Wakar Bakandamiya
Wata in har ta fito
Taurari dole su ja da baya
Rana in har ta fito
Tafin hannu bai karewa
*****
Da sunan sarkina
Allah na mai kowa da komai
Wanda ya yi mana rana
Yai ruwa gefe can kuma ga mai
Tsira da amincinsa
Su tabbata a gurin ɗan Amina
Alaye da sahabbansa
Da dukkan mai son Manzona.
*****
Bakandamiya mun danno
Muna nan ko a ina ka duba
Kambu in muka murzo
Saura ai dole su ja da baya
Shi mai nema na jini
Wannan ai sai ya yi can kwata
In ko labarai ne
Sai Bakandamiya ai ƙawata.
*****
Shirye-shiryen mu a tsari
Ƙwarai suna faɗakarwa
Komai namu tsari
Aiki tsaf ba wata hargowa
Marubuta ku taho nan
Akwai dama domin bugawa
Mai karatu ka taho nan
Kai karatu tamkar ba kowa.
*****
In harbi kake so
Sai kunama ko kuma jaki
In ko bayanai kake so
Sai Bakandamiya gandun aiki
Taskar mu akwai faɗi
Tana nan kullum kan aiki
Bata da kowa na haɗi
Ta zama sha kundum babu raki.
*****
Bakandamiya son kowa
Ba ma tsari na su ‘yan wawa
Ma’aikatanmu haziƙai
Aiki kawai muke babu ƙiwa
Ana batu na giwa
Wake kawo zance na sauro
Bakandamiyar kowa
Ita ɗai ce domin ta fi saura.
******
Kafa ‘yar zamani
Me basajar tafiya a tsari
Ta zagaye ƙauye da birni
Da ƙamshi babu batu na wari
Kayan aiki zan-zan
Komai na tafiya kan tsari
Aiki tangarasras
Babu shirme kuma sam babu tsiwa.
*****
Allahu nake roƙo
Ya ida mana manufa a kullum
Sarkinmu nake roƙo
Ya kare mu da sharri a kullum
Ni ne naku Jamilu
Ko kuce Haiman ɗan Kaduna
Mai waƙe Bakandamiya
Nake ta adabo sai watarana.
Masha Allah! Godiya muke, Haiman. Allah Ya kara basira da daukaka, Ya bar zumunci, Ya ja kwana.
Amin, Jazakallah Khair
Masha Allah. Allah ya ƙara hazaƙa.
ye
yes