Skip to content
Part 21 of 37 in the Series Fadime by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

LITTAFI NA BIYU

Lagos

Tsayawa ta yi tana ƙarewa kanta kallo cikin tangamemen madubin da aka ƙawata banɗakin da shi. Abubawa da yawa take tunawa na rayuwarta da ta gabata, abubuwa da yawa kuma ba ta iya tunawar. Akwai wani abu da take ƙoƙarin yaƙi da shi ganin yana son ta da mata da kyakkyawar zuciyar da ta daɗe da ajiyeta a tun ranar da ta buɗi ido da gawar Mamuda, idonsa soke cikin dafin kibiyar da ba ta iya mantawa. A yanzu kam da take cikin garin Lagos, cikin gidan kyakkyawar budurwar Linda ba ta fatan wani abu da zai katse mata sabuwar rayuwar da take son farawa ko da tausayi ne ko jin ƙai, kai uwa uba imani gabaɗaya ta dunƙule su ta ɗorawa Abbati dan amfanarsa shi kaɗai tal! Tabbas za ta yi koma menene ganin rayuwar tilon ɗan nata tayi irin nagartar da take so. Za kuma ta maida kome ba kome ba gurin gina ta ta rayuwar da take son fara ta a yau ko kuma gobe. Fatanta ta manta kowa, ta kuma shafe duk wani baƙin ciki shafewa irin ta baƙar tawadar da aka zanata jikin farar takarda bayan an tsumbula ta cikin ruwa. Murmushi ta saki ita kaɗai tana kallon kanta cikin madubin, a hankali kuma ta jawo shampoo ɗin dake gabanta ta fara kwarara shi cikin tattausan gashin nata.

Cikin takura kai ta fara ƙoƙarin saka dogon wandon jeans ɗin da Linda ta fito mata da shi da ‘yar matsattsiyar rigar. Kankace mene wannan ta haɗe tamkar wata Baby Doll cikin kayan ƙawarta ta, ko muce uwar ɗakin nata. Ɗan stole ɗin mudubin ta jawo ta zauna hannunta riƙe da kwalin tabar da idan ta kunna wannan ta kunna ta Ashirin da biyar ke nan cikin ƙasa da awa biyar tun haɗuwarta da Linda. Tsaf! Ta sauke lumsassun idanuwan nata cikin na Linda da ta yi ƙamewar mintuna tana ƙarewa Fadi kallo fuskarta dauke da mamaki.

“Ya rabb! Faɗi kin kashe ni da tunanin wacece ke, na rantse ba wanda zai ganki yanzu yace ke ce ta cikin tashar nan, kin koma tamkar wata yar ƙasar Ethiopia. An ya Faɗi ba ki da alaka da larabawa ko sarakuna?”

‘Mijina da aka kashe Balarabe ne.’

Sai kuma ta sakar mata murmushi mai sauti tana fesar da hayaƙin sigarinta ta hanci. “Kinsan me? Da farko dai ce miki zanyi ki kira ogan naki dan naji sun karɓe ni ko kuwa, sannan kuma ki manta kinsan ni da Faɗimw, bariki na shigo, ba makaranta ba. Zaki iya zaɓar kowane suna ki sanyamin amman banda sunan da zai dinga tuna mini wani abu da ya gabata a baya. Sai abu na ƙarshe, na yarda zan miki koma menene da kuma ladabin da zaki mamaki, amman da sharaɗi. Karki takurani mu’amala da ɗa namiji kin dai gane kowanne mu’amala nake nufi, karkuma muyi duk wani abu marar kyau gaban yaron nan, zanyi koma meye dan ganin na inganta rayuwarsa da tarbiyyarsa, dan haka ba na fatan ya kalli wani abu marar kyau daga gare ni ko gareki ko ga waninmu. Idan kin amince mini hakan ni kuma na yarda zan dawwama dake daga nan har ƙarshen rayuwarmu.”

Ta furta tana sauke idanuwanta kan Abbati dake barci kishirɓan tun bayan wankan da ta masa.

Raf-Raf! Ta sau mata tafi tana mai jinjina maganganun Fadin. Jikin madubin tayi a hankali ta zauna gefensa, hannayenta ta chusa cikin gashin nata tana mai yamutsa ‘shi kamar mai tunani. Da sauri kuma sai ta dago tana duban Fadimen da idonta ke lumshe tana kallon rufin dakin.

