ZAFI DA SANYI
Allahu Kai ne dai ɗaya
Kai ne kuma sarkin gaskiya
Kai ne kuma Ka yi duniya
Da komai ma gaba ɗaya
Daga dare har rana.
Ya Rabbi Ka ninka salati
Ga Mustapha Baban Fati
Shi ne Miftahul Futuhati
Annabi mai kyawun zati
Muhammadu ne gwanina.
‘Yar magana ce za na yi
Game da sauyin yanayi
Na zafi har da na sanyi
Dukkansu waye ke yi?
Allahu ne sarkina.
Idan loton zafi yaz zo
Wani sa’ilin ai ta hazo
Kai har ma da bakan-gizo
Wasu na sassaƙa da gizago
Iko sai Allah gwanina.
Da sanyi a jawo bargo
Don ka da ya ratsa ɓargo
A Nijeriya ko a Chicago
A kowane loto na agogo
Cikin dare ne ko rana.
Abin fa ya zarce tunani
Ya ma fi gaban a yi nuni
Sai dai kawai a yi imani
Da lazimi na neman sani
Daga wurin sarkina.
Yanzu lokaci ya canza
Dubi rayuwar dai kaza
Ta yi daban da ta guza
Ko kuma dubi dai gwaza
Wani abin ya fi ƙarfina.
Wasu mutane kan so zafi
Wasu kuma ba sa son zafi
Tambaya suke wanne ya fi
Sanyin ne ko kuma zafi
Duk ɗaya ne ni a wajena.
Wasu na karantar yanayi
Da launukan canjin yanayi
Har ma ɗumamar yanayi
Da sauye-sauyen yanayi
Suna bincike dare da rana.
Wani lokaci su yi kure
Daidai ko kuma su ƙure
Suna ta yin ƙare-ƙare
Wasu ma har da ature
Ilimi kuwa sai sarkina.
Mutane duk sai mu gane
Ilimi ko da na menene
In dai har na nema ne
Yana wurin sarki Allah ne
Shi ke da zamanina.
Ilimin Allah ya fi a tona
wuce dukkan zatona
Kai har ma da hasashena
Da dukkanin t unanina
Allahu ne maƙagina.
Wannan waƙa da na rera
In an ce waye ya rera
Sai ku ce Haiman ya tsara
Cikin nutsuwa babu gadara
Domin wasa alƙalamina.