TANTAMA
1.
Allah ga annoba ta cika duniya,
Uwa da 'ya yau su ke ƙiyayya,
Ɗa da uba ne suke ta hamayya,
'Yan'uwan jini su na ta jayayya.
2.
Ba maza ba mata a fagen gulma,
Kowa kuɗi kawai yake nema,
Wannan shi ya sa ake fama,
Da ta'addanci har a fagen noma. . . .