Skip to content
Part 1 of 3 in the Series Dutse Daya by Rukayya Haroun

“Ya hayyu Ya Ƙayyumu Birahamatika Astagisi, wayyo Allah na Ubangiji ka kawomin dauki, ya rahman ya rahimmmmmmmmm.”

Da dukkan karfin ta take rike da karfen gadon, gumi ya wanke dukkan ilahirin jikinta, ban da sunan Allah babu abun da yake fitowa a bakinta.

Likitoci guda biyu ne a kanta sai ma’aikatan jinya guda uku, sosai suka tsorata da yanayin nata. Daya daga cikin likitocin ne ya kalli abokan aikin nashi yace.

“Ku cigaba da bata kulawa zamu danyi magana da mijinta. Dr Lurwan zo muje mu tattauna.”

A nan suka bar Nurses suna kokarin Bata kulawa. a corridor din da zai sadaka da harabar asibitin suka tsaya.

Dr Lurwan ne ya kalli abokin aikin na shi yace “Wato Dr lamarin matar nan dole sai dai mu ceto abu daya ko ita ko jaririn dake cikinta, amma ya zama lallai mu yi magana da maigidan nata, idan har muka yi sakaci zamu iya rasa dukkansu. Ya zama lallai mu yi zaman ujila da shi don muji daga bakin shi ko? “Eh hakan ya yi Dr muyi hanzarin sanar da shi. ”

A Reception suka same shi ya hada kai da gwiwa, daka gan shi zaka tabbatar yana cikin tashin hankali, Dr ne ya bukaci su je ofishin daya daga cikin su dan tattaunawa mai muhimmanci.

Da ƙyar yake hada ragowar karfin halin daya rage mishi ya bisu office. Dr lurwan ya kalle shi cikin tausayawa, zuciyar shi a karye ya fara magana.

“Alhaji Haidar ya kamata ka bi komai a sannu, duk da lamari idan ya kasance haka dole sai ka shiga dimuwa, Amma ka sani komai da ka gani Allah shine mai yi. Am sorry to say gaskiya matar ka tana mataki na karshe, dole a cikin daya ayi guda. Walau ac eto rayuwar uwar a rasa babyn ko kuma a ceto baby ayi hakuri da uwar.”

Da mamakinsu sai suka tsinkayi muryar shi tana amo wajen fadin
“Na hakura da Uwar a ceto min babyn, a halin yanzu nafi bukatar babyn akan uwar.”

Dukkansu mamaki ne ya hanasu motsawa, amma sai suka yi mishi uzuri a karon farko, domin suna tunanin kunnuwan su ne bai ji musu daidai ba, Dr Habib ya kasa hakuri yace “ni kam Alhaji Haidar kasan mai kake fada kuwa? Sosai ya jijjiga kai tare da kara basu tabbaci da “Eh da dukkan hankalina da nutsuwata nake baku tabbacin hakan, domin sanin kanku ne na dade ina kaunar ganin jinina a duniya, duk kuwa da irin tarin dukiyar da Allah ya yi min, amma sai ya jarabceni da son haihuwa , gashi kuma bai bani rabo ba tsawon shekaru. Dan haka yanzu bazan iya zabar matata na rasa gudan jinina ba, na tabbatar ko gobe zan iya samun wacce zata aure ni kuma ta rikemin jaririna, amma na yanke shawarar a fiddo min jaririna ita kuma Allah ya jikanta.”

Basu ce mishi komai ba suka koma dakin mara lafiyar jikinsu duk babu kwari. Koda suka shiga dakin ta fara dawowa hayyacinta, idanunta cike da hawaye ta fara yiwa Dr Habib magana.

“Dr dan Allah kuyi min aiki ku cire babyn nan, jikina yana ba ni ba zan rayu ba. Hakika mun kwallafa rai akan abun da zamu haifa ni da mijina, ina so na cika mishi burin shi na ganin gudan jinin shi a duniya. Dan Allah Likita karku bata lokaci ku yi gaggawar yimin aiki karmu rasa babynmu dan naji motsin shi yana raguwa.”

Dukkan Nurses din dakin sai da suka zubar da kwalla, duk da basu san cewa mijinta ya zabi jariri akan ta ba.

Take aka shirya Emargency Cs, likita ya yi mata allurai sannan aka fito da ita zuwa dakin Tiyata. Haidar na ganin an fito da ita kwance akan gado ya yi hanzarin tahowa wajenta, ganin hakan ya saka Nurses din suka dakata da turata. Rike hannun ta ya yi tare da fashewa da kuka, bakin shi ya kasa furta koda kalma daya ce, ta yi murmushin karfin hali sannan ta ce,

“Masoyina a koda yaushe bana son ganin ka cikin damuwa, na tabbatar zaka bawa babynmu kulawa fiye da kulawar da zan ba shi, dan haka ka rike min abun da muka samu bisa amana idan Allah ya karbi rayuwata…”

Fashewa ta yi da kuka mai cin zuciya kafin kace mai bacci ya dauketa, dama duk acikin magagi take masa wannan Maganar.

Dr Lurwan ya kalli Nurses din fuska a tsuke ya ce “ku shiga da ita Thyter, kar kuyi westing time mana.” Haka suka wuce da ita yana bin su har aka zo bakin kofa, dole tasa ya dakata sabida babu mai damar shiga sai ma’aikatan lafiya.

Suna rufe kofar ya durkusa a bakin kofar ya saki kuka mai cin rai, ya dade a tsugune yana kuka babu mai rarrashi, sai dai mutane dake tai mishi kallon tausayawa.

Bayan awa daya da minti arba’in Dr Habib ya fito fuska ba annuri, ya yi hanyar ofishin shi, can sai ga Nurse rike da baby a wani kyakkyawan towel. Bata karaso gurin shi ba sai ga Dr Lurwan rike da wani jaririn, dukkansu a irin abun dauka guda aka sakasu.

Nurse din ta mika mishi babyn tareda gangarowar hawaye a fuskar ta, tana ba shi ta tafi tana kuka mai tsuma zuciya, domin ta saba da matar mai rasuwar sosai.

Dr Lurwan ya karaso tare da kara mika mishi dayan jaririn, take Haidar ya zaro idanu waje, shi kuwa Dr ya daga mishi kai alamar eh, fuska ba walwala ya fara magana.

“Alhamdulillah an yi aiki anyi nasarar ciro yara har guda biyu, mun zaci daya ashe Ubangiji ya boye dayan bai yi niyyar bayyanawa ba sai yau, I apologize for the loss of your wife, and I offer my condolences.”

Sandarewa Haidar ya yi domin zuciyar shi ta tafi hutu na dan lokaci, wai Nanar shi ce ta haifa mishi yan biyu, sannan ita ta mutu kamar yadda yaji Dr na fada mishi? Kukan Jariran ne ya dawo da shi duniyar daya fada ta tunani, a firgice ya kalli Dr Lurwan tare da cewa “Dr yanzu ya zan yi da wannan yaran?”

Cike da takaici ya kalle shi, da har zai yi magana sai ya fasa, domin a wannan yanayin shirun yafi maganar ciwo a wajen Haidar. Shima wuce wa ya yi ba tare daya furta ko kalma daya ba. Tuni hawaye sun cika idanun haidar umarni kawai suke jira su fara kwaranya.

Dutse Daya 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×