Skip to content
Part 35 of 37 in the Series Fadime by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Cira kumburarran idonsa sama ya yi yana watsawa ga tarin jama’ar da ke kallonsa, daga can tsakiya ya hangota tana hawaye. Abinda yake so ya faru ya farun, a tare suka haɗa ido ya aika mata da wani shu’umin murmushi kana ya buɗe baki.

Murmushin da ke saman fuskar Zuby ya tarwatse yana maye gurbi da ɓacin rai a lokacin da kunnuwanta suka zuƙo mata maganar Jabiru na bada shaidar babu Fati cikin lamarin, daga Ibraheem sai Linda suka sani. Idanuwansa da ke kafe wani gun, da ɓoyayyen murmushin da ke maƙale a gefen bakinsa ta bi da kallo da nata idon suka zarce da ita kan Faɗime da hannunta ke kan ƙirji, ido a zare cikin hawaye. Wato ita ya kafe da kallo. Da ƙyar ta haɗiyi wani yawu muƙut! Ta duƙa ta ɗauki bironta da ya zame daga hannunta. A sanyaye ta gyara zamanta kan kujerar da ke kusa da ta Jagazi ba tare da ta ƙara kallon sashin da Jabiru yake ba. Kome kuma ya ƙare, sai dai burinta guda ne Sagir ya zama ɗan halak, ya kuma yarda uwar ɗan nasa tana da masaniyar kome, ta yi ni domin ramuwa. Tana da damar da za ta na ce kan lamarin har ta fitar da shaidar masaniyarta. Sai dai fa sai ta cika gwangwanin kwankwalati ashirin da ruwan gumin goshinta kafin a yarje mata, Sagir kam ba ma tada wani fata kansa kan batun, ta sani da wahala idan ma yana da wannan lokacin. To amma da ta saurari ɗayar zuciyar tata sai gata tana taɓe baki tana girgiza kai duk a lokaci guda. Babu ruwanta! Kamar yadda aka tunatar da ita. Tunda ta samu cikar burinta me zai dame ta da wata Fati, me zai sa ta damu kanta da ganin sai ta tafi prison alhalin tasan wata guda ya yi yawa tana ɗakin Sagir. Tasan ko da wannan aka bar Fati, ta gama da ita har abada. A hankali ta sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya.

Sau uku ta ja addu’ar neman tsari ta haɗa da Suratul Falaqta tattofe a hannuwanta da ke rungume a ƙirjinta. Gabaɗaya nutsuwa ta gagareta saitawa musamman idan ta haɗa ido da shi taga ita yake kallo. Ta tabbata wani baƙin sharrin yake nemanta da shi shi ya sa ya ɓoye lefinta. A dukkan tunaninta ta rasa gano dalilin da yasa Jabiru yin ƙarya saboda ita. Ita dai bata ga wani abin alheri da ya taɓa shiga tsakaninsu ba. Babu abinda ke ɗaga mata hankali sai murmushin da yake ta auno mata da sun haɗa ido. Hankalinta ya gaza kwanciya duk da tasan cewa Jabiru ya shiga hannu ke nan, ba ta jin yana da damar kuɓuta. Kisa ne ya hau kanshi, kisa kuwa na nan take. A lokacin ne ta ji nutsuwar sake ɗagowa saitin da yake, sai dai babu shi gurin, har an bada umarnin a fita da shi ba tare da ta ankara ba. A gaggauce ta juya saitin ƙofar fitar, lokacin sun buɗe za su fita shi kuma ya waigo suka sake haɗa ido a karo na barkatai. Yanzun fuskar tasa a ɗinke take da ɓacin rai bayyananne, sai dai bakinsa da ke motsi ta kalla ta fahimci kalmomin da ya furta mata. I Love You Forever And Ever. Ta juyo da sauri jin zuciyarta ta buga da sunan Liman, tabbas Mamuda ya tabbatar mata Jabiru ya kashe mata su Liman. A yanzu kuma ga shi zai bi bayansa ta hanyar da bai za ta ba. Allah ke nan! Mai yin yarda ya so da bayinsa. A cikin wannan tunanin nata ta tsinkayi maganar Alƙali na ƙarasa yanke hukuncin. Ya jaddada ma su Linda da su biya Sagir Maƙudan miliyoyin da ya nema. Sa’annan ya musu rangwame daga shekaru 14 zuwa 10 sakamakon neman afuwar da suka dinga yi. 

