Ka Cuce Ni
Babana ka cuce ni
Ka tauye mini haƙƙi
*****
'Yata karda ki zarge ni
Allah zai baki sauƙi
*****
Babana ka cuce ni
Ka tauye mini haƙƙi
Aure nake so
Na bayyana maka ka ƙi
Ina da masu sona
Amma ka ce musu ka ƙi
Ka ce sai boko
Na gaza ce maka na ƙi
*****
Sanadin haka ne
Kai ko ka tauyan haƙƙi
Na kammala digiri
Ka ce sai na ƙara
Samarin cikin gari
Ka ce kada in saurara
Ƙawayena duk sun yi aure
Wasunsu ma fa har da. . .
Masha Allah.
Ya ƙara shiryar da mu
Amin. Jazakallah Khair. #haimanraees