Skip to content
Part 36 of 37 in the Series Fadime by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

“Ba fa wani abu ba ne, idan ba kya sonsa ba kya san wata alaƙa da za ta ƙara haɗa ki da shi, ki faɗa mini zan fahimce ki. Ba ni da ikon tursasaki dan ki rayu da jinina.”

Wasu maganganun Hajiyar suka dawo da ita daga zancen zucinta.

‘Wai idan bata sonsa ta faɗa mata?’ Ita har ina ta yi wannan isar da za ta dubi tsabar idonta ta ce bata son jininta. Girgiza kanta ta yi da sauri tana danne wani kuka da ke taso mata tun daga ƙasan ranta, ta daɗe bata ji wutar ƙiyayyar Sagir irin yau ba, da ƙyar ta buɗe baki cikin sanyi ta ce, “Ban isa ba Hajiya, ban isa ba wallahi, ko Ilu Maigadi kika ban umarnin na aura zan karɓa hannu bibbiyu balle kuma wanda yake jininki. Na yarda da duk abinda kike so, to amma na ga ai yana…”

Sai kuma ta yi shiru tana haɗiye wani maƙoƙo da ya tsaya mata a maƙoshi. Ba za ta ma iya furta abinda take son fadar ba.

“…Kin ga yana shirye-shiryen aure ko? Babu damuwa ai, da nakin zai haɗa ya yi lokaci guda. ‘Yar uwar taki ba tada wata matsala kin ma santa, wannan lauyar ce da ta tsaya masa a shari’arku.”

A firgice ta ɗago tana kallon Hajiyar jin kamar ba sosai ta ji ba, sai dai Hajiyar ba ta ma kalleta ba hankalinta ya koma ga Sagir da ya shigo ta yafito shi ya taho gurinsu.

“Na gama yanke shawarar aurenka da Fati, gata nan ta amince ita ma. Dan haka ina so ka haɗa da wannan ɗin duk ayi lokaci guda, kai kuma ka zama mai riƙe amana da adalci a tsakaninsu, ka sake ka zalunci yarinyar nan ko bayan raina ban yafe maka ba! Ba dan kowa na yi haɗin nan ba sai dan Abbati, ba na so ya tashi ana sheganta shi dan har yanzu Bahaushe bai san cikakkiyar ma’anar shege ba. Bar ganin wai yana gabanka, hakan ba zai hana a sheganta shi ba ayi masa gorin Uba, to gwara kuyi auren ku rayu da shi a tare. Allah yasa Albarka ya kaɗe duk wata fitina.”

Ba yabo ba fallasa ya amsawa Hajiyar da Amin. Ta gefen ido yake satar kallonta ganin yadda ta sunkwi da kai can ƙasa, idan ma ba idonsa ke masa gizo ba ya kula da ɗigar hawaye a hannunta da ta aje ƙasan. Taɓe baki ya yi yana jin ba daɗi a ransa.

Ba ta kalli sashen da yake ba ta miƙe bayan ta yiwa Hajiyar sallama. Juyawa ta yi hannunta a baki tana jin yadda ruwan hawaye ke ambaliya a fuskarta, ba abinda ke ƙara mata ciwo sai jin Baristar da ta tsana ce wai kishiyarta, ita kuwa me ta yiwa zaman duniya ne a rayuwarta? Ba ta damu ta goge fuskarta ba haka ta fice, ƙarshen abinda kunnuwanta suka jiyo mata shi ne Hajiyar da take bawa Sagir umarnin su shirya cikin satin dan zuwa garinsu Fatin neman aurenta.

*****

Ba ta yi zaton akwai wata ƙaddarar da za ta sake kawo ta ko da hanyar garin Bebeji ba sai yanzun da take zaune a bayan mota tana ganin Babban Mutum na gaisawa da Malam. Har ya kammala yi masa bayani Faɗime ta gaza fitowa sai ma ƙanƙame jikinta da tayi a cikin motar komai yana sake dawo mata cikin kwakwalwarta kamar a yanzu ake haska film ɗin. Domin ta ɗauki rayuwarta kamar shirin film din da a yanzu aka kawo ƙarshensa.

Malam da kansa ya iso har gurin motar ya buɗe cike da ƙaunar ya sake haɗa idanu da ‘yarsa ko da kuwa wannan ne haɗuwar da za su yi na ƙarshe. Fitowa tayi kanta a ƙasa kawai ta durƙushe a gabansa tana shessheƙar kuka.

Daga hannayensa sama ya yi yana godiya ga Allah. Da ƙyar Faɗime ta amince ta shigo cikin gidansu da ta daɗe da goge sunanta daga cikin Ahalin gidan.

Hansai ta gani gabaɗaya ta fita kamanninta sun sauya saboda tsabar wahala. Zuwa tayi da nufin ta riƙe Faɗime malam ya daka mata tsawa, “Kul! Kada inji kuma kada in gani. A ina kika taba saninta da zaki taɓa ta?”

