Skip to content
Part 1 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

AIKIN BANZA

Bismillah da sunan Allah

Shi ne masani gwanina

Shi yai Uba a gurina

Kuma dama shi yai Manana

Tsira da aminci gare shi

Manzo ahalin Ƙuraishi

Wanda duk duniya ba kamar shi

Sahibina me daɗin ƙamshi.

*****

Ya ku jama’ar ƙasta

Assalamu Alaikum gaba ɗai

Na yi gaisuwa a gare ku

Maza, mata gaba ɗai

Allahu ya taimake ku

A tare haka ko da ɗai-ɗai

Ga nasiha a gare ku

Sai ku saurare ni gaba ɗai.

*****

Yau nasiha na shiryo

Game fa da aikin banza

Ko me ka saka za kai yo

Kai dai kada kai aikin banza

Ga Dankali da Yalo

Me za ka yo da Gwaza?

Da ka ɗau kwaɗi a sanho

Ai gara ka ɗau ƙwai na Kaza.

*****

Aikin da duk bai da lada

Tabbas shi ne aikin banza

Ko kuma a ce babu la’ada

Shi ma ya zam aikin banza

Ai gara ace ka hau gada

Da ace ka yo aikin banza

Ko kai tallar kadada

Ya fi maka aikin banza.

*****

Burina ni a kullum

Kuskurenmu mu zam gyarawa

Nasihata a kullum

Kayan wani kar mu yi ƙawa

Fatana ni a kullum

Allahu ya yo shiryawa

Sarki masani mai kullum

Laifinmu ka yo yafewa.

*****

Zan dakata a ɗan nan

Domin in yo hutawa

Ni ne dai naku Haiman

Me yin waƙar faɗakarwa

Ko da wataran bana nan

Nasihata ku yi tunawa

Domin Allah yana nan

Ba ya bacci ko makuwa.

Fasaha Haimaniyya 2 >>

15 thoughts on “Fasaha Haimaniyya 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.