Skip to content
Part 23 of 28 in the Series Falsafa by Haiman Raees

LALE DA SO 

Jajurtuwa kan so, jarmai yake,

Lamintuwarsa ko sa shagala take,

Sauƙin isa kan karagar so ya yake?

Sharaɗi na so na biya,

Don na zamo garkuwa,

Na baki so bai ɗaya,

Na kai ki ƙololuwa.

Ƙaunarki na yi tsiko can ƙarƙashin zuciya,

Tamkar ruwa mai gudu a ƙasan furen lubiya,

Tsoro nake kar a ce so ya zaman rijiya,

Don za na faɗa in kika ƙyale hannuna.

Na tabbatar duniya,

Ba wani mai zuciya,

Ni ne masoyi ɗaya,

Mai sonki ba tariya,

Na zam kamar inuwar wani janibi,

Kuma na ɓace a duhu ke ce na bi,

Kullum na kalli wata in gan shi kamar rabi,

Nazarinki ne ke tsamo so a ƙirjina.

Da babu ke duniya,

Ma da ba zan zo ba,

Da babu ke zuciya,

Ma ba ta buga min ba.

Ni na ga ƙwari suna kuka a kan so,

Na hangi taurari suna faman dakon so,

Ni yaushe ne za ki sau ni in yo jidon so,

Don ke nake rai in ba ke zan kashe kaina.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Falsafa 22Falsafa 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×