Skip to content

Duniyata | Babi Na Biyu

3.3
(6)

<< Previous

Umma ta ɗan musƙuta ta ce,

“Gaskiya ya yi yarinta.”

Daga baya Sadiq ya fashe da dariya soaai, sannan ya ɗora da cewa,

“Ni Wallahi na yi zaton Aljanah ce. Gaskiya na yi nishaɗi yau sosai. Dama abin da nake hasashe kenan shiyasa na yi ta zumuɗi.”

Zahra’u ta kwantar da kanta jikin Umma kamar za ta yi kuka, ta ce

“Ummana ni ƙilama sai na yi mafarki.”

Iffaan dai bai ce komai ba, gaba ɗaya nazarin Ihsan ya sanya shi a dogon tunani duk da yana yaronsa.

Shi kuwa Irfaan ji yake surutansu yana matuƙar damunsa. Zai so ya taka masu burki ko zai sami daman gano abubuwa da yawa da ke kwance a bisa fuskar Sulaiman.

Sai dai kuma babu daman dakatar da su, saboda bai cika son takura masu ba, musamman a gaban Abba yanzu zai fara zancen idan ya mutu ba zai jawo ƙannansa jiki ba kenan. Shi kuwa idan akwai abin da ke ɗaga masa hankali bai wuce Abba ya yi zancen mutuwa ba, duk da yasan dole ce.

Har suka iso gida hirar Ihsan suke yi. Suna fitowa duk suka yiwa kansu mazauni a falo kowannansu ɗauke da gajiya. Umma ta fara duban mijinta ta ce masa,

“Sannu da hanya.”

Ya amsa da,

“Yauwa.”

Daga nan Irfaan ya dubi Abba da ƙyar ya yi masa Sannu da hanya, sannan ya yi wa Umma. Daga nan ƙannansa suka yi masa sannan suka yi wa junansu. Wannan kaɗan kenan daga cikin irin tarbiyyan gidan Alhaji Abbas. Gida ne na ‘yan boko, amma kuma yana ɗauke da koyarwa irin ta Islama.

Irfaan ya miƙe ya nufi ɗakinsa. A hankali duk suka watse domin yin wanka su kintsa sannan su dawo su ci abinci.

Tunda ya shiga ɗakinsa ya faɗa dogon tunani. Ya rasa dalilin da yasa Ihsan ta yi masa tsaye akai. Yana so ya ji dalilin da duk duniya Sulaiman ya rasa matar aure sai Ihsan. Bayan a ƙauyen yaga wasu ‘yan matan waɗanda suke da kyansu babu laifi.

Har dare Irfaan baida walwala. Babu kuma wanda ya kula da hakan, kasancewar ya saba shiga irin wannan yanayin.

Yau daga shi har mahaifinsa basu je Office ba, kasancewar Abba shi ne Oga kuma tafiya ta kama masu, sai suka ɗauki hutun yau kawai.

Cikin dare yana barci ya yi mummunan mafarki da Ihsan kasancewar ya sanyata aransa sosai. Shi dai gani ya yi Abba da Umma tsaye akansa suna tofa masa addu’a. Bai gama tunanin abin da ya faru ba, sai ji ya yi Umma tana cewa,

“Yallaɓai dole gobe mu kira malaman nan su zo, tunda abun ya kai matsayin da har Irfaan zai dinga ihu.”

Irfaan ya girgiza kai cike da takaici ya ce,

“Haba Umma.. Babu abin da ya sameni mafarki na yi shiyasa, kuma barci ne ya kwasheni banyi addu’a ba.”

Duk dai suka yi shiru alamun basu yarda ba. Abba ya dube shi suka haɗa idanu, ya nuna masa hanyar banɗaki. Babu musu ya miƙe. Su kuma suka zauna shiru suna jiran fitowarsa.

Da alwala ya fito wannan karon fuskarsa a sake. Yana ayyanawa aransa lallai ya zama dole ya samawa kansa lafiya akan abin da babu ruwansa, idan ba haka ba kuwa sai ya zama ƙaramin mahaukaci. Sannan zai jawowa kansa iyayensa su sake yarda da gaske ne yana da Aljanun da suka hana shi aure.

