Skip to content
Part 2 of 28 in the Series Falsafa by Haiman Raees

AMANAR SO 

Amana a soyayya, 

Lamari ne mai ƙarfi. 

Ƙarfinsa ya fi na dutse, 

Balle a haɗa shi da ƙaya ta kifi. 

Na so a ce a soyayya, 

Na ga na zamo laɗifi. 

Amma sai ga shi yau, 

Ni ke neman tallafi. 

Na riƙe ki a zuciyata, 

Ba na kula wasu ‘yan mata. 

Har aikina na bari, 

Dominki Sahibata. 

‘Yan uwana har abokai, 

Saboda ke kawai gimbiyata. 

Ashe amana ta so, 

Ke ba ki ɗauka ba. 

Na sakankance, 

Ina ta washe baki kamar ɓera. 

Ina ta farinciki, 

Na samu dai nima na tsira. 

Daga tarkon matan zamani, 

Na samu mai kyawun sura. 

Ashe da sauran rina, 

A jikin kabar da rana. 

Jikina ɓari yake, 

Ruhina bai saba ba. 

Kaina ciwo yake, 

Ƙwaƙwalwata ba ta ɗauka ba. 

Zuciya narkewa take, 

Sam ba ta yi zato ba. 

Idanu hawaye suke, 

Ba su gano abar ƙauna ba. 

Gani nan abin tausai, 

Kamar marayan zomo.

Da ma dai ki taimaka, 

Wurina bebi ki dawo.

Ki wanke cuta ta rai,

Da sabulu ko kuma omo.

Hankali sai ya kwanta, 

Kamar taliya a romo.

So shi ne sanadi, 

Na ƙauna a fili.

Ki yi yanga domin ke ce, 

Mai kyau da fi’ili.

Ina jira tun ɗazu, 

Gani nan akan dakali.

Daure ki zo gare ni, 

Kar ki barni kamar ɓawon dankali.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Falsafa 1Falsafa 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.