Skip to content
Part 26 of 37 in the Series Fadime by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

12 December, 2014

Ba wai dan ba a taɓa irin ta ba ne ya saka su cika ba. Ba kuma wai dan wani uba bai taɓa kashe ɗansa ba ya saka su tururuwar shiga, a’a, rabinsu labari ya je musu yadda ‘Yan Sanda a binciken farko suka tabbatar da gaskiyar wanda ya yi kisa, sai dai kuma shi ya ƙi yarda da yayin. Suna so su ga wane wawa ne shi da zai ja da ‘Yan Sandan Legas. Suna so su ga yadda za a ƙare shari’ar ba tare da yau ɗin an yanke masa hukunci ba. Yayin da kwatarsu suke so su ga ɗan karambanin da zai yi gangancin tsaya masa a matsayin lawyer. To koma dai mene kotun ta yi wani irin ta cika ta yadda sai da aka rage wasu mutanen.

Ita ce shari’ar farko, dan haka da su aka fara.

“Lauyoyin da za su fara gabatar da ƙara suna nan?”

Alƙalin ya furta a bayan an kira ƙarar su Sagir ya gama nazarin takardar da aka miƙa masa.

Wani fari ƙato ya miƙe tsaye.

“Sunana Dawud Jagazi, ni ne lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara.

Yana gama furtawa ya zauna.

Alƙalin ya mai da dubansa ga Sagir da tunda aka shigo da shi kan shi ke sunkuye.

“Ka na da lauyan da zai tsaya maka?”

Idanuwansa ya wulla tsakiyar gurin yana lalubar Yaya. Zuciyarsa ta buga da ƙarfi sa’ilin da suka haɗa ido ya nuna masa babu. Cike da karaya ya buɗe baki zai furta babu, a lokacin ne kuma buɗaɗɗiyar muryarta ta ratsa gurin.

“I’am here My Lord, I apologise for being late!”

Ba Yaya ne kaɗai ya kaɗu da ganinta ba, hatta Faɗime da ke can gefe sai da yanayinta ya canja ta ɗago tana sauke dubanta ga Linda, da ido take tambayarta wannan me yanayin Turmin fa? Watsa mata hannu ta yi alamun ba ta sani ba. Sagir kam mamakinsa kaɗan ne. Ya sani idan har ta ci sunan mayyarsa to kuwa za ta iya tsaya masa kan lamarin. Sai dai bai yi zaton har haka Kare ya cinye zuciyarta ba. Murmushi ta masa tana yashe masa fararen haƙoranta irin na zomo. A kan takunta na Agwaga ta ƙarasa tsakiyar gurin ba tare da ta ɗauke dubanta daga gare shi ba. Duƙawa ta yi ta kai gaisuwa ga Alƙalin.

“Sunana Zubaida Rabe, ni ce lauyar wanda ake ƙara.”

Hayaniya ta ɗan tashi a gurin. Da yawansu tattaunawa suke kan gangancinta, ta rasa dawa za ta jera ma sai da Jagazi, ko da yake idan mutum ya ce zai haɗiyi gatari sai ka sakar masa ƙotar cikin mutuntawa.

Bayan an karantawa Sagir laifin da hukuma ke zargin shi da shi, sai Alƙalin ya dube shi.

“Kaji ƙarar da ake akan ka ?”

“Na ji ya mai girma Mai Shari’a”

“Kuma ka fahimta sosai, ko akwai buƙatar a fassara maka zuwa yaren da kafi fahimta?”

“Na fahimta sosai”.

“To menene amsar ka ga wannan tuhumar?”

“Ban aikata ba ya mai girma mai sharia.”

Bayan ya ɗan yi rubutu, Alƙali ya juya kan Barr. Jagazi
“Muna saurarenku, ko kuna da wata hujja da za ku gabatar gaban kotu dan tabbatar da tuhumar da kuke masa?