Duban su Malam ya yi da dukkansu suke duban ko’ina cike da mamaki, ya fara kora masu bayanin da ko zama bai bari sun yi ba, “Kun gan su nan babu abinda ba su yi mini ba, da raina kuma da lafiyata. Da Allah ya tashi kawo sakayya, sai Uwale ta dinga abubuwa kamar mara hankali, tana surutai. In taƙaita maku har kashi ci take yi da fitsarinta. To dama abinda yasa ban sake ta ta bi duniya ba, saboda ina jiran ranar da za ki dawo gare ni. Alhamdulillah! Ku zo mu je ku ganta.”

Suna isa inda Uwale ke ta tsince-tsincenta, a gabanta da wani mushen ɓera tana zungurinsa da tsinke, ta ɗago a matuƙar razane tana kallonsu. A take Faɗime ta ji wani irin ciwon kai har sai da ta dafe kan, ta sake zura idanunta a cikin na Uwale.

A zabure tayo kanta wanda hakan yasa ta ɓoye a bayan Sagir cikin rawar jiki. Uwale ta nuna Sagir da hannu, “lahhhhh Kai ne? Lah wallahi kai ne yaron Malam ya nuna mini fuskarka a cikin kindirmo na maka fitsarin da za ka dinga jin sha’awar Faɗime. Hegen gari, ina yara goman da aka ce mini Ka haifa da ita, kai! Kai!! Na tuna, Tsidugu ya ce mini duk randa na haɗu da kai zan mutu!” Ta furta a tsawace tana yin zaman daɓaro a ƙasa hannunta ɗaya bisa kanta.

“Waiiiiiiiiiii ni Allah na shiga uku ni Uwale. Shege Malam duk kai ka cuce ni, ban taɓa sonka ba, Bashari nake so kai da Falmata kuka shiga tsakani.” Sai kuma ta ƙara rushewa da ihu tana fusgar gashin hammatarta da ya zama kamar sheƙar Ungulu.

“Waiiiiiiiiiii ni Allah na shiga uku Ni ‘yar Malam! Da hannuna na babbaka Bashari da Matarsa na cusa maku duk wata masifa da kuka tsinci kanku a ciki. Shi ke nan zan mutu! Wuta zan afka!! Wutar Mai Shayi.” Ta dire zancen tana zabura a guje tayi hanyar waje cikin kwantsama ihu. Ba Babban Mutum ba, harta Sagir sai da ya ji kwalla cikin idanuwansa. Faɗime kam a hankali ta sulale ta zauna tana fidda numfarfashin kaɗuwa. Malam kuwa goge hawayensa yana yiwa Uwale Allah ya isa.

Bayan duk sun gama jaje, cikin mutuntawa Babban Mutum ya bawa Malam labarin duk abinda ya faru tun daga ranar da suka fara haɗuwa da ita, da duk yadda suka yi da Hajiya. Hakan ya yi masa daɗi ya yi ta doguwar Addu’a jin aurenta zasu yi, haka ya gayawa Babban Mutum a gayawa Hajiya Faɗime ‘yar ta ce, wuƙa da nama duk yana hannunta. Don haka shi nasa kawai a gayyace shi ranar biki ya zo.

Babban Mutum ya ji daɗin irin karamcin da Malam ya nuna masu. Shi da Sagir suka miƙe suka ba Faɗime wuri da mahaifinta don samun damar tattaunawa. Sosai yake sake yi mata nasiha da jaje, daga ƙarshe ya ce mata Sagir amana ne a gurinta wanda shi da kansa ya danƙa mata, ta kuma yafe ta manta kome, ta dai ji da kunnenta abinda ya yi silar koman, ke nan su ya kamata a bawa haƙuri.

Haka suka baro Bebeji jikin Faɗime duk a sanayaye. Cikin dabara take ta sharar kwalla. Duk abinda take yi Sagir yana kula da ita sai dai ba shi da hurumin yin magana da ita bare har rarrashi ya shiga tsakaninsu.

*****

Sagir ne tsaye da misalin ƙarfe biyun dare yana ta kaiwa da komowa. Shi har ga Allah baya jin ko ɗigon son Zuby a cikin ransa. Ta ya ya ma zai iya rayuwa da ita, anya babu zalunci a aurenta, zai ma iya adalci tsakaninsu? Ya sani Faɗime ta ci zarafinsa akan laifin da ba shi da masaniyar dalilin aikata shi sai yanzu da Uwale take gaya masu ita ta aikata hakan. Ya kuma kasa cire son Faɗime a ransa, soyayyarta ba kaɗan take wahalar da shi ba, daurewa kawai yake yi, musamman a yanzun da yake ganinta cikin gidansu. A fili yake magana. “Ya zama dole na auri Zuby ko don in samu damar rama duk abinda Fati ta yi mini. Ina da tabbacin ta wannan hanyar ne kawai zan sami kanta.” Sai dai yana da buƙatar yaje ya gayawa Faɗime maganar da idan ma tana tunanin yana sonta ne to gara ta daina, ba ya so ta sake samun wata damar kan shi. Da wannan tunanin ya fito daga ɗakin.

