Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Fitilar Kwai by Dielaibrahim

Tun ba a fara min halitta ba na ke wahala, har tsahon watanni biyu a cikin ciki ina gwabzawa tare da mahaifata, ni ne ƙwan halittar dake cikin ta, ƙwan halittar da ake son a zubar. Kaifin kwakwalwar da Allah yayi ma jarirai ya sanya na ke fahimtar cikin labaran ta akwai rina a kaba. Mahaifiya ta ta shiga halin tsaka mai wuya, ta sha gwagwarmaya a rayuwar ta don kare ni daga magungunan da Abba na ya ke kawo mata don zubar da ciki na, Abba ya manta cewa mugun nufi, baya kashe ɗan barewa kuma da ikon Allah haƙan sa ba zai taɓa cimma ruwa ba akan gurbatacciyar buƙatar sa.

A lokacin da sinadarin allurar ya feso zuwa mahaifar wato cikin in da na ke babu irin jijjigar da ban sha ba, maganin ya so ya tarwatsa sassan jiki na wanda bai da ɗe da zama tsoka ba, da ikon Allah na koma bayan mahaifarta na yi wa kai na ɓuya duk da tsananin wahalar da na sha tsakanin rayuwa ko mutuwa, Allah ya zaɓa min rayuwa, tsahon watanni shidda ina bayan mahaifarta sannan na dawo na zauna daram a cikin mahaifarta na kuma ɗaura daga kwanakin da na tsaya,lokacin na san da cewa kainuwa dashen Allah ne, haka zalika zakaran da Allah ya nufa da cara ana muzuru ana shaho sai yayi abin sa.

Tula Kaltungo

Yankin arewa maso gabashin Najeriya, Tula karamar hukumar kaltungo cikin jihar Gombe.

Babban gida ne daga waje fentin da plaster da tsarin gidan ya tsaru ta yadda alkalamina ba zai iya rubuta adadin tsaruwar gidan ba.

Cikin gidan ɓangare biyu ne mai kyau da kuma mara kyau. Sashin da za ka fa ra cin karo da shi, shi ne wanda ya ke hannun hagu kusa da ɗakin mai gadi, ɓangaren kamar ba a gidan yake ba. Sashin mu ginin blo ne wanda ba a karasa masa plaster ba, rufin ma babu ceilin, kofar ɗakin umma ƙasa ce cike taf yashi wanda yake shan shara a wajan Umma kullum kasancewar babu siminti ko interlock da akwai bishiyar bedi da tayi mana rumfa a kofar ɗakin.Umma ta na zaune saman tabarmar ta gaban ta wani babban baƙin baho ne wanda yake chike taf da goron tula sana’ar da ya karɓe ta hannu biyu kuma ta dogara da shi.

Wani ɓangare na hannun dama a cikin gidan tsararran gini ne ginin blo mai kyau ya tsaru makurar tsaruwa, ƙasan barandar interlock ne aka kuma kewaye sashin da gajeruwar katanga mai huji huji, ma’ana an keɓance sashin ta yadda idan ba ka doshi wajan ba baka iya ganin cikin sashin da kyau….Muryoyin yara ne manya da kananu suke ta wasa, uku manya suna karatu, biyu yara masu shekaru goma suna ta wasa da keke kowa da nasa abin gwanin ban sha’awa.

A wannan lokacin ina kwance saman tabarma gefen da Umma take zaune ina jan jiki wasa na na ke amma kunnuwa na suna ɗauko mun muryoyin yaran gidan daban daban izuwa kwakwalwata.

Bana iya tashi tsaye balle nayi tafiya, koda yaushe ina kwance ina rarrafawa tamkar macijiya, babu wani abu da ya fi saurin kai sako zuwa kwakwalwata face maganar Umma ta shekara ta bakwai, ni ma mutum ce kamar kowa, mara lafiya, bana gane me a keyi cikin duniyar mutane bana kuma gane kowa kasancewar kwalkwalwar tawa ba ta amsar sako sai bayan sa’i talatin kafin na ke iya gane abin da ake nufi.
Wannan kenan.

Washegari
8:00am

Ko wacce safiyar ubangiji da izinin Allah na ke sake samun rayuwa, Cikin madaidaicin ɗakin Umma ta na kai idanuwa na saman cilin daga nan nake sanin safiya tayi, kafin na yi wani yunkuri tuni na sako bayan gari na a kunzugun da Umma take min.

Da sallama na jiyo muryar da sai da hanjin ciki na suka kaɗa, idanuwa na suka soma juyawa tamkar mai aljanu, A lokaci ɗaya jiki na ya soma kakkarwa, yayin da ina ta kokarin son ganin na matsa gefe sanin cewa duk shigowan da zaiyi sai yamin abin da ba zan ji da daɗi ba.