Barista Jagazi ya miƙe ya isa ga Sagir.

“Akwai mu da hujjoji gamsassu ya mai sharia, muna neman alfarmar kotu dan mu gabatar da wanda ake kara matsayin shaidar masu ƙara na farko”

“Kotu ta baka dama “.

Bayan Sagir ya shiga akwatin shaida, Barr Jagazi ya ci gaba da yi masa tambayoyi

“Ko za ka iya gayawa kotu sunan ka?

“Sunana Sagir Muhammad Maƙarfi. “

“A ina kake da zama, kuma mene ne sana’arka?”

“Anan Lagos nake zaune, ina koyarwa a Makarantar Little Angels.”

Ranar Tara ga watan Satumba (December), ko za ka iya faɗawa kotu a ina kake a wannan ranar?

“Ina gidana ina barci, na tashi wuraren ƙarfe tara, nan na shirya da sauri na isa makarantar da nake koyarwa da misalin karfe 9:30. Anan na iske yaro a ofis ɗi na ya daɗe da mutuwa, ganin haka ya saka ni kiran ‘yan sanda na sanar musu.”

“Ta ya ya kasan ya daɗe da mutuwar? Kana da ilimin sanin daɗewar gawa ne?”

Shiru ya masa kasancewar ba ya da amsar.

Barr Jagazi ya ci gaba da cewa

“Wannan shi ke nuna kai ka kashe shi, saboda ka ɓoye lefinka ko kuma ka wahalar da Shari’a ya saka ka kiran ‘Yan sanda ka sanar musu da ka tsinci gawa a ofishinka.”

“Da ni na kashe shi ba zan kira Yan Sanda ba.”

“Wannan ba hujja ba ce, abu ne mai sauƙi da kowa zai iya yi. Kamar ni ne muna wasa da yaro na hankaɗa shi cikin rijiya, na je gida na ce ya faɗa rijiya.”

“Amma mene dalilin da zan kashe ɗan cikina, yaro ƙarami kuma ɗalibi na a cikin office ɗi na?”

“Shi ne abinda nake so ka yiwa kotu bayani, mene dalilinka na kashe ɗan cikinka? Saboda ba ka son shi tun yana ciki ko? Ko kuwa saboda fyaɗe ka ma uwar…”

“Objection My Lord! Barista yana wuce tsarin tuhumarsa, yana cusa kalmomi a bakin wanda ake tuhuma kuma yana tambayoyin da basu da alaƙa da abinda ke gaban kotu.

Barr. Cingam ta furta a bayan ta miƙe tsaye.

Alkali Ya sube shi, “Ka kula da irin tambayoyinka.”

“Na gode.”

Ta furta tana komawa mazauninta.

“A baya ka ambaci cewa karfe 9:30 na safe ka shiga makaranta, dama shi ne lokacin da kowane Malami ke shiga makarantar?”

“A’a, ni kaina bansan dalilin makarata ranar ba, wani barci ne ya ɗebe ni, sa’adda na farka ma lokaci ya ƙure.”

“Ko akwai wanda ya ga shigarka lokacin?”

“Babu.”

“Good! Sai kuma gashi ina da shaidar shigarka cikin makarantar da misalin ƙarfe 7:30.”

“Ban gane ba!”

“Za ka gane yanzu. “

Ya furta. Sannan ya dubi Alƙali

“Iya tambayoyin mu ke nan ya Mai Shari’a, sai dai idan an ba mu dama za mu gabatar da shaida ta biyu.”

Alƙali bayan kammala ‘yan rubuce-rubucen shi, sai ya bawa Barr. Cingam dama dan gabatar da nata tambayoyin ga wanda ake tuhuma. Sakamakon rashin tambayoyinta ne yasa Alƙali bawa Barr. jagazi dama ya gabatar da shaida na gaba, wato Samuel.