Ganin yana shimfiɗa darduma yasa duk suka miƙe tare da yi masa sai da safe.

Umma da Abba basu yi barci ba, sun jima suna tattauna lamarin Irfaan. Shi kuwa bayan ya idar da Sallah ya koma gado tare da jero addu’o’i hatta Sulaiman sai da ya tsinci kansa da yi masu addu’a.

***** *****

Kamar wasa Irfaan ya fuskanci aikinsa ba tare da ya sake tuna wata halitta wai Ihsan ba, bare Sulaiman. Baba Sani kuwa ya dawo ya ci gaba da aikin gadinsa.

***** *****

Uniform ne a jikinsa mai ruwan roɗi-roɗi, ya yi matuƙar ɗaukarsa. Yana sanye da takalmin boot, sai sheƙi yake yi. Bayan ya aza hular ne ya fito yana taku a tsanake kuma cikin izza! Idan yasa kakin nan ji yake duk wani lokaci na wasa ya kau. Hannayensa dukka ya zuba a aljihu ya dakata da tafiyar da yake yi, ya zubawa su Abba da Umma idanu. Shima Abban yana sanye da kakinsa na ‘yan sanda. A saman kafaɗunsa rank ɗinsa ne na wurin aiki mai ɗauke da taurari guda uku, wato (3 star) sai dai kuma na Irfaan ɗaya ne jal!

Irfaan ya yi nisa cikin kallon iyayen nasa, waɗanda a kullum suke sake komawa saurayi da budurwa. Suna matuƙar burge shi, zai so ya yi rayuwa da iyalinsa kwatankwacin na iyayensa.

Ganin da gaske basu ganshi ba, yasa ya yi gyaran murya yana sake gyara wuyan riga alamun bai gansu ba. Sai a lokacin duk suka waiwayo suka dube shi. Dukkansu suka saki murmushi.

Abba ya ƙaraso ya riƙo kafaɗunsa yana jijjigawa. Yana murmushi ya ƙaraso wurin Umma ya kama hannunta ya ɗora a bisa kansa,

“Kiyi mana addu’a ni da Ogana, anjima muna da fita. Addu’ar nasara kawai muke buƙata.”

Umma ta jero masa addu’o’i kamar yadda ta saba sannan ta rakosu har wurin mota. Irfaan ya buɗewa mahaifinsa baya, bayan ya shiga ne ya sara masa sannan ya rufe shi ya koma mazaunin Driver.

Umma tana ɗaga masu hannu har suka fice. A hanya Abba da Irfaan suka yi ta tattaunawa akan kasuwancinsu, Abba ya sake tabbatar masa yana gab da ajiye aikin ɗan sanda ya koma kula da kamfaninsa, domin kwana biyu baya gane komai.

Cikin ladabi Irfaan yake yi masa magana, babu wanda zai gansu ya fahimci uba da ɗa ne.

Irfaan yana cikin Office ɗinsa ya gaji matuƙa saboda ayyuka da ya tarawa kansa. Office ɗin mahaifinsa yake son zuwa saboda ya kai masa wasu files yasa hannu, amma kamar anyi masa duka.

Ƙwanƙwasa ƙofarsa da akayi yasa ya bada izinin shigowa ba tare da ya ɗago ba.

Ƙamshin da ya daki hancinsa yasa shi ɗaga kai yana ƙarewa wacce ta shigo kallo ba tare da ya shirya ba.

Ko makaho ya laluba sai yasan cewa tana da kyau. Sai dai shi ko alama bata burge shi ba.

“Bani da appointment ɗin ganin wasu baƙi a daidai wannan lokacin waye ya baki izinin ganina ba tare da ansanar min ba?”

Ya yi maganar yana sake duban irin shigar da ta yi kamar ba musulma ba.

“Au sai ka bani izinin zama ko?”

Ta yi maganar cikin siririyar murya. Da sauri ya sake dubanta, yana nazarin muryarta mai kama da ta Ihsan. Sai yanzu ta sake faɗo masa a rai. Da sauri ya ja A’uzubillahi ya nemo natsuwa ya ɗorawa kansa.