“Wane suna ma na ji yaron nan na kiranki? Ammi? Bari to na kai ki da Amin.” Buɗe idanuwanta ta yi tana gyaɗa mata kai.

“To Ammi, Idan da takarda ma ki ɗauko ki rubuta. Ni Linda na yi Alƙawarin bazan taɓayin abu marar kyau gaban yaro ba, ba kuma zan takura ki kiyi abinda baki so ba, ko da kuwa ci gabanki ne. Dan haka karki damu. A bayan son taimakonki da nake son yi, harda ƙauna irin ta yan uwantaka da naji ina miki a tun ɗora idanuna da na yi kanki karo na farko. Abbati kuma renonsa bazai hanaki kome ba bare ya taɓa kasuwancinki. Akwai makaranta da aka buɗe nesa kaɗan damu ce ta yara masu shekarunsa, ita zamu samu mu saka shi, sai a samu mai kula da shi, kinga haka zaki samu damar kasuwancinki kije kuma duk inda kike so yaronki na cikin Amana. Ya kika gani ?” Gyaɗa ma ta kai ta yi alamar duka zancenta ya yi.

“Okay to shi ke nan, tunda da gajiya tare da ke, ki kwanta yanzu, gobe sai mu fita, ko kuma ki huta har kwana uku kafin na kaiki gurin oga.”

Daga haka ta fita. Ita kuma ta kishingiɗa idanuwanta a rufe tana jin kamar yanzu aka sake haihuwarta. Cikin tunaninta babu kome sai ƙiyasin me zai faru daga gobe?

***** *****

Bayan Kwana Uku

Harta ɗau ‘yar jakarta da Linda ta bata za su fita idanuwanta suka sauka kan Ledar Viva. Gabanta ya faɗi da ta tuna ita ce silar zuwanta garin nan. Kamar ta juya idan suka dawo ta duba a nutse, sai dai kuma haka kawai ta ji wani abu na fisgarta zuwa ga ledar jikinta kuma na daɗa sanyi.

A hankali ta miƙa hannu ta jawo Ledar kamar me tsoron tarda saƙon kwanakin da suka rage mata a duniya, ta hau zazzageta. Murmushi ya kuɓce mata ganin takardunsa ne duka na shaidar kammala karatunsa. Sai kuma wani kyakkyawan Zoben Azurfa. A sannan ne kuma ta kula da wata zungureriyar Ambulan da aka manne bakinta da cingam. Ambulan ɗin da daga ita dukkan wani buri da take da shi kafin lokacin ya rushe.

Gabanta ne ya faɗi ganin sunanta ɓaro-ɓaro a jikinta. Zuciyarta ta tsinke ganin zanen rubutunsa. Shafa rubutun take tana jin ɗumin hawayen da ke bin kuncinta na zarcewa har saman laɓɓanta. ‘Mamuda!’ wata halitta ce a rayuwarta da ba za ta taɓa daina zubar masa da hawaye ba, haka ba ta zaton za ta ƙara samun halittar da za ta gwada mata ƙauna irin sa. Kome ya dawo mata sabo a yanzun.

Cikin hawayen da bata san yadda za ta hana zubarsu ba ta fara karanta takardar. Gata nan date ɗinta ya nuna ya rubuta ta kwana goma sha huɗu kafin mutuwarsa.

Ki yi hakuri!

Banji a jikina zan ƙara kwatankwacin watannin da na yi da ke ba. Haka banji a jikina za ki tozarta a yayin da babu Ni ba. Ki yi hakuri! Ban kuma ji a jikina za ki illata rayuwarki saboda rashi na ba. Na sani, a lokacin da za ki ga wannan takardar ba na duniyar nan tamu, na kuma sani ba za ki taɓa fasa yin abinda zan roƙe ki ba.

Zan roƙe ƙi alfarmar da ban taɓa roƙarƙi irinta ba. Ki yi mini wannan alfarmar ba dan ni ba, ba kuma dan ke ba, sai don yaron mu Abbati.

Fati, kome matsin rayuwa karki kuskura ki lalata gabanki irin yadda na ɓata nawa. A kome za ki yi ki duba gabanki wanda na tabbata ba za ki hango kome ba sai ci gaban Abbati. Haka Kome rintsi karki ciyar da shi da abinda yake haram. Ki yi haƙuri da kalar rayuwarki, ki kuma yi koma menene da ƙarfinki ta tsarkakkiyar hanya gurin gina gabanku.