Mr. Samuel dogo, zangalele, ya aje gashin baki irin na mutanen Hitler. Shi ya taso ya tsaya a akwatin shaida. Clerk (magatakarda) ya biya masa rantsuwa, shi kuma ya ɗaga hannunsa na dama yana mai maimaitawa.

“Mr. Samuel ko za ka yiwa kotu bayanin inda kake aiki ?”

Ni Mai Gadi ne, ina aiki a makarantar Little Angels.

“Ko kasan wanda ake tuhuma ɗin nan wato Sagir?”

“Eh na san shi kwarai, malami ne a makarantar da nake aiki.”

“Madalla, Samuel ko za ka iya maida zuciyarka baya zuwa ranar Tara ga watan Satumba ka yiwa kotu bayani akan ranar?”

“Eh sosai. Ranar kamar kowace rana ina wurin aiki na. Kuma duk ma’aikatan mu sun je aiki harda Malam Sagir, da ƙarfe 7:30am ya shigo kamar kowacce rana. Haka na ga fitarsa wuraren 8:30am dan har ina mamakin abinda zai saka shi fita daga zuwansa. Sai dai ban ga dawowarsa ba sai gani na yi za a fita da shi a motar ‘yan sanda. Sagir yana da kirki sosai, ba zan masa ƙarya ba kan wannan abin, i saw him at that time, I swear by Allah!”

“Kar ka damu, to shi kuma yaron fa, yaushe ya shigo cikin makarantar?”

“Da ƙarfe 8:00am aka kawo shi, dan har ya yi hira da ni, ya ba ni Cake ɗin da ke hannunsa.”

Ya furta yana mai ƙoƙarin mai da kwallar da ta tarar masa. Da alama yana cikin masu jin raɗaɗin mutuwar yanzu.

Ji ya yi kamar yana rayuwa a tsakanin suma da mafarki. A lokacin da Jagazi ya furta around 7:30am ya shigo makarantar ya ɗauka kawai sharri ne irin na laulayoyi da suke iya bin kowacce hanya idan suna son ba ka lefi, Sai dai a yanzu tunaninsa ya canja da ya ga Samuel a gabansa yana tabbatar da faruwar hakan. Tun shigowarsa garin Lagos babu mutumin da ya ji daɗin mu’amala da shi irin Samuel, wata irin girmamawa ke tsakaninsu, kai hatta gidan da yake ciki shi ne ya masa hanyar samunsa a matsayinsa na ɗan gari. Abu ɗaya ya sani babu abinda ya haɗa shi da Samuel da zai masa ƙarya. Haka a saninsa da shi ko da yake a matsayin mai gadi to fa mutum ne shi mai wadatar zuci da ya yarda ya nemi kome da ƙarfinsa. A iyakar hangawarsa bai ga ta yadda za ai ya yarda a saye shi ba dan ya bada karya kansa ko da kuwa nawa ne. Duƙar da kansa ya yi yana mai tsirawa ankwar hannunsa ido. Ga mamakinsa ji ya yi yana tambayar kansa to ko da gaske shi ne ya kashe Abbatin? Amma kuma ai ba zai ce ga ranar da ya taɓa shan giya ba.

“Ko da wannan aka yi duba za a gane Sagir ya daɗe da gama shirya hakan. Ya kuma ci nasara ba tare da an ankara ba. Ya shigo makaranta a lokacin da ya saba shigowa. Ya yi amfani da wannan damar domin ya ɗauke hankalin jama’a daga kansa. Wannan shi ya tabbatar mana Sagir yana cikin makarantar bai fita ba har zuwa lokacin da ya kira ‘yan sanda. Fitarsa kuma da Samuel ya gani ba shi ba ne. Kasancewar ya daɗe yana shirya hakan shi ya sa yake aiki tare da wani, wanda shi ne Sagir ya bawa motarsa ya fita da ita dan ya kauda tunanin mutanen da za su za ci yana cikin makarantar. Idan kotu ba ta gamsu da hakan ba, za a iya jinkirta lamarin saboda mu samu damar kawo shaidar wanda ya taya Sagir kisan. Iya tambayarmu kenan.”