“Idan baki da abin cewa daga tsaye zaki iya fita don Allah. Akwai ayyuka da yawa a gabana.”

“Uhum! Sunana Sadiya Bashir. Ina tare da mahaifina yana cikin Office ɗin Abbanka. Anturo ni ne muyi zumunci, idan da rabo kuma a ƙulla alkhairi.”

Bai yi mamakin ganin mara kamun kan nan a matsayin ‘yar Alhaji Bashir ba, domin yasan waye shi. Sai dai Mahaifinsa yafi bashi mamaki. Kullum nasiharsa Irfaan ya auro mai addini. Me zai sa ya turo masa Sadiya?

“Kina ji ko? Ban iya Zumunci da ‘ya mace ba. Kuma kin cika kyau, ni kuma a tsarina ba zan taɓa auren mai kyau ba.”

Sadiya ta rausayar da kai ta yi fari da ido,

“Me ya sa ba zaka auri mai kyau ba? Ko don kai mai kyau ne?”

Bai ce uffan ba, ya mayar da kansa akan abin da yake yi cikin ɗaure fuska. Daga ƙarshe ya miƙe ya kama hanyar Office ɗin mahaifinsa yana jin tarin damuwa a zuciyarsa wanda ya rasa dalilin irin wannan ƙunci da yake yi.

Sai da ya sara masa sannan ya miƙa masa files ya yi masa bayani. Abba yana kula da yanayin ɗansa, sai dai kuma yanzu ba lokacin kulawa ba ce, ba kuma lokacin tattauna matsalar gida bane, don haka shima ya ci gaba da tsare gida.

Har ya juya zai fita, Abba ya kirawo shi, ya juyo ya sara masa ya ce

“Sir!”

Abba ya yi iya bakin ƙoƙarinsa domin ganin sun haɗa idanu abin ya gagara.

“Irfaan kun gaisa da Alhaji Bashir kuwa?”

Kafin ya yi magana, Sadiya ta shigo babu Sallama ta murɗa ƙofar ta turo kai. Irfaan ya daka mata tsawa,

“Ke! Ki koma sai kinyi Sallama anbaki izinin shiga tukuna.”

Ta haɗa rai tana feleƙe. Zata ƙaraso Irfaan ya daka mata razananniysr tsawan da tasanyata kama hanyar fita babu shiri. Abba bai ce komai ba, domin ya kula yau Irfaan ɗin nasa ya sauya da yawa. Dole akwai abin da ke damunsa, amma zai yi haƙuri har su koma gida. Sadiya tana fita ta yi waje da gudu tana kuka. Ba a taɓa ci mata mutunci ba, kamar yau, ta ɗau alwashin sai ta mayar da Irfaan abin tausayi. Shi kuwa Alhaji Bashir idan ransa yayi dubu to ya ɓaci.

***** *****

A can ƙauyen Saulawa kuwa, bayan taro ya watse aka kawo Ihsan gidan mijinta. Gidan Baba Sani anan za su zauna, don haka aka bata ɗaki ɗaya, zata zauna da mahaifiyar Sulaiman wato Innayo.

Bayan anwatse aka bar amarya da ango suna zaune jigum-jigum. Da ‘yar katifarsu a ƙasa, itama Sulaiman ne ya samu ya siya da ƙyar. Ta dube shi ta cikin hasken fitila ta yi rau-rau da ido zata yi kuka.

Yasa hannu ya yafito ta. Babu musu ta rarrafa ta ƙara so. A duniya bata jin bayan mahaifinta akwai wanda take so sama da Sulaiman.

“Yaya Sulaiman. Ta kira sunansa cikin matsananciyar kuka.”

Ƙwalla suka sauka a fuskarsa yasa hannu ya ɗauke.

“Ki yi haƙuri. Daga yau kukanki ya ƙare. Ba zan sake bari kiyi kuka ba.”

Yana maganar yana buga bayanta har ta yi shiru sai ajiyar zuciya da take yi babu ƙaƙautawa.

Anan barci ya kwashesu gaba ɗaya, ko awaran basu sami daman ci ba.