Abinda ba ki sani ba, silar aikata haram ya kawo ni gurin nan da a yau nake nadamar kasancewata cikinsa, nake kuma nadamar ƙin bin abinda mahaifina ke so saboda gudun saɓawa Allah. Sai kuma gashi na zo ina aikata abin da yafi munin wanda mahaifina ke yi. Ina kashe musulmi ina kashe duk wata halitta da ta tsaya a gabana.

Da ace na san rayuwa za ta kawo Ni nan da tun ina shekaru 15 zan bawa mahaifina haɗin kai, a tun ranar da na gane menene sana’arsa da me ya auri mahaifiyarmu da kuma me ya same mu har muka rayu tsawon wannan shekarun.

Kamar yadda na fada miki Balarabe ne. Ya taho Nijeriya shi da wasu abokansa. Anan Lagos ya haɗu da mahaifiyata ya aure ta bayan an kai ruwa rana ita da ‘yan uwanta.

Ba su cika shekaru biyu da aure ba aka same ni. Bayan shekara biyar da haihuwata Allah ya mata rasuwa wanda har yau ba a san abinda ya kashe ta ba an dai wayi gari ne kawai an ga gawarta. Duk da wani likita ya ce zuciyarta ce ta buga irin bugu dayan nan. Allah dai masa Ni. Ta dai mutu ta bar ni Ni kadai sai mahaifina.

Yan uwan mahaifiyata sun so karɓata amma ya hana, ya ce zai nemo wacce za ta ci gaba da kula da Ni har zuwa girmana. To, haka na tashi da mahaifina cikin wata irin kulawa da bansan ya zan miki bayaninta ba har zuwa lokacin da na cika shekaru 18 a ranar da na kammala secondry ranar na gane waye mahaifina a bayan kyakkyawar surarsa.

Na dawo gida a cikin rashin saninsa na zan dawo ranar. A falon gidan na tarda su tsirara shi da Abokansa suna aikata masha’a. Mahaifina babban ɗan luwaɗi ni da babu na biyunsa kaf lagos dan kuwa har daga ƙasashen ƙetare ake hayarsa, Fati.

Wani abu ne wannan da bansan ya zan wasafta miki girmansa cikin idanuwana ba. Abu mai muhimmanci dai shi ne bayan ya tabbata na gansu ya jawo Ni yana rarrashina da nuna mini ba fa kome ba ne hakan, nan gaba Ni yake so ma na gaje shi. Ina kuka ina rokansa ya daina, ƙarshe ma na bar cin abinci da duk wata walwala saboda haka. Ganin yana ƙoƙarin rasa ni ya sa yi mini alƙawarin ya bari.

A haka rayuwar ta tafi ban ƙara kama shi da wani lefin ba har zuwa lokacin da na kammala Degree na. A sannan nan ne ya fara fiddo da maitarsa fili kaina shi da Abokansa. Ashe su duka jira suke in kai lokacin da za su jawo Ni cikinsu. Su duka sun saka ‘ya’yansu ciki ni kaɗai na rage. Take na nuna musu ko za su kashe Ni ba zanyi abinda suke so ba. Ƙarshe ma tattarawa na yi na bar gidan.

Bayan wasu lokuta na dawo ko mahaifi na ya shiga nutsuwarsa ashe duk a banza. A haka in tafi in dawo har watarana na dawo mahaifina ya mini alƙawari a karo na biyu cewar ya tuba ba ya sake aikatawa.

Mun zauna tsawon wata biyu cikin kwanciyar hankali, kafin wani dare kamar cikin barcina na ji an tsikari min abinda ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai bayan wasu awannin. Na farka na ganni Ni da mahaifina tumɓur, zigidir, ya gama aikata abinda yake muradi kaina ba tare da yarda ta ba. Ban san ya zan kwatanta miki girman bakin cikin da ya mamaye Ni ba, na dai san lokacin da na shaƙe mahaifina, ƙarshe na sauke masa yatsuna biyar a fuskarsa. Na mari mahaifina Fati, abinda har abada ba zan bar nadamarsa ba. Akan ido na ya goge kwallar idonsa sa’adda nake harhaɗa takarduna. Na fice daga gidan na fice daga rayuwarsa gabaɗaya na shiga duniya.