Ai Sagir kawai sai ya hangame baki yana ganin yadda ake ƙoƙarin maida shi mashayin da ke rabuwa biyu.

Alƙalin bayan kammala ‘yan rubuce-rubucen shi, sai ya bawa Barr. Cingam dama dan gabatar da nata tambayoyin ga Samuel.

Miƙewa ta yi ta ƙarasa inda yake.

“Mr. Samuel, shin ko za ka iya tuna lokacin da Sagir ya shigo ko yana tare da wani a motar?”

“A’a, ban kula ba gaskiya.”

“A sa’adda Sagir ya wuce ta gabanka, akwai wata magana ko da ta ɗaga hannu da ta shiga tsakaninku?”

Shiru ya yi yana nazari.

“Kai muke sauraro.”

“Ba mu yi magana ba, ko da na ce masa barka da shigowa hannu kawai ya ɗaga mini.”

“Kuma dama ɗabi’arsa kenan kowacce rana ya shigo ka gaishe shi hannu kawai yake ɗaga maka?”

“A’a, leƙowa yake ta tagar mota ya mayar mini da gaisuwata.”

“Sai kuma ranar bai yi hakan ba?”

“Kwarai kuwa.”

“Ko ka kalli fuskarsa? Ma’ana kun haɗa ido da shi?”

“A’a, kasancewar na riga na saba da shi, na kuma san motarsa ba na maida hankali gurin kallonsa.”

“A taƙaice dai ba ka ga fuskarsa ba?”

“Ban gani ba.”

“Ko za ka iya tuna da misalin ƙarfe 9:30 na ranar a ina kake? Kana bakin gate din makarantar ko kuwa ka yi wani gurin?”

Shiru ya ratsa ilahirin gurin, kamar ita kaɗai ce tambayar da ta rage a rufe shari’ar.

“Gaskiya ba zan iya tuna daidai lokacin da na bar bakin gate ba, sai dai wuraren ƙarfe Tara zuwa Goma Sha Ɗaya ina ta sintiri zuwa banɗaki sakamakon cikina da ke ta murɗa mini.”

“Kenan a tsakanin waɗannan lokutan idan wani ya shigo cikin makarantar ba za ka sani ba?”

“Ba zan sani ba gaskiya ba.”

“Ko za ka iya tuna mintuna nawa kake yi a bayan gidan.”

“Ina kaiwa kamar mintina biyar. Gudawa ne sosai ya kama ni.”

“Na gode!”

Ta furta tana baro gurin ta dawo gaban Alƙali.

“Ya Mai Shari’a idan aka yi duba da tambayoyin da Mr. Samuel ya amsa za a gane cewar shi kansa bai da tabbacin Sagir ya gani a wannan safiyar ko kuwa. Saboda ya saba gaisawa da Sagir, a ranar kuma bai gaisa da Sagir ba, bai ga fuskarsa ba. Motar kawai ya gani ta wuce. Ganin motarsa ba shi zai ba da tabbacin Sagir ya yi kisa ba. Wannan kuma shi zai kore hasashen Barr. Jagazi na cewar Sagir su biyu ne a motar. Wani zai iya ɗaukar motarsa ya yi amfani da ita dan ya ɗaura masa lefin. Haka idan aka yi la’akari da makarar da Sagir ya yi ranar wanda bai taɓa yin irinta ba, za a gane lalle akwai wata maƙarƙashiya da aka ƙulla masa dan ganin an ɗora masa lefin. Wani abin ɗaukar hankalin shi ne, yadda a tsakanin ƙarfe Tara da Goma Mr.Samuel bai yi zaman mintuna biyar a bakin gate ba. Ke nan Sagir zai iya shigowa a lokacin da shi kuma ya tafi banɗaki. Sai abu na gaba, tsakanin shigowar Sagir da mutuwar yaron mintuna Sittin da biyar ne (65), na’urar da ta gwada hakan ta nuna tun ƙarfe 8:25 yaron ya rasu. Sagir kuma ya shigo ne da misalin ƙarfe 9:30, idan aka lissafa za a ga mintuna Sittin da Biyar ne tsakaninsu. Ga wannan takardar da ke ɗauke da sakamakon gwajin…”
Ta furta tana miƙa takardun ga Alƙali.

