Skip to content
Part 30 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

Zabina

Ni ke na zaɓa cikin ‘yan mata

Don ke kaɗai ce a zuciyata

Bana buƙatar ki bani rata

Gara ki zam mini sarauniyata

*****

Ke ɗai nake so a zuciyata

Kin zama jigo na rayuwata

Kada ki ce za ki bani rata

Ke ce kaɗai magani na cuta

*****

A zuciya ke nake ta ƙauna

Babu kamar ki a duk wurina

Ga zuciyata tana ta ƙuna

Ki zo ki bata ruwa na ƙauna

*****

Ganin ki ya ke farincikina

Yasa zuciya ta daina ƙuna

Tunda na ce ke ce zaɓina

Sai ki bani jiƙo na ƙauna

*****

Ƙaunarki guna ta zamma farali

Domin wurina kin zamma gadali

Son ki ya zama jinin jikina

Ƙaunarki ta zama ruwan jikina

Kin zama hasken cikin idona

*****

Kin zama sanyin da ke a raina

Akanki ni za na bada kaina

Ko da dare ne ko kuma rana

Ke kaɗai ce kawai zaɓina

*****

Ke ce muradi na zuciyata

Ke ce ruhi yake buƙata

Na baki komai na rayuwata

Tunda ke ce sarauniyata

<< Fasaha Haimaniyya 29

2 thoughts on “Fasaha Haimaniyya 30”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×