Skip to content
Part 2 of 3 in the Series Dutse Daya by Rukayya Haroun

“Alhamdulillahi an yi aiki anyi nasarar ciro yara har guda biyu, mun zaci daya ashe Ubangiji ya boye dayan bai yi niyyar bayyanawa ba sai yau. I apologize for the loss of your wife, and I offer my condolences.”

Sandarewa Haidar ya yi domin zuciyar shi ta tafi hutun na dan wani lokaci. Wai Nanar shi ce ta Haifa mishi Yan biyu, sannan itace ta mutu kamar yadda ya ji Dr na fada mishi? Kukan jariran ne ya dawo da shi daga duniyar tunani, a firgice ya kalli Dr lurwan tare da cewa

“To Dr yanzu ya zanyi da yaran nan?” Cike da takaici ya kalle shi, da har zai yi magana sai ya fasa, domin a wannan yanayin shirun yafi maganar ciwo a wajen Haidar. Shima wucewa ya yi ba tare daya furta ko kalma daya ba.

Tuni hawaye suka cika idanin Haidar umarni kawai suke jira su fara kwaranya. Cikin zafin nama ya fara bin bayan Dr Lurwan, kusan tare suka shigo Ofishin Dr Habib. A zaune suka same shi ya hada kai da gwiwa, idanun shi sun yi jazur dukkan jijiyoyin kan shi sun bayyana.

Dukkan su babu wanda ya nemi izini suka zauna kan kujerun dake gefen Dr. Shiru ne ya ratsa dakin na dan wani lokaci kana Haidar ya katse musu shirun da cewa. “Dan girman Allah Doctor ku taimaka min ku tayar min da matata, wallahi ina tsananin kaunarta. Hakika Nana ta kasance wani sashe na jikina, bazan iya rayuwa babu itaba. Itace farin cikin rayuwata, ni na yarda yaran su koma maman ta tash…

” Wani mugun kallo suke bin shi da shi kana Dr Habib ya fara magana cikin tsananin bacin rai
“Haidar ko dai kafara wannan shaye-shayen ne na zamani? hakika nasan kana da ilimin Boko dana Islama, Amma na lura jahilci ya lullubeka ta kowacce irin kofa. To idan baka sani ba gwanda kasan cewa, idan har da muna da dama to rayuwar Aisha zamu ceto ba jariren nan ba. To wai a tunanin ka mu mahaukata ne kamar ka, da ka zabi ita ta muku yaran su rayu, kayi zaton maganarka muka yi aiki da ita ne? Wallahi naso yaran ka rasa ba iya Aisha ba. Kawai dan dai rayuwa ko mutuwa ba’a hannunmu suke bane da kaga danyen aiki. Domin wannan yaran na tabbatar ba za suyi alfahari da kai a matsayin mahaifi ba, domin ka zabi su akan uwar data kawo su duniya. Tunda nake aiki asibiti ban taba haduwa da mutum mara Imani kamar kaba, dan haka yanzu idan ka fita waje ka daura aure, shi ne kawai abun da zakayi ka burgeni. Dan na tabbatar ko kaita ba za’ayi da kai ba kana dakin sabuwar amaryar ka.”

Dr Lurwan ne ya tashi yaje inda Dr Habib yake zaune bubbuga mishi kafada yake tare da cewa.

Haba Dr kayi hakuri mana, hakika Abokinka bai kyauta ba sam, irin kalaman dayayi amfani dasu a farko. Amma sanin kanka ne Allah ne mai yin komai, dan haka yanzu a maida hankali wajen cike cike, domin yin duk abun da ya dace don samun gawar domin a samu damar yi mata suttura kamar yadda musulinci ya hukunta.”

Computer shi ya jawo ya fara rubutu akan ciwon Nana Aishatu, dama yadda Cs ya zama sanadin mutuwarta. Bayan ya gama ne ya yi saving kana yai Printing out ya mikawa Haidar takardar. Mikewa ya yi ya fice daga dakin, tuni Haidar da Dr Lurwan suka take mishi baya. Inda aka ajiye gawar Aisha suka tunkara, har lokacin yaran suna hannun Haidar babu wanda ya yi mishi karar karba a cikinsu.

Kwance take sambal an lullube ta da wani koren zani, kana gani kasan gawace kwance babu alamar ruhi. Kamar mai koyan tafiya haka ya karasa inda take yaran duka ya ajiye a gefenta, fuskata ya bude yana taree da fashewa da kuka mai cin rai.