…”Saboda haka nake roƙar kotu mai alfarma da ta yi duba da rashin yaronsa da wannan bawan Allah ya yi, da kuma wannan shaida da na kawo, ta ƙara mana lokaci yadda zai ishe mu mu gabatar da ainihin wanda yake da hannu cikin lamarin nan. Na gode”

Ta furta tana komawa mazauninta.

Alƙalin bayan ya gama nazarin takardar da ta miƙa masa.

“Kotu ta ba da dama da ɗaga wannan shari’ar zuwa ranar 22 ga watan 12 na wannan shekarar, sakamakon ko ke da Barr. Zubaida ta kawo da kuma rashin hujja kwarara da zai sa a yanke hukunci. Shi kuma za a ci gaba da tsaronsa.”

Abu guda ne ya zo zuciyarsa.

“Me ya sa Jagazi bai gabatar da shaidarsa ta yatsunsa ba?”

“Karka damu talala ne.”

Ya ji muryarta a sa’ilin da ake wucewa da shi ta gabanta zuwa motar da za ta mai da shi kurkukun ɗakinsa.

Da kallo ya bita yana tuna ko akwai ƙarfen da zai iya karya Rabbit Teeth ɗinta?

“Ka yi mamakin gani na a court ko?”

“Ba abin mamaki ba ne ai. Abin mamakin shi ne ta ya ya a cikin kwana biyu ki ka zo da wannan shaidar, ya a kai ma aka bar ki kika ga gawar alhalin Yaya ya ce mini wani irin tsaro aka ba ta, idan da kuma mun samu lawyer fa?”

“Na san ba za ku samu ba.”

Wani kallo ya bita da shi me yanayi da tuhuma.

“Eh ba za ku samu ba. A gari dai irin wannan ba za ku samu ba. Case ɗin ka ba kaɗan ba ne. Ba kowane lawyer ne zai saka kanshi ciki ba. Wani ko yana da niyya idan ya ji Barr. Jagazi ne na gwamnatin. Zai iya haƙura.”

Ta yi shiru tana lumshe masa idanuwa.

“Kasan Mr. Samuel C.I.D ɗinka yake mini?”

Ta furta tana kallon ɗan sandan da ke can baƙin ƙofar ɗakin. Sai dai hankalinsa baya kansu.

“To shi ne ya mini waya a ranar ya sanar da ni duk abinda ke faruwa. A sannan kuma na taho, sai dai ban je in da za ka ganni ba. Kai tsaye gurin da aka yi da gawar na nufa. Na sha wahala Sagir.” Ta yi shiru tana sake kishingiɗa a kujerar.

“Babu wani abin sha’awa a wannan labarin. Wanda zai yarda a yi min gwajin da nake buƙata a ba ni. Sai da na siyar masa da mutuncina tukunna…”

Ya gode Allah, ya ƙara gode masa da ba ruwa yake sha ba a lokacin da ta yi wannan furucin. Ya tabbata da babu abinda zai hana shi mummunar ƙwarewa.

“…Sai dai kuma hakan ya yi rana ai, tunda gashi a dalilin hujjar an ɗaga shari’ar taku zuwa lokacin da zai ishe ni yin kowane irin bincike…”

“…Oh, kar fa ka damu, na ga kana mini wani kallo. Ba shi ba ne na farko. Da can wani me walda ya taɓa yi mini fyaɗe, yanzu kuma na yi wannan ne saboda kai!”

