Al’ummata
Ku mu hankalta
Mu daina mita
Mu ɗau nagarta
Da halin bauta
*****
Bismillahi Allah da ya yo sammai
Shi ya yo bishiya har da fa su ƙassai
Shi ya yi duniya ya ce a bauta mai
Shi ya yi dolaye kana ya yi jarmai
Ya ibadallah ya kamata mu bauta mai
*****
Allah
*****
Tsira da aminci wurinsa abin ƙauna
Manzo habibi ɗaha abin ƙauna
Salati wurinsa ɗa wajen Amina
Shugaban halittu ɗaha abin sona
Ya ibadallah gare shi mu yi biyayya
*****
Manzo
*****
Ya ibadallah gunku na zo yau ni
Ga tunatarwa ga duk mai imani
Gare mu dukka ku har zuwa ni
Ku mu hankalta mu kama addini
In kuma muka ƙi za mu shige tasku
*****
Wayyo
*****
Mai jan kunne kun san dai bai son mu
Baya son mu ko ci gabanmu
Al’adarmu har addininmu
Duka bai son su har da abincinmu
To mu ɗau ɗamara don gyaran kan mu
*****
Bayi
*****
Maimakon haka nan sai muka ɗau wasa
A tsakaninmu muna ta sa-in-sa
Wasu na talla wasu na shan barasa
Ana kashe mu kamar mun zama mussa
To ibadallah ya kamata mu hankalta
*****
Ya fi
*****
Wanda bai son mu shi fa muke ƙyama
Wanda ke son mu sam ba ma sonsa
Rana zafi inuwa na ƙuna
Ga mu nan zaune muna ta hayyasa
To ibadallah ya dai kamata mu hankalta
*****
Ya fi
*****
Ku mu hankalta mu ɗau halin nagarta
Mu daina mita mu koma yin bauta
Ku mu hankalta ku al’ummata
Ku mu ɗau gyara maza duka har mata
In mukai hakan za ko mu rabauta
*****
Bayi
*****
Al’ummata
Ku mu hankalta
Mu daina mita
Mu ɗau nagarta
Da halin bauta