“Dan Allah Humaira ki tashi ki tausayamin Ina sonki, Aisha karki barni a cikin wanna duniyar Mai cike da kalubale masu yawa. Nanata ga yaranki nan suna bukatar dukkan kulawarki, basu San kowa ba sai ke, sun kwanta tsawon wata Tara da kwanaki a kasan mararki, suna bukatar albarka daga bakin ki. Hakika rashin uwa babbar barazana ce ga dukkan mutum, ballantana wannan jariran da Basu saba da kowa ba. Habebty ki tausayamin ni da jariran jaranki ki tashi karki tafi ki barmu. Innalillahi WA inna ilahi raji’un yau na rasa masoyiyata aishatul humair…”

Dr Habib Bai san lokacin da ya rungumi abokin nashi ba suka yi kasa suna kuka kamar wasu Yara, Dr Lurwan shima hawayen yake, domin yana da labarin tsantsar kaunar dake tsakanin ma’auratan. Da kyar Dr Lurwan ya shawo kansu suka yi shiru, sannan suka fara kiran wayar iyaye yan uwa da abokai na kusa dana nesa suna tabbatar da rasuwar Aishar bayan an ciro mata yara biyu.

Kafin a karasa da gawar Aisha unguwar ta cika da dan Adam, gidan kuwa cike yake da mata, iyaye yan uwa da kawaye sai koke koke ake dan nabu mai iya rarrashin wani. Cikin mintuna aka gama wanke Aisha da yake mace ce mai zafin nama, Yan uwa aka kira domin yi mata addu’ar bankwana. Nan ma wasu sai fito dasu akayi a sume domin zuciyar bata karba ba. Haka aka fito da ita daga cikin gidansu mata na kuka wasu na kiran sunan Buwayi gagara musali Allahu ahadu.

A makabarta ma da kyar Haidar ya iya kama kanta aka saka ta a kabarinta, ana sakata ya fadi sumamme. Haka wasu suka tsaya karasa binnewa wasu kuma suka dauke shi aka kaishi cikin mota sai asibiti.

Bayan an dawo daga kai Aisha ne, matan dake cikin gida labari ya kai musu Haidar ya fadi yanzu haka yana asibiti. Maman Hafiz yayace a wajen Haidar ta fashe da kuka tare da fadin “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, yanzu ace Aisha ta mutunma bamu tsira ba, haba wannan wanni irin bala’i ne. Tunda ta mutu ai sai asirin ya karye ko? ” Ta kalli kanwarta wanda Hafiz yake bi. Itama amsawa ta yi da.” Maman Hafiz ke sanin kanki ne Aisha gurin arnan kan dutse take zuwa, da ina zai karye nan kusa ai wallahi sai mun ta shi kan dan uwanmu.” Karamar kanwarsu Jawahir dake rike da daya daga cikin jariren tana kuka ta fara magana.

Haba Maman Hafiz ai yau ko dan mutuwa Aunty Humaira taci ku raga mata, ace mutum ya mutu ma bai tsira ba, Dan Allah ku bita da addu’a domin itakam tata tayi kyau saura mu…”

“Kiyi mana shiru munafukar banza mara kishin dan uwanta, wayasani kema ko ta sakaki a layin ne ta tafi tabar baya da kura. Dan naga mijinki kema sai nan nan yake dake , ki kiyayemu.” Maman Hafiz na gama magana ta tashi suka fice daga dakin. Yan uwan Aisha dake Parlour sun ji duk irin tattaunarwar data kasance tsakanin Yan uwan Haidar, domin ba’a hankali suke maganar ba, dama burinsu kowa yaji halin da ake ciki. Ita kam Jawahir kara kankame jaririn da har yanzu bata san namiji ne ko mace ba, kuka take mai ban tausayi ji take kamar ta maida jariran cikin jikinta, har yanzu ko ganin irin kalarsu babu wanda ya yi balle asan Matane ko Maza.

Yayar Aisha ce ta shigo dauke da dayan jaririn dayan hannunta dauke da jakar jarirai, da yake shayarwa itama take. Haka ta zauna kusa da Jawahir rungume juna sukai suna cigaba da kuka mai tada hankali. Bayan sun rage kukan Yaya Maryam ta hai harhadawa yaran Madara, dayake tana hadawa yarta da madara dole tasa akaje gida da yake basu da nisa aka dauko domin bawa yaran.

Asibiti

Tunda aka shiga da Haidar ko motsi baya yi, amma likitoci sun tabbatar yana da sauran numfashi, doguwar suma ya yi. Sosai likitoci suka taru a kan shi suna ba shi duk wata kulawar daya kamata.