“Wannan ganganci ne, ya za ki aikata zina ki ce kinyi ni saboda ni? Haka dama aka ce ku bi ta kowacce hanya dan kare mutum?”

Ya furta yana ɗora idanuwansa kanta. A karon farko da ya taɓa nazarin gajeruwar fuskarta ta mintina.

‘Ba lefi, ashe munin bai kai yadda ya za ta ba.’

Sai dai kuma ya ji kunya da sai yau da ta masa wani abu me muhimmanci a rayuwarsa ya fara ganin kyanta.

“Ina sonka har gobe Sagir, ba zan taɓa dainawa ba. A kan sonka idan da abinda ya fi zina ma zan iya aikatawa…”

Ta furta, yanayinta da kome na bayyana zahirin abinda ta faɗa haka yake a zuciyarta.

Allah ne shaida fuskarta ma baya son ƙara kallo, balle kuma ta buɗe bakinta me haƙoran Zomo ta ce tana sonsa. Dan haka kawai ya kauda kansa gefe.

“Ko zan rasa raina zan tsaya na ga ba a hukuntaka kan abinda ba ka yi ba. Alƙawari ne wannan tsakanina da kai!”

Ya ji zantukan, sun kuma shige shi, sai dai ya gaza daurewa ya ƙara dubanta.

“Abar wannan zancen mu yi abinda ke gabanmu, wanda shi ne ya kawo ni gunka yanzun. Ko ka kula da duk abinda Mr. Samuel ya faɗa babu ƙarya ciki. Tabbas da 7:30am ɗin an shiga makarantar a cikin motarka.”

“Ban gane ba, ta ya ya hakan zai faru. Ke kin sani ko Aboki ba ni da a garin nan balle na ba shi aro, sannan ya za a yi a ɗauki motata alhali mukullinta yana guri na asalima a gefen gadona na ajiye shi?”

“Shi ne abinda nake so ka tuna. Ka tabbata ka shiga gida da mukullin motar?”

“Idan ban shiga da shi ba da me na rufe motar kenan, da me na buɗe ƙofar gidana? Duk mukallaye na Suna jikin Key holder ɗaya.”

Ya furta yana jin kamar ya mangareta, tambayoyinta ƙoƙari suke su dawo masa da ciwon kan da ya fara sarara masa.

“Sagir dole fa za ka ba ni haɗin kai har mu gano gaskiyar lamarin. Dole ka rungumi haƙuri ka amsa mini duk abinda zan tambaye ka ba tare da ka raina tambayar ba. Saboda abinda ba ka za ce shi wani abu ba, ta yiwu shi ne zai kawo warwarar kome. Ka kalle ni a matsayin Barr. Zubaida Rabe, ba wai a matsayin Cingam ɗinka mai nace maka ba…”

Ta furta tana ɗauke kallonta daga gare shi, ba ta so ya ɓoye mata wani abu ko ya ya yake. Ta sani ko mai za ta furta masa ba zai gane muhimmancinsa a rayuwarta ba.

“…Yadda na faɗa maka hakan ne, wani ya yi amfani da motarka, wanin da ba mu san kowaye ba. Ka yi ƙoƙarin tuna wani abu ko ya ya yake, karka duba ƙanƙantarsa, ko mene ni zai iya yi mini amfani.”

Shiru ya yi yana nazari, idan har ba ciwon ƙwaƙwalwa take son haddasa masa ba bai ga abinda zai tuna ba. Yadda ya aje motarsa da mukullinsa da ya ajiye a gefen gadonsa bai ga wani abu da ya canja muhallinsu ba. Ba ƙaramin abu ba ne zai sa ya aje abu a taɓa masa ba tare da ya gane ba.

“A sa’adda ka tashi daga barci babu wani abu da ka ji canjin shi? Ka tuna dan Allah”.

