa abubuwan da za su fissheshi. Har ya fara harhada kaya kalaman Sulaiman suka dinga dawo masa tsakiyar kai. Cilli ya yi da wata riga da ya dauko ya mike kawai ya nufi falo.

Abba da Umma suna zaune suna kallo cike da natsuwa. Duk wanda ya kallesu zai fahimci babu wata matsala da ke damunsu. Farin cikin yadda yaga iyayensa ya tsirga masa. Ba kowa bane sila face Sulaiman, tabbas Sulaiman ya taka mahimmiyar rawa a cikin rayuwarsu. Ya dawowa da mahaifiyarsa farin cikin da ta rasa a watannin baya.

Duk suka daga kai suna dubansa.

“Lafiya lau kake kuwa Irfaan?”

A daidai saitinsu ya zauna a kasa yana fuskantarsu. Hakan yasa duk suka sake mayar da hankulansu kansa.

“Abba kasan waye ya baka koda?”

Da sauri duk suka amsa da “A’a”

Irfaan ya sake yin shiru daga bisani ya ce, “Abba ba kowa bane ya baka Koda face Sulaiman dan wajen Baba Sani mai gadi.”

Duk suka razana, suka ware idanu sosai suna duban Irfaan. A natse Irfaan ya gaya masu yadda akayi yasan Sulaiman ne. Sai kuma ya yi shiru idanunsa suka canza zuwa jaa. Abba ya numfasa ya ce,

“Allah sarki bawan Allah. Shiyasa yake da kyau kayi mu’amala na kwarai da mutane, domin kuwa bakasan wanda zai iya taimaka maka anan gaba ba. Wannan yaro Allah ya saka masa ya yi min abin da ‘ya’yana ne kadai za su iya yi min.”

Abba ya dauke kwallan da ya zo masa gefen idanu. Tun bayan da ya sami lafiya kullum sai ya yi wa wanda ya bashi koda addu’a da kuma fatan Allah ya hada su wataran shima ya rama kyautatawan da ya yi masa. Duk da yasan ko me zai bashi ba zai iya biyansa ba. Umma ta jinjina kai tana cewa,

“Ikon Allah kenan. Yaron nan tun ganin farkona da shi ya shiga raina matuka. Allah ya saka masa da alkhairi.”

Jin Irfaan ya yi shiru yasa duk suka sake dubansa. Sosai fuskarsa ta nuna damuwa don haka Abba ya tattaro dukkan natsuwarsa ya maida kansa.

“Akwai wata matsala ce? Me ya sa na ganka ahaka? Ko baka yi farin ciki da ya taimakemu bane?”

Irfaan ya yi saurin girgiza kai,

“A’a Abba. Bana jin akwai wanda ya kaini farin ciki. Damuwa da sanin waye din shi ya sa na kasa natsuwa inmayar da hankalina kan aikina. Ina sonka Abba fiye da yadda nake son kaina. Da aka gaya min ciwonka saboda gigicewa har sabo naso inyi. Bayan anyi maka aiki naci alwashin nemo wanda ya yi min wannan taimakon tare da damka masa rabin dukiyata ko kuma dukiyar tawa gaba daya. Sai gashi na samo wanda nake nema. sai dai da na yi masa tayin dukiyata sai ya ce min baya bukata, ya gaya min shi farin cikina kawai yake so ya dauke ya yi gaba da shi. Sulaiman baya bukatan ganin ina farin ciki ina dariya. Abin da ya rokeni inbashi kenan.“

Ya sauke maganar cikin matsananciyar damuwa.

Abba da Umma suka kalli juna. Ko alama basu fahimci inda zancensa ya dosa ba, amma kuma sai Abba ya daure ya ce,

“Idan har kana ganin lafiyata tafi farin cikinka, me zai hana ka dauka ka bashi? Zaka kasa bashi farin cikin nan ne a lokacin da ka fahimci farin cikinka yafi lafiyata.”

Mahaifinsa ya fi shi gaskiya, ya kuma bashi wani irin kwarin guiwa da ya rasata tun bayan da Sulaiman ya mika masa kokon baransa.

Sannu a hankali ya labarta masu yadda ya yi da Sulaiman. Gaba daya sai dakin ya dauki shiru.  Umma ta yi matukar firgita da zancen. Za ta so ace mafarki take yi ba ido biyu ba. Tayaya danta da ta ci burin bikinsa ace wai Ihsaan ce matar da zai aura? Kai wannan ba me yiwuwa bane.”

Abba ya dauke shirun da kalamansa, “Ina ganin wannan ba wani abu bane Irfaan. Na gaya maku yaron nan akwai wani abu aransa. Yana son rayuwar Ihsaan ya inganta ne shiyasa yake son siyar da rayuwarsa akanta. Ya hango adalcinka shiyasa yake so ya kaita ma’ajiya mai kyau.”

Umma ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Idan haka yake nufi me zai hana ya karbi dukiyar yaje ya inganta rayuwarta din? Ko kuma ya kawo mana ita nan ni nayi alkawarin riketa kamar Zahra. Amma maganar aure ba karamar magana ba ce. Kila dan suna ‘yan kauye shiyasa basu san girmansa ba. Akwai bukatar ayi nazari akan zancen nan hankalina bai kwanta ba.”

Abba ya yi murmushi ya ce, “Anan gaba kadan zaku gane manufar yaron nan. Shi jahilci ba a kauye kawai yake ba, yana ko ina. Don haka dan kauye yasan mahimmancin aure tunda duk littafi iri guda muke karantawa. Irfaan ka koma ka kammala ayyukanka a London ka dawo indaura maku aure kai da Ihsaan. Kada ka dubi kyan mutum wajen gwada masa kiyayya, ka fara duban yadda zuciya take, domin kyawunta ita tafi tasiri fiye da kyawun fuska. Idan ka aureta kana da daman da zaka iya karo uku. Amma bana son zalunci. Idan kasan zaka zalunci amanar da Sulaiman ya baka kada ka amshi abin da ba zaka iya ba.”

Irfaan ya jijjiga kai, “Duk yadda kace haka za ayi Abba.”

Abba ya yi murmushi ya dubi matarsa ya ce, “To me kika ce?”

Muje zuwa dai… ‘Yar mutan Bornonku ce.

Me zaku ce akan wannan shafin?

Fatinku ce.

<< Duniyata 8Duniyata 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×