"Ba fa wani abu ba ne, idan ba kya sonsa ba kya san wata alaƙa da za ta ƙara haɗa ki da shi, ki faɗa mini zan fahimce ki. Ba ni da ikon tursasaki dan ki rayu da jinina."
Wasu maganganun Hajiyar suka dawo da ita daga zancen zucinta.
'Wai idan bata sonsa ta faɗa mata?' Ita har ina ta yi wannan isar da za ta dubi tsabar idonta ta ce bata son jininta. Girgiza kanta ta yi da sauri tana danne wani kuka da ke taso mata tun daga ƙasan ranta, ta daɗe bata. . .