Kasancewar Baba Sani yana nan, hakan yasa Innayo ɗaga masu ƙafafu. A duniya ji take kamar ta kashe Ihsan saboda tsabar tsana. Dariya kawai take yiwa jama’a gudun a tafi da ita a bakin duniya.

Washegari. Ya kamo hannunta suka shiga wurin Innayo domin su gaidasu. Innayo da ta fito hannunta ɗauke da kofin koko zata kaiwa Baba Sani ta dube su ido buɗe,

“Me zan gani haka Sulaimanu? Dilla sakar mata hannu tun kafin ranka ya ɓaci. Ni zaka yi ta jawowa abin magana?”

Sulaiman mai yawan fara’a, da wahala aga fuskarsa a ɗaure koda kuwa anɓata masa rai ne.

“Menene a ciki dan na riƙe hannun Ihsan? Innayo ba yau na fara riƙe hannun Ihsan ba. Kin tashi lafiya? Ina Baba ya shiga ne?”

Innayo ta watsa masa harara taja tsaki tare da wucewa abinta. Ihsan ta saki baki tana kallonta, gabanta yana tsananta faɗiwa. Tana ƙoƙarin ƙwace hannunta ya dubeta yana murmushi,

“Kada insake riƙeki kiyi ƙoƙarin ƙwacewa kinji? Idan ba haka ba raina zai ɓaci.”

Sai da ta shanye kukanta sannan ta gyaɗa kai.

A daddafe suka yi kwanaki biyu, a lokacin kuma Baba Sani ya dawo bakin aikinsa. Suna barci da asubahin fari, suka ji bugun ƙofa kamar za a karya ƙofar. Sulaiman ya tashi ya buɗe cikin magagi. Itama Ihsan ta biyo bayansa a tsorace. Innayo ta dube su duba na takaici ta ce,

“Sannunku masu idanun barci. Don Allah ke fito mu kama aiki.”

Kafin Sulaiman ya yi magana ta ratse shi ta fice jikinta yana kyarma. Shi kuwa ya tsaya yana kallon ikon Allah. Ji yake zuciyarsa tana tafarfasa, amma ya yi alƙawarin ba zai ce komai ba, zai dai tsaya yaga iya gudun ruwan mahaifiyarsa.

Uban wanke-wanke ta nuna mata. Babu musu ta ɗauki bokiti ta yi bakin rijiya. Ta ɗibi ruwa kafin ta durƙusa ta kama wanke-wanke. Ɗaki ya koma ya canza kaya ya fito yana dubanta.

“Tashi kije kiyi Sallah.”

Babu musu ta tashi, shi kuma ya wuce Masallaci. Ko da ya dawo ya sameta ta gama wanke-wanken ta ɗora ruwan kunu. Ga iccen baya ci, sai hurawa take yi idanun sunyi jaa. Ya ce ta matsa ya hura wutan, ya dawo ya kama mata ayyukan. Hatta shara ya hanata yi. Innayo tana ciki batasan abin da ke faruwa ba, sai da ƙanin Sulaiman ya leƙo ya gani sannan ya sanar da Innayo.

Aikuwa ta fito tana ta ruwan bala’i bai ce mata komai ba. Sai can ya yi murmushi ya ce,

“Wai Innayo ko dai kin tsaneni ne? Nifa ɗanki ne, dan nayi aiki a gidan ubana wani abu ne? Murna ya kamata kiyi.”

Ta dube shi sheƙeƙe ta ce,

“Kaji min yaro. Me zai kai ka yin aikin mata? Tunda ba kai nasa ba sai ka kauce ka bani wuri.”

Sosai ya dubeta ya ce,

“Ihsan yarinya ce da ba zata iya yin aiki irin wannan ba. Don haka ni zan dinga tayata.”

“Ahh ikon Allah. Da can a gidansu da take yin komai na gidan kuma fa? Kai kake zuwa kana tayata?”

Ya dubeta sosai ya ce,

“Wallahi ki tambayeta kiji. Ni nake zuwa ina tayata. Anan ma ni zan tayata.”

Ya juya kawai abinsa. Da yake tasan halin Sulaiman ba a kayar da shi a magana. Cikin ruwan sanyi zai maido da martani mai zafi. Dole ta ɗaga masu ƙafa ta koma ciki.