To akan hanyata ta zuwa Kano ne dan na gina sabuwar rayuwa ta a can, su Imam suka tare mu, na tsira ba dan kome ba sai dan kyawun da na yiwa Imam. Wannan dalili ya sa ya ɗauko ni ya kawoni cikinsu aka fara ba ni horo har zuwa sanda na yi gogewar da ta silarta na haɗu da ke. Kinji wanene Ni.

A yanzu ina roƙanƙi da duk ranar da kika samu kuɓuta daga nan ki tafi lagos can gurin Mahaifina. Na tabbata zuwa yanzu ya yi girman da ba zai iya aikata wata alfasha ba. Waya sani ma ko ya tuba. Ki ba shi labarin abinda kuskurensa ya jama tilon ɗansa. Ke kuma tabbatar masa da cewar ke matata ce dan haka duk wani abu da yasan ya yi shi da sunana ya mallaka miki shi. Ki nuna masa zoben Azurfar da za ki tarar tare da kayan nan, ita kaɗaice za ta ba shi shaidar Ni na aiko ki gare sa.

Ki rayu da Abbati rayuwa mai inganci.

Mamuda!

Izuwa yanzu hawayen sun ƙafe, sai tsantsar tausayin Mamuda daya mamayeta. Ashe dai ba ita kaɗai aka halitto da damuwa ba, ashe dai masu kuɗi da masu ilimi suma suna da irin tasu damuwar. Ashe ita wauta za ta yi da ta zaɓi saɓawa mahaliccinta saboda ta gaji da irin ta ta damuwar. Ashe ga wani can da ta rayu da shi tsawon shekara biyu garin ya gujewa saɓawa mahallicinsa ya guji mahaifinsa, ya zo ya zama yana aikata abinda idan bai yi kunnen doki da ubansa ba, to kuwa zai fi shi. Shin me ya sa ba za ta gode ba da aka barta da lafiyarta ba? Ta gano darasin, tabbas ta gano abinda Mamuda bai gano ba. A cikin layi biyu na rubutun ta gano lefin Mamuda, silar kuma kome da ya same Shi, wato garaje. Mahaifinsa ya yi nadama, nadamar da ta tabbata ko’ina yake yanzu to fa yana tur! Da halinsa ne, ba kuma sai bayan ya tafi ya yi ta ba. A’a, nadama ta same shi ne a tun lokacin da yatsun Mamuda biyar suka wanzu a fuskarsa. Mamuda bai kula da nadamarsa ba sai hawayensa, bai san hawayen nan shi ne nadamar ba. Shin me ya faru bayan nan? Bata sani ba, tana kuma buƙatar sanin. Dan haka ta ƙara duba Address ɗin, ta miƙe da niyyar zuwa gurin Linda. Sai dai ma turus ta yi ganinta tsaye a bakin ƙofa tana binta da wani irin kallo mai kama da na ƙasƙanci.

“Yadda kika zaburo ɗin nan ina gargaɗinki da ba cewa za ki yi kin fasa fitar nan ba? Ammi ina da ƙuduri mai yawa kanki, ba kuma na son harka da mutumin da baya magana ɗaya, baya cika alƙawari.”

Wani yawu ta haɗiya muƙut! Jin gargaɗin da Linda take mata. Sai yanzu take tuna kalamanta, idan aka shiga, babu fita.

“Ai ban riga na shiga ba.”

Zata rantse da Allah bata san sa’adda kalaman suka haɗa kansu ba. Sai dai sun fita da wani kwarin gwiwa da ya sakata rungume hannunta tana kallon cikin idanuwanta.

“Haka kika ce? A kwana uku kaɗai kike ƙoƙarin nuna mini rashin halacci irin naku hausawa? Wane irin halitta ne ku wai? Me ya sa kuke da yawan karya alƙawari?”

Ta furta tana ƙoƙarin saita kanta, ba ta so tun yanzu ta nuna mata ɗayar kalar ta ta. Sani ne bata yi ba, a tun ranar da ta ɗora idanuwanta kanta take jin sha’awarta, a yanzu kuwa, babu wata halitta da take ƙauna irin ta, za ta iya mallaka mata kome dan ganin ta aure ta.

“Babu alƙawari a abinda yake na saɓawa Allah!”

Wasu kalmomin nata suka fisgota daga tunanin da ta shilla. Ai sai ta saki baki tana dubanta, idanuwanta na ƙanƙancewa.

<< Fadime 20Fadime 22 >>

2 thoughts on “Fadime 21”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×