Skip to content
Part 11 of 13 in the Series Fitsarin Fako by Sanah Matazu

Tunda garin Allah ya waye take tunanin hanyar da zata gabatar da abinda ta ga ni cikin mafarki. Ba kowa ba ce face matar Alhaji Labaran. Daren jiya ubangiji ya ye mata hijabi aka nuna mata tukunyar tsafin da take a ƙarƙashin gadonsa wadda aka bata tabbacin matuƙar ta fitar da ita za a sami babban naƙasu wajen gudanar da hidimomin tsafinsa. Ƙila ma ta karya alkadarinsa.

Lokacin da ta farka ta ɗauki abin kawai a sha’ani irin na mafarki sai dai kuma ta kansa mantawa. Kwananta uku tana juya lamarin cikin ranta. A kwana na huɗu ne ta yanke shawarar ba wa Baba Ladi kuɗi a yi mata saukar alƙur’ani kan ubangiji ya bata nasara akan manufarta. Ta rasa wanda zata gayawa damuwarta ta ji daɗi. Duk duniya mutum ɗaya take hange kuma ya gagareta samu wato Aufana.

Har gobe tana hassaso yanayin fuskarta, murmushinta tare da kuma karamci da tausayi irin nata. Sai dai ta rasa inda zata ganta. Hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba lokacin da Baba Ladi ta zo mata da labarin saceta. Dan haka ta duƙufa addu’a babu dare babu rana kan ubnagiji ya bayyanata.

A ranar kwana na bakwai ne ta sake maimaita mafarkinta, har ma da wajen da zata ɗauko abin da ake nuna mata. Sossai ta tsorata da yanayin da ta ga ɗakin a mafarki duk da ta kai shekara kusan takwas rabonta da shigarsa. Dan haka abin ya dinga cinta a rai har lokacin da ya yi sallama ya bar gidan. Be nemata ba, idan da sabo ta saba, domin tunda suka zama dalilin nakasarta baya ta ita. Idan ma ya zo inda take to be wuce labarin ɓarnar da yake gudanarwa  a doron ƙasa ba ce zai zauna yana zayyane mata ita. Wanda hakan ke sakata zubar hawaye babu ƙaƙautawa.

Tun fitarsa take tunanin hanyar da zata bi, ƙarshe dai ta nemi haɗin kan Baba Ladi. Sai da suka bari sahu ya ɗauke sossai sannan suka nufi ɗakin. Da farko sun tsorata saboda karikicen kayan tsafi da suka dinga karo da su. Haka suka dinga bincike da tsantsani har suka kai bakin gadonsa. Cikin taimakon Allah suka sauke katifun tare da janyo wata ƙwarya. Take wata irin ƙara ta soma tashi wadda ta karaɗe gidan gaba ɗaya. Addu’a Baba Ladi ta soma yi, sossai take ƙaranta ayatul kursiyu sai hayaƙin ya lafa.

Ɗaukarta suka yi suka fito ta ƙofar bayan sashin nasa suka nausa cikin lambun gidan. Sai lokacin suka soma taradaddin abin da zasu yi. Domin