A ɗakin ya buɗe kanta yaga duk ya dunƙule. Da mamaki ya ce,

“Ba ayi maki gyaran kai bane?”

Kanta kawai ta ɗaga. Ya fahimci tana cikin damuwa don haka ya ce,

“Ihsan.”

Ta amsa a sanyaye. Ya ci gaba da cewa,

“Idan Sulaimanunki yana kusa da ke, ki fatattaki damuwa daga fuskarki kinji? Ki ɗauka kasancewana a kusa da ke shi ne maganin damuwarki. Na yi maki alƙawarin indai ina raye ba zan taɓa bari wani ya cutar min da ke ba. Ba zan taɓa yarda ki tagayyara ba.”

Da sauri tasa bayan hannunta tana goge idanun.

Tana zaune ya tsefe mata kan, ya kamo hannunta suka nufi banɗaki. A can yasa omo ya wanke kan suka dawo ciki yasa zani ya goge mata. Man shafawansu ya ɗiba ya goga mata, sannan suka fito ya kaita har gidan kitso.

Duk abubuwan da suke yi, Innayo tana kallonsu, sai dai baƙin ciki ya hanata furta komai. Ji take yi zata iya zama ajalin Ihsan.

***** *****

Shigar ƙananan kaya ya yi wanda suka dace da jikinsa. Yana tsaye a gaban modubi yana gyara gashin kansa, da mayuka masu kyau. Yau weekend babu inda suke zuwa, don haka ya zaɓi wannan rana a matsayin ranar da zai je wajen Baba Maigadi domin su ɗan taɓa hira.

Daga falonsu ya fito yana duba filawoyin gidan yadda duk suka yi yaushi. Hakan yasa ya fara kiran ma’aikatan gidan yana tambayarsu ba’asi.

Kamar ance masa ya ɗago ya zuba masu idanu cikin son gazgata su ɗinne kuwa kokuwa? Da gaske shi suke tunkarowa kowannensu fuska cike da walwala. Kamar zai ja da baya, domin gani ya yi Ihsan ta sake lalacewa. Da ƙyar ya dake ya tsaya, yana dubansu kamar zai fasa ihu.

“Yaya Irfaan Barka da warhaka.”

Sulaiman ya furta cikin fara’arsa. Irfaan bai amsa ba, sai ya dubi Sadiq da ya yi masu jagora, ya ji kamar ya shaƙe shi. Fuska babu fara’a ya amsa yana ƙoƙarin barin wurin ba tare da ya sake duban inda suke ba.

Dukkansu jikinsu ya yi sanyi, musamman Sulaiman da ya yi zaton wannan ziyara zai farantawa mutanan gidan, sai ya ga saɓanin hakan agun Irfaan.

Har Irfaan ya faru taku, sai kuma ya yi tunanin hakan bai kamata ba, don haka ya dawo da baya ya kama hannun Sulaiman yana murmushi,

“Sorry Sulaiman wani abu ne ya ɗan ɓata min rai. Amma naji daɗin ganinku.”

Sai a lokacin duk suka yi ajiyar zuciya, suka kuma ci gaba da binsa kamar jela. A falon Umma suka yada zango. Murmushin ƙarfin hali kawai yake yi, amma acan ƙasan zuciyarsa tsanar Ihsan ce kawai a ciki.

Yana kallon yadda take ƙauyanci, kamar a taɓa ta ta zura da gudu. Can ta dubi Sulaiman idanunta kamar wacce ta yi ƙarya ta ce,

“Yaya Sulaiman.”

Ya amsa mata yana dubanta. Hakan yasa idanun Irfaan suka koma kanta.

“Wai shi Yayan nan mai sanye da kayan arna baya taɓa dariya ne? Kazo mu koma kallon tsana yake mana.”

Mamaki yasa Irfaan zuba mata idanunsa. Da sauri ta duƙar da kai dan bata yi zaton ya ji ba. Shi kuwa kallonta da yake yi addu’a kawai yake jawowa yana roƙon Allah idan mayya ce Allah ya yi masa tsari da ita.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×