ƊAN ZAKI
Zuciya na ji na da tasiri
Shi ko hankali gwanin tsari
Yin ilimi ko ya zamo jari
Sai ka gujewa rayuwar sharri.
Mai tafiya a kan gada ta zare
Ko ka taka ‘yar ƙaya jure.
Ɗan ɗaga kai ka kalli Ɗan Zaki
Ya riƙi rayuwa cikin mulki
Sam baya kula da ɗan doki
Baya ƙoƙari wajen aiki.
Sai dai yai kururuwar gyare
Kana ya hau saman tudu ya dire.
Yunwa ga shi ta shigo jeji
Ta sa rakuma suna gunji
Du sun tarwatse cikin daji
Ka ce sun yi tozalin yaji.
Sai kuka suke a shusshure
Ɓauna har da Zabuwa da Kare.
Shi goganka na cikin daula
Sai kora ya ke da bulala
Ya manta da du faɗin Allah
Baya ambatonsa ma ƙila.
Wasu sun fara yin gudu da dare
Kan junansu yanzu yai ware.
Shi kuwa Ɗan Dila ya same shi
Ya yi magana yana batun kishi
Sai Zaki ya sa a kamo shi
Sarƙa ce, ya ce a ɗauro shi.
Zai faɗi gaskiya a jejjere
Saura za su haɗa kai cure.
Baya so su san malafarsa
Sai ya kashe shi don ya numfasa
‘Yan maganar cikin su sun kasa
Kar su ma a sa su bayansa.
Zai binne su ne a nan tare
Don haka bakunansu na ɗaure.
Can gefe ana ta yaƙar su
Ɗai-ɗai-ɗai ake ta satar su
Wai sai sun biya fansarsu
Sannan za’a ‘yanta sauransu.
Wannan rayuwar akwai ƙware
Kiwon lafiyarsu an gutsure.
Wai sai yaushe za su san ƴanci?
Yaushe za su sami sassauci?
Yaushe za su bar cikin ƙunci?
Su ma dai su dinga kalaci.
Kar hakurinsu dai ya ƙaƙƙare
Ko wataran a ji su sun tubure.
To yau dai darensu ya waye
Ba na so su fara tawaye
Kurayen ciki da giwaye
Sun ja hankali da a kiyaye.
Kukan kurciya ku yi saurare
Na faɗi gaskiyar da na ƙudire.
Nomal