“Kamar na ji ƙamshin da ba nawa ba?…”

Ya furta da tarin kokwanto, idanuwansa na kanta alamun ita yake tambaya. Sai dai kafin ta buɗe baki ya ɗora.

“…Tabbas haka ne na tuna. Na ji ƙamshin ɗakin ya sauya. Dan har sai da na raya a raina waya shafa turare mai mugun ƙarfi haka. Sai dai kasancewar tagar ɗakin na dubar bayan gidan ya sa na yi zaton ko wani ya gifta na ji ƙamshin.”

“Saboda ba a daɗe da shigowa gidan a ajiye mukullin motar ba, shi ya sa ƙamshin bai gushe ba. Idan kuma ban yi ƙarya ba, zan iya cewa mace ce ba na namiji ba.”

Ta furta da haƙiƙanin da ke nuna kamar wani ne ya ba ta labarin hakan, ba wai hasashe take yi ba.

“Da yake maza ba sa saka turare ko? A sanina turaren mata baya da ƙarfi. Zuby kar ki ɓata lokacinki anan. Ni mutum ne da ko ƙuda ya gifta ta gefena ina barci zan ji motsinsa, balle ace wani ya shigo ɗaki na har gefen gadona ya ɗau mukullina wai ban sani ba. Wannan ba zai taɓa yiwuwa ba. Ta ya ya ma kike ta magana kamar kina da tabbacinta?”

“Aikina kenan, ka manta? Ban ce dole macece ta yi kisan ba ko take da hannu kan kome, amma dai duk inda za a aje a dawo da mace aka yi amfani gurin shiga gidanka. Ko ka yi tunanin menene ya saka ka makara ranar? Ko dama ka saba tsawwala barci?”

“Abinda na gaza fahimta kenan ni ma, ba na tunanin na taɓa kaiwa wannan lokacin ina barci.”

“Da ka farka ba ka ji wani sauyi a jikinka ba?”

“Kamar ya?”

“Kamar ciwon jiki haka ko ka…”

“Ciwon kai! Tabbas na tashi da matsanancin ciwon kai, ya ilahi, har yanzu ina fama da irinsa. Ya akai duk ban tuna hakan ba? “

Ya furta yana goga gashin kansa a jikin garu. akwai alamun ya fara gajiya da maganar.

“Saboda ba ka ɗauke shi wani abu ba…”

“…Ko za ka iya tuna abubuwan da ka yi da wuraren da ka je kafin ranar?”

“Ba zan iya ba. Ki ƙyale Ni dan Allah! Tambayoyinki za su fasa mini kai!! Na gaji!!!”

Shiru ta yi tana nazarinsa, tabbas hasashenta ke daɗa fitowa zahiri. Gajeran murmushi ta yi tuna ko waye ya yi ƙoƙari, wautar kaɗan ce.

“Okay, to shi kenan bari na barka ka huta. Amma dan Allah kafin na dawo ka tabbata kana iya tuna abinda ka yi a shekara ba ma kwana ɗaya ba.”

“Hmm! Ba ki faɗi abin da za a biya ki ba. Kar kuma sai kin gama ki nemi abinda ba mu da shi, na ji Yaya ya ce da tsada kuke aikin.”

“Ba zan nemi abinda ba ka da shi ba. Asalima saboda shi na sadaukar da rayuwata kanka.”

“Menene?”

“Aurenka! Ina so ka aure ni bayan kome ya kammala, gaskiya ta bayyana. Shi ne ladar aikina.”

‘Amma ke ‘yar iska ce marar hankali.’

Abinda ya kamata ya furta mata kenan bayan ya kwantse ta da marin da zai saka ta ganin stars na mata gwalo, sai dai kuma ya gaza hakan. Da ya san za ta kai su da wannan maganar, da ya barta ta yi ta masa tambayoyinta daga nan har a tashi duniyar.

“Dan ALLAH Sagir ka ce za ka aure ni.”