Runtse idanuwanta ta yi da ƙarfi sa’ilin da wasu hawayen masu ɗumi suka sauka a silin kuncinta, tana jin ɗanɗanonsu har a cikin bakinta zuwa maƙogwaronta a hakan ta ɗora tafukan hannayenta a fuskarta. Cikin shessheƙar take jin ihun Linda da ke ƙara fasa zuciyarta. Tunananinta ya ruga cikin ƙwaƙwalwarta yana tuna mata da ita Karfa Ce Mai Baƙar Ƙafa duk wanda ya kutso rayuwarta sai ya ƙare tasa rayuwar a wani mummunan yanayi. Yau dai ga Inda rayuwa ta kawo su ita da Yayanta da shi ne mutum na uku da ya fara nuna mata ƙauna a bayan mahaifanta biyu, ya haska mata duhun jahilcin da ya yanyameta. Har gashi a yau ya zaɓi da ya tafi prison ya rabu mahaifiyarsa da shi kaɗai gare ta, ya rabu da kowane irin jindadi domin kawai ita ta ji daɗin. Tunaninta ya zarce a tun ranar da rabon haihuwarta ya hana Uwale samun Mahaifinta. Ke nan ba ita ta kashe mata iyaye ba. Ita da rabon ya sanya kome ya farun ke da alhakin kisan. Ta tuna ranar da Sagir ya fara shigowa rayuwarta. Ke nan ba haka kawai ya ƙi ta a karan farko ba, ya ji a jikinsa cewar ita ba Alheri ba ce gare su. Ta tuna ranar da ta sunkuya a ƙofar Liman tana naƙuda ya tallafeta zuwa cikin gidansu. Me ya sa duk da ake kawo harin bai taɓa kusantarsu ba sai sa’adda take cikin rayuwarsu? Ta tuna Mahmuda! A lokacin nan da yake cewa; Jabiru mu ɗauke ta mun samu ganimar da za mu ƙarawa Imam!. Ta tuna abin da ya fara furtawa Imam domin cetonta. Ina son waccar mai yaron zan aura. Ƙarshe a gaban idonta cikin kunnuwanta aka kashe shi. Ta tuna Linda, a ranar da ta ɗau abincinta ta miƙawa Abbati cikin ƙauna mabayyaniya, ƙarshe yau a dalilinta gata a prison, ta tuna, ta tuna abubuwa da yawa da duk sanadinta ya faru, cikin tafasar zuciya da take ji kamar ta cire ta ta bawa Kare ya cinye. “Ko menene kuskurena da haka ke faruwa da ni?”

Ba ta san a fili ta yi tambayar ba sai da ta ji muryar Babban Mutum a saitin kunnenta.

“Kuskurenki ɗaya ne kin manta cewar ke musulma ce. A ƙa’idar shari’a shi ne idan mace ta haihu da Namiji ba ta hanyar aure ba, to fa abinda aka samu nata ne ita kaɗai, hatta gadon uban baya da. Babu kuma kotun da za ta ƙwace abinda aka samun daga hannun uwar ta danƙawa uban wai dan yana so. Babu hakan a Shari’a! Yaro ko Yarinya nata ne ita kaɗai. Idan da kin yi haƙuri Sagir ko da yana son karɓar yaron nan babu mai barinsa. Kai ko ni da baki ɗauke ni a bakin kome ba ba zan taɓa goya masa baya ba saboda ke. Ina jin kin manta baya. Nasan wannan ne dalilin ya saka ki yin hakan. Ba ki yi tunani ba ko kaɗan. Kin kuma yi yarintar da bata gyaruwa. Kinsan menene abu ma fi ciwo a cikin lamarin nan? Shi ne ranar da Hajiya ta tako da ƙafarta ƙofar gidanki domin ta roƙe ki da ki yafewa Sagir ta kuma yi miki ta’aziyar ɗan da kika ɓoye amma kuma kika ce ace kin yi tafiya. Kinsan ta ya ya ta iya zuwa? Kinsan Ƙarin Ruwan da Ledojin Jinin da ta shanye? Ba ki san na ga giftawarki ta window ba ko? Hajiya fa Fati, ita kika ce a cewa baki nan, Hajiya? Shin ta ya ya za ta manta wannan?”

Girgiza kanta take cikin hawayen da bata san ya za ta hana zubarsu ba. So take ta furta masa dalilinta amma bakinta ya yi nauyin da ta gaza furta kome sai kaɗa kai da take.

“Na tafi!”

A hakan ya juya ya fice kamar yadda sauran jama’ar kotun suke ficewa. An fita da Linda da Yaya ba tare da ta ankara ba. Abbati ma babu shi, ta sani kuma Ubansa ya tafi da shi. Ba tada kwarin gwiwar miƙewa ba kuma tada ikon kallonsu. Ita A Karan Kanta tsoron kanta take ji da kunyar kanta. Dan haka ta ƙara jingina jikin kujeran tana girgiza kanta da ƙafafuwanta. A sannan ne ta ji ta dafa wata ‘yar takardar da ba ta san wanda ya aje kusa da ita ba. Da sauri ta ɗauka ta warware.

JWBilisco.

Na san na tafi a sa’adda saƙon zai riske ki. Magana guda ce nake son faɗa miki. Ni Jabiru ban nufarki da sharri a yau. Na yi ne saboda kar ace tun da na zo duniya ban aikata wani abin Alheri ba. Haka na yi ne dan na farantawa marigayin Abokina rai. Ina roƙarki da ko da za ki bada mummunan labarina, to ki faɗi wannan guda ɗayan ma. Kar ki manta har abada ni mai son ki ne. Ina Sonki Fati, ina son ki har gaban gobe!