A wajen asibiti kuwa mai Napep na ajiye Maman Hafiz da Rauda koke koke suka fara, kamar ce musu akayi Haidar din mutuwa ya yi. Mutane sai binsu suke da idanu. Reception suka nufa dan jin dakin da Dan uwansu yake kwance. Mai kula da wajen ce tace musu yana Room 104 a gigice suka nufi dakin tare da kuma fashewa da sabon kuka.

Babu kowa a cikin dakin sai shi kadai a kwance babu alamar motsi. Maman Hafiz ta yo kanshi tare da jijjiga shi tana fadin ” innalillahi shi kenan shima ya mutu, Aisha kin cuce mu, yau mun shiga uku…”

Duk addu’ar da za ta kori manya da kananan shedanu shike fitowa daga bakin Nana, ayatul kursiyyu, falaq da Nasee su take kara nanatawa.

A firgice Haidar ya tashi tare da karewa dakin kallon tsanaki, mamaki yake sosai ganin shi taresa iyalinsa, duban shi ya dawo da shi gurin Nana, tuni hawaye masu kauri suka fara yin ambaliya a kan firgitacciyar fuskar shi, kamar mai koyan magana ya fara da cewa,

“Aishatul Humaira kece? Alhamdulillah masha Allahu lakuwwata illah bhillah.” Rungumeta ya yi tare da fashewa da kuka mai ban tausayi. Itama kuka take na rashin sanin makama. Sosai suke kankame da juna kamar wani zai zo ya rabasu, sai da Hydar ya yi kuka mai isar shi sannan ya fara aikin rarrashin matar ta shi.

Cikin karfin hali Nana ta kalli mijin nata tace mishi suje su dauro alwala su gabatar da sallah, domin yanzu karfe uku ne da minti arba’in na dare. Haka kuwa suka tashi suka yi alwala sannan suka gabatar da sallah.

Sun dade a zaune suna addu’o’in neman kariya daga dukkan abun ki, har aka fara kiraye-kirayen sallar asuba suna zaune kan sallaya. Nan ma tare suka kara gabatar da sallarsu cikin jam’i, har gari ya fara wayewa suna addu’o’i. Nana bata daina mamakin sabon al’amarin daya ziyarcesu ba.

Tsawon shekaru da suka kwashe tare da Haydar bai taba kuskuren rasa sallar asuba a masallaci ba, sannan tun bayan tashin shi daga bacci mai cike da firgici komai ya canja. Tabbas Nana tana da tarin tambayoyi a tare da ita, amma ta yiwa kanta alkawari, a zaman takewarsu da mijinta bazata taba takura mishi akan wani al’amari ba, ta tabbatar idan hali ya yi zata ji komai.

Nana bata kara shiga rudu ba sai da ta tashi zata je kitchen dan nema musu abun karyawa, sai ta ji ya rikota da karfin shi, tare da cewa. “Humairata dan Allah karki tafi, Ina so ki zauna dani har karshen rayuwata, na yadda na zauna da yunwa tsawon lokaci, amma bazan iya jure rashinki ba…”

Murmushi ta yi wanda har sai da fararen hakoranta dake dauke da hakorin makka ya bayyana. Lumshe idanu tayi mai cike da kauna da cikkakkiyar kulawa, dan karamin bakinta ta bude ta fara magana cikin muryarta mai cike da nutsuwa.

“Haba Babyn me meyasa kake so ka sakawa kanka damuwa ne? Nasan ka sani kuma zan kara sanar dakai, komai ya yi tsanani to akwai sauki a gaba, ni dai fatana ka cigaba da addu’a in sha Allah komai zai zo mana da sauki.”

Sosai yaji nutsuwa ta ziyarci zuciyar shi, yana daya daga cikin abubuwan da yasa yake tsananin son Aisha. Macece mai Addini, hakuri, gaskiya, kyau, kulawa da miji, da son mutane. Tunda yake ganin mace mai biyayyar aure bai taba cin karo da kamar Nana Aishatul humaita ba, wannan dalilin yasa yake kiranta da suna mabanbanta.

Duk lokacin da tagan shi cikin damuwa, takan kawar da tata damuwar ta shiga yi masa zantuttuka masu dadi da Nasiha mai ratsa jiki. Humaira bata barin Hydar ya kwana da kunci a zuciyar shi, sai tasan yadda ta yi ta wanke masa zuciya da gwagwalan kalamanta kamar yadda yake fada a kowanni lokaci.

Lumshe idanu ya yi tare da yi mata kyawawan addu’o’i kamar yadda ya saba a kullum.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Dutse Ɗaya 1Dutse Daya 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×