Yawun bakinsa ya ji yana neman ƙafewa. Idan kana raye ba ka ƙare ganin abubuwan mamaki ba. Shi da baya da maraba da matacce shi ake fatar aura. Ba ta gani, ta makance. Tabbas dama can ba wadattaccen hankali gare ta ba, tana girma kuma hakan na daɗa bayyana, gashi yanzu ta ida zarewa a gabansa…

“Kodayake shi kenan ma. Ba sai ina maka magiya ba. Idan ka zaɓi mutuwarka akan zama da ni a yadda nake, gajera me gajeruwar fuska ai shi kenan. Amma fa ka sani, daɗin rayuwa shi ne ka amfaneta a lokacin da amfanin ya zo. Idan ba ka aure ni ba ka mutu ka huta. Ni kuma wani zan aura wanda baya kallona a wacce ta fi Wada tsayi da kaɗan, baya duba duk wani aibu na. Amma kai fa? Ka zo sillanka za ka koma a haka. Na tabbata ban da ni, babu wani kuma da zai tsaya maka a shari’ar nan. Shi kenan wanda ya aikata maka hakan ya ci riba. Za ka mutu ba tare da ka cika burinka na duniya ko guda ɗaya ba. “

“Wacce hujja gare ki da ke ba ki tabbacin za a ci nassarar lamarin.”

“Ba ni da kome a yanzun. Sai dai ka sani duk abinda nasa a gaba ba na faɗuwa, ka fi kowa sanin hakan. A jinina hakan yake da hakan kuma aka halicce ni.”

Shiru ya yi yana nazarin abin. Idan har za ta fidda shi daga wannan masifar bai ga hujjarsa na ƙin aurenta ba. Shi ba ma auren ba, damuwarsa karta haifa masa yara irinta. Yatsina fuska ya yi yana zagin zuciyar da ta fara tunanin har zai iya mu’amalar aure da Cingam ta haifa masa yara. Idan ta miƙe tsaye a cikinsa fa take tsayawa, idan ta hau dogon takalminta shi ne take isowa ƙirjinsa. Shi kam a rufa masa asiri saboda Allah ina shi ina ita.

‘Kai banza ne, da aka halatta auren sai aka wajabta saki ai. Ba sai ka cika alƙawarin ka aure ta ba, idan ya so ana ɗaurawa sai ka sake ta.’

Wata zuciyar ta zungure shi da hakan.

“Yanzu fa ba lokacin tunani ba ne kana ƙiyasta siffofina, abu a duhu ne fa Sagir, munin a fuskar kawai yake ba ka san abinda ke ɓoye a cikin ba. Ka amsa kawai eh ko a’a.”

“Na yarda.”

Ya samu bakinsa na furtawa. Sai dai kuma gaskiya ta faɗa masa, yanzu ba lokacin da zai tsaya tunanin kamanninta ba ne. Abinda ke gabansa ya shallake duk wani ƙawa ta duniya.

Washe masa fararen Rabbit Teeth ɗinta ta yi tana masa dariyar farin ciki.

“Na gode Sagir, na gode sosai. Ina ƙaunarka har raina.”

“Kin yi kyau!”
Ya samu bakinsa na furtawa bayan ya gama ƙarewa doguwar rigar da ta daɗa dunƙule kallo.

“Ko ƙarya ka faɗa, wannan wani abu ne da ba zan taɓa mantawa ba.”

Ta furta tana miƙewa ta ɗau jakarta.

“Zan dawo. Sai dai ina buƙatar ka ba ni mukullin gidanka ina buƙatar zuwa wani bincike.”

“Yana gurin Yaya, ki amsa.”

Daga haka ta ƙarasa ficewa daga gun. Shi kuma aka zo aka riƙe shi zuwa nasa ɗakin.

Ku saurare mu  a Babi Na Bakwai. 

<< Fadime 25Fadime 27 >>

2 thoughts on “Fadime 26”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×