Lumshe idanuwanta da ruwan hawaye ya gaza tsayawa ta yi tana cukurkuɗe takardar tamkar ta tsiren da ya kwana goma ƙasan gado. A can wani saƙo na zuciyarta take jin ba za ta ƙara bawa wata halittar damar kusanto rayuwarta ba! Da wannan tunanin ta idasa sumewa.

*****

B ayab Sati Shida

Awanninta biyu ke nan durƙushe a kan gwiwowinta a dandanyar Tayil ɗin falon tana kallon saitin da Hajiya take zaune tana jan carbi. Akwai alamun yau ma ba za ta kula ba ta amshi roƙonta. Sai dai fa rantsewa ta yi da abinda zai kashe ta yau ɗin ba za ta gaji ta tafi ba. Idan kwana Hajiya za ta yi ba ta yi mata magana ba, to ita ma ta shirya kwana a kan gwiwowinta tana jiranta. Ta kuma gaji, fushinta ya gama yi mata duk wata illa da zai yi, ya cinye duk wata tsoka ta jikinta sai ƙashi da ko ruwa aka zuba a ramin wuyanta babu abinda zai hana shi tsayawa. Ko da dai ta sha jinyar da har sai da ta fidda rai da rayuwar duka. Sati huɗu baya i wannan lokacin tana kwance gadon Asibiti tana karɓar Allurarai da ƙarin ruwa. Wata moƙaociyarta da take ƙawa ga Linda ita ce ta yi jinyarta har ta samu sauƙi. Da fitowarta kuma ta yi ƙoƙarin rabuwa da Kamfaninta na Lagos ta biya kotu abinda ta nema ga Sagir.

A bayan nan ne kuma hankalinta ya karkato kan Hajiya da take ta kira tun tana gadon Asibiti ta ƙi ɗauka har Babban Mutum. Dole ta sakata tattara ina ta ina ta ta yo Kano.

A karon farko ta sha idan ta haɗu da Hajiyar za ta ce mata ‘ashe kina da sauran kunya?’ Sai dai ga mamakinta ko kallon inda take ba ta yi ba, har ta ƙaraci neman gafara tana kuka, ƙarshe ma ta bar mata falon. A kaf! Gidanma babu wanda ya kula ta sai Abbati, shi ma rabin hankalinsa na ga Uncle Slim da ke ta shirye-shiryen auren da bata san wacece matar ba.

To fa tun daga lokacin ta dage da zuwa sai dai kullum a saɓule take fitowa, Hajiyar ba ta ko kallonta balle tasa ran za ta amsa mata ko da gaisuwarta ne. Sau ɗaya ne ma Babban Mutum ya faɗa mata maganar da ajikinta ta ji shi ma jikinsa ya yi sanyi. Ya ce mata ta daina musu zirga-zirga, idan ɗanta take son ɗauka ta ɗauki abinta ta tafi, amma kar ta sace shi ta ƙalawa Hajiya ta kashe mata yaro. Maganar ta dake ta da har ya kaita da buga kanta garu tana fasa ihu ko za ta ji daɗi. Rayuwar ta mata zafi ta ko’ina. Sai dai hakan bai sa washegari ta fasa zuwa ba. Ci gaba ta yi da zuwan har zuwa yau da ta cika sati uku cif! Ta kuma ƙuduri niyyar babu inda za ta matsa har sai ta mata magana, kai ita koda zagi ne, tana so har ranta.

Har Maghriba da Hajiyar ta ƙara fitowa tana nan sunkuye a inda ta barta. Hawayen sun kafe sai sauke ajiyar zuciya take yi cikin tafasar rai. Tsai! Ta yi tana kallonta, tana jin tausayinta na ratsata a karo na barkatai. Faɗime yarinya ce, dole ta mata uzuri. Sai dai fa akwai dalilinta na yin hakan. Takowa ta yi a hankali ta zauna a kujerar saitinta tana gyaran murya. Ɗago da kanta ta yi tana kafeta da rinannun idanuwanta da suka daɗe da shigewa lungu. Tana tuna rabonta da isasshen abinci, tun kafin ta gane Uncle Slim shi ne Sagir.

“Ta so ki dawo nan.”

A karo na farko cikin sati uku da ta mata magana.

Kasa motsa ƙafarta ta yi sakamakon tsamin da ta yi. Ganin ba za ta iya motsawa ba ya sakata rarrafowa ta zauna gefen ƙafarta.

“Kinsan kin yi kuskure shi ya sa kike so na yafe miki ko?”

Kaɗa kanta ta yi alamun eh, hawayen har sun fara sauka.

“To zan yafe miki. Amma idan ina da mutuncin da za ki damu da ɓacin raina har tsawon sati shida. Idan ina da sauran darajar uwa a cikin idanuwanki. Fati, ina roƙarki da ki manta baya, ki auri Sagiru!”

‘Yar fara’ar da ta fara bayyana saman fuskarta a take ta ɓace.

‘Shi ke nan! Abinda ta guda ɗin, har wasu suka tafi prison saboda shi, gashi ya farun cikin ƙanƙanin lokaci.’

<< Fadime 34Fadime 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×