Ga mamakinsa ƙofar ɗakinta a buɗe yake. Don haka ya tura kansa ciki. A tsaye ya sameta ta ƙurawa taga idanu kamar me ƙirga wasu abubuwa. Da alama ta yi zurfi a cikin tunanin da take yi idan aka yi la’akari da yadda ba ta san da shigowar shi ba. Motsi ta ji hakan yasa ta juyo a ɗan firgice. A karo na farko da taga ya mata wani irin ƙwarjini, dan haka ta kalli gefensa, “Lafiya ka shigo mini ɗaki?”

Ɗaure fuska ya yi kamar wanda bai taɓa dariya ba.

“Eh ga ɗan iska mai danne mata kin gani dole ki tambayi ba’asi.”

Kanta ta yi da ƙasa tana jin ba daɗi cikin ranta. Ba haka take nufi ba sam! Amma me za ta ce masa?
“To Lafiya ƙalau, na zo in gaya maki ne zan bi umarnin Hajiya ne wajen aurenki ba wai umarnin zuciyata ba. Kin kasa yarda da ƙaddara kina ganin kamar Sagir yafi kowa laifi da har ya kasance da ke, kika sami ciki. Ashe daga zuri’arku ce, kuma saboda ke aka sa na aikata abinda har gobe na gaza yafewa kaina. Haka na neme ki na baki haƙuri, a ƙarshe kika ƙi duban tubana kika tozartani a idon duniya. Ta ya ya zan manta wannan? Ta ya ya ma zan so ki ina kallon ki a hakan? Na godewa Allah da Hajiya ta amince mini in auri mata biyu a rana ɗaya, da ban san ya zan yi da ke ba. Ina fatan zaki shirya zama da Amaryarki mai kirki Zuby.”

Ba ƙaramin dauriya Faɗime tayi ba, wajen ganin ta hana hawayen idanunta zuba. Ɗaci take ji a maƙogwaronta, ga wani maƙoƙo da ya tsaya mata. Ta rasa ta yadda za ta daurewa duk wata damuwarsa da ke addabarta bare ta iya amayo masa abinda ke cikinta. Da ƙyar ta iya tattaro kalaman da suka rage mata ta dage ta fitar masa cikin sanyi. “Duk ba matsalata ba ce wannan, ni ma ban damu da ka so ni ba. Damuwata ɗaya ce kada ka haɗa ni gida ɗaya da ita…Dan Allah…”

Yadda taga idanuwansa sun ƙara girma ya sakata ankara da wautar da ta yi, kamar fa ta gwada tana kishin zama gida guda da kishiya ne. Wai har yaushe ma wannan ya zama damuwarta? Girgiza kai ta yi ta juya a sanyaye tana kallon tagar, a hankali tasa ƙaramin yatsanta ta ɗauke hawayen idonta.

Ta yi matuƙar bashi tausayi, zai so a irin wannan yanayin tana rungume ne a ƙirjinsa yana gaya mata kalamai masu daɗaɗa rai. Sai dai baya jin zai yi saurin bayar da kansa da wuri, dole ya jure tauna tsakuwa dan aya ta ji tsoro. Dan haka ya hau girgiza kai yana ƙarewa bayanta kallonta. “Ba ni da sha’awar raba Matana. Ki shirya zama wuri ɗaya da ita. Ki huta lafiya.”

Daga haka ya juya tana jin ƙarfin takunsa cikin kunnuwanta. Kwanciya tayi a bisa gadonta tana zubda hawaye masu raɗaɗi. Ta rasa dalilin da take jin zuciyarta kamar ta tsage saboda azabar zafi. Wani yanayi da akan Mamuda kawai ta san shi, take ji akan Sagir a tun ranar da suka je Bebeji. Za ta rantse da Allah ko Mamuda ba ta ji shaƙuwa da shi ba yadda take ji a kan Sagir, ga wata kunya da ke ɗawaniya da ita a duk sa’adda ta yi tozali da shi, ta sani Allah ne ya kamata ya gwada mata duk tsananin ƙiyayya kar ka tsanantata.

A kwanakin nan ƙaramin hauka ne kawai ba ta yi ba kan tunaninsa. Abin kamar tsafi, har tsoro take ji ko dai Sagir ya kai sunanta ne an rufe a cikin Minjaye. Hatta wannan nacin tsayawa a jikin taga domin shi take yi. Abinda Ya fi damunta da ta riga ta sani sai dai ta shirya zaman haƙuri cikin gidansa, amma tuni Zuby ta ɗauke mata Sagir, gashi a yanzu da bakinsa ya tabbatar mata bai sonta. Ita ma kam za ta jure za ta yi duk ƙoƙarin wurin ganin ya ɓoye abinda ke ranta game da shi. Hawaye masu ɗumi suka sake wanke mata fuska tuna kalamansa na ƙarshe. Tana da buƙatar ganawa da Mahallicinta a irin wannan lokacin domin neman sauƙin lamarinta.

<< Fadime 35Fadime 37 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×