“Tauraruwa mai wutsiya, ganin ki ba bu alheri” Ya faɗa yana tsirta yawu a waje ya yamutsa fuska ya toshe hanci ba kakkautawa ya fita bakin kofa yana kwala kiran Umma, Maryama, Maryama wai ina kike ne”.

“Gani fa ina ta amsawa aradu” Ta taho jiki duk kyarma, doso kofar ɗakin taji warin kashin ƴar tata hakan ya tabbatar mata da yau kam mitar Abba na sai in da karfin sa ya kare.

“Zanyi kwallo dake billahillazi Maryama ki fita daga cikin ido na” Yayi kwafa sannan ya cigaba da cewa,”Shikenan garin Allah ya waye baka isa ka shigo duba iyali ba sai wannan yarinyar mai kama da…” Sai kuma yayi shiru ban san dalili ba.

Umma ta tashi ta shiga ɗakin tana cewa,”Kayi hakuri, ban san tayi bayan gari ba, Abba kamar Amani ba ƴar ka ba”

Haushi ya sa Abba ya kai hannu zai make Umma amma ta kauce ta ɗauke ni ta kai ni waje, Ina jin yadda yake kwallo da butar Umma ya fice da ga ɗakin.

Jin sautin kukan ƙuda sun dabaibaye ni, abin sai ya zame min kaman wasa, saboda a duniya ta babu yaran da suke zuwa wasa dani, ban san zafi ba ban san sanyi ba, ma’ana bana gane mai kyau da mara kyau, bana gane mutane kasancewar ba kasafai nake gani ba sai wulgawan mutum sai kuma muryoyi kalilan. Murya uku, idan kuma na ƙoƙarta gani nazan iya hango inuwar mutum biji biji/blur.

Umma tana gyara ni na ji saukar ɗigon hawayen ta zuwa gadon baya na, alamar kuka takeyi sai dai bani da bakin da zan bata haƙuri.

Umma ta kirawo suna na wanda ko da yaushe da shi nake amsa kiran ta, Amani

A hankali na juyo da fuska ta kamar ina ganin ta, ta cigaba da cewa,”Yan da mahaifin ki ya tarwatsa rayuwar ki In Sha Allah wata rana sai kin zama abin kwatance, Allah zai albarkaci rayuwar ki, ta yanda babu mai yi miki wulakanci”Murmushi ne ya suɓuce wa fuskar tawa, to zan iya sanya hakan a ma’anin wani mataki na gane in da maganar ta ya dosa saboda na saba jin ire iren maganar daga bakin ta. Ta ajiye ni a cikin baho tana yimin wasa, tsahon minti talatin tana bani tuwo wanda na ke karɓa da kyar, har sai taga na fara kauda kai sannan take fahimtar na koshi.

Hayaniyar yara yafi yawa ta ɗayan ɓangaren da Umma take ajiye ni, jifa jifa suna zuwa inda nake suyi ta dunguri na, duk da ban san ma’anar abin da suke yi ba, da sun dungure ni sai na yi dariya, idan ƴan kukan su ka zo kuma sai na fara kuka har sai Umma tazo ta ɗauke ni, idan naji ɗimin jikin ta sai na kama murna don har murmushi nake mata nayi ta ɗariya ina kwantawa a jikin ta.

“Kai Allah dai ya wadai naka ya lalace, Idan mutum baya da aikin yi shikenan zaman ban za da aikin banza ya same shi”

Naji ana yiwa Umma na magana, ba so ɗaya ba kuma ba sau biyu ba ina yawan jin muryar kwana ki ma har mari aka wanka min akan Umma ta aje ni a gefen katangar sashin da ba namu ba, kuma ta ce,”Maryama an yi muku iya ka da kofar ɗakin nan amma kamar mayya sai kin zo, na faɗa miki ko abinci kika gama zai aiko mana da shi ki ba ma Mama Ladi ta rinƙa kawo wa ko ki ba ma Mai gadi bana son ganin ki ke da aljanar ƴar ki a harabar sashi na daga yau”

Duk da cewa ba na magana ba na motsa sassan jiki na balle nayi wani abin amfani amma kunnuwa na lafiyan su kalau domin ina jin magana kuma ina fahimtar duk abin da aka faɗa ba ni da bakin amsawa ne.

BORNO

Bayo karamar hukuma ce dake Jihar Borno, karkashin hanyar Masarautar Biu, mafiya yawan Al’ummar mutanen baburawa ne.

Bakin titin da yakasance titi ƙwaya ɗaya tal mai kyau a garin wanda manya da kananan motoci da keke napep da mashina suke bi zuwa cikin gari, A kalla ba akasari ba zai ɗau kimanin awa guda yana tsaye, kallo ɗaya za kayi masa ka hango tarin gajiyawa da ɗunbin wahala da jikin sa ya nuna, kananan kayan jikin sa masu launin baki wuluk, sun sha tsufa haɗe da datti da kuma alamar yagewa, sai maikon man inji da alama ma’aikacin gareji ne.

Kaifin walkiyar da ya sauka shi ya bashi damar hango kwantaccen hadarin daya shata yayi baki sidik

Hadarin da ya mamaye sararin samaniya, haɗe da guguwa mai ɗauke da iska wacce kasa ke dabaibayi a idanuwan muta ne, a dai dai lokacin ya tsaida wani mai napep karo na biyar kenan babu mai tsaya wa, sai wani baba tsoho mai nema wa iyali abin da za su saka a bakin salati.

Cikin ɗan tsukukun layin gidan su mai zubin lungu dan da kyar napep dinnan ta shiga wajan, Ya fancala kafafuwa babu sallama ya fada gidan nasa yana faman kiran sunan Fatou wacce take tsugunne alamar ta na shan wahalar naƙuda.

Da karfin zatin da Allah ya basa ya taimaka mata ta mike tsaye ya fitar da ita tsakar gida bayan ya sanya mata hijabi suka karasa bakin kofar gida ya shigar da ita adaidaita suka tafi asibiti.

Asibitin gwamnati wanda ya ke garin Bayo dake jihar Borno. Yana ta safa da marwa, kallo ɗaya za kayi masa ka hango tashin hankalin dake kunshe a  fuskar sa bayan wani lokaci likitocin guda biyu suka fito suna kiran sa akan ya same su a offishinsu.

“Malam wato haƙiƙanin gaskiya baiwar Allah nan matar ka ta sha wahala” cewar ɗaya daga cikin likitocin suna magana da harshen turanci, wanda suke sirka masa da yaren kanuri kasancewar mafiya yawan majinyata duk kanuri ne.

“Likita ku taimaka ku ceci rayuwar matata da jaririn dake cikin ta” Cewar Bukar Mijin Fatou

Cikin ƙwarewa da nuna sanin aikin su suka mika masa wata takarda suna nuna masa inda zai sanya hannu ba tare da yi masa cikakken bayani ba, takaita bayanan su kayi ta hanyar cewa,”Za mu sanya mata ledar ruwan naƙuda wanda zai taimaka mata ta haihu” Suna kai wa nan suka fice, su ka bar Bukar da faɗin,”Na gode na gode likita, Fatou Allah ya sauke ki lafiya”.

Tun bayan da aka sanya ma Fatou ruwan naƙuda wanda aka soka allura, tun daga lokacin ta soma jin wani yanayi mai wuyar fassarawa, ciwo ya ƙaru azaba kamar za ta bakunci lahirarta, cikin jikin ta ya rage motsi numfashin cikin ya daidaita ya koma harbawa a hankali. Cikin ikon Allah ta ɗauki awa biyar tana gwabzawa tsakanin rayuwa ko mutuwa kafin Allah ya bata sa’ar haifo jaririn ta bayan sa’i guda yayi kuka don har an fara tunanin ya mutu ne.

Bayan kwanaki ko ince sati biyu da haihuwan *Ibbi* wato Ibrahim hankalin Iyayen sa Bukar da Fatou sun yi matukar tashi sanadiyar jaririn baya abubuwa kamar sauran lafiyayyun jarirai, sai ya zamana kullun suna sintirin zuwa asibiti don binchiken ainahin abin da ke damun Ibbi.

JIBIYA, KATSINA, NAJERIYA

Garin Jibiya na cen Arewacin birnin Katsina kimanin kilomita arba’in da huɗu (42) Garin jibiya yayi iyaka da Jamhuriyar Nijar da kuma Jahar Zamfara Najeriya.

General hospital Jibiya, wanda ake masa laƙabi da asibitin hayin gada asibitin yana da sashi daban daban wanda ake karɓar marasa lafiya, Maternity word wato ɗakin haihuwa dare ne mai tsananin duhu da zafi kasancewar zafin garin Jibiya ya fita daban dana sauran garuruwa saboda suna kusa da sahara wato Nijar.

Muryar ta kaɗai ke tashi daga cikin kusurwan ɗakin haihuwan tana ƙara labarta wa Inna abin da ya kawo ta asibitin har likita ya umarci Nurses da su yi mata allurar nakuda….ta ce,”Naƙuda ta ba ta tashi ba, suka yi min allurar nan Inna” Ta cigaba da cewa,”Ni ban san wace irin allura bace amma sun ce wai tayi failing ma’ana allurar ya gaza, Inna babu likitan da yazo du bani tun jiya, nurses ne kuma suma ɗirka min magunguna na kasan harshe suke tayi”

“Ki yi shiru Fadila, In Sha Allah babu abin da zai samu jaririn ki da ke kan ki, tun da sun zo yanzu kuma sun tabbatar mana da cewa zaki iya haihuwa da kanki, sai mu yi ta addu’a Fadila”.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.