Cira kumburarran idonsa sama ya yi yana watsawa ga tarin jama'ar da ke kallonsa, daga can tsakiya ya hangota tana hawaye. Abinda yake so ya faru ya farun, a tare suka haɗa ido ya aika mata da wani shu'umin murmushi kana ya buɗe baki.
Murmushin da ke saman fuskar Zuby ya tarwatse yana maye gurbi da ɓacin rai a lokacin da kunnuwanta suka zuƙo mata maganar Jabiru na bada shaidar babu Fati cikin lamarin, daga Ibraheem sai Linda suka sani. Idanuwansa da ke kafe wani gun, da ɓoyayyen murmushin da ke maƙale a gefen. . .