Skip to content
Part 18 of 30 in the Series Falsafa by Haiman Raees

TANTAMA 

 1. 

Allah ga annoba ta cika duniya,

Uwa da ‘ya yau su ke ƙiyayya,

Ɗa da uba ne suke ta hamayya,

‘Yan’uwan jini su na ta jayayya. 

 2. 

Ba maza ba mata a fagen gulma, 

Kowa kuɗi kawai yake nema, 

Wannan shi ya sa ake fama, 

Da ta’addanci har a fagen noma. 

 3. 

Ina masoyi da ke yin soyayya, 

Da maƙiyi mai fama da ƙiyayya, 

Basarake da ɗa na demokuraɗiyya, 

Da ma su na tarihin mulukiyya. 

 4. 

Wanda duk ya tsaya ya yi duba, 

Matsalolin dai ba za su ƙirgu ba, 

Ba wai birni ko kuma ƙauye ba, 

Ba manya kau ko yaran ba. 

 5. 

Cin amana ta zaga gidan kowa, 

Mutane yanzu kowa rowa, 

Wani da ya ba ka kofin ruwa, 

Ya gwammace ka yi mutuwa. 

 6. 

Asiri da tsafi ya yi tasiri, 

A zukata masu rashin tsari, 

Mun manta da neman tsari 

Safe da yamma azkari. 

 7. 

Allahu ka kawo sauƙi,

A ƙasarmu ka kawo sauyi,

Albarka sunƙi-sunƙi,

Ko za mu ɗan ji sanyi. 

<< Falsafa 17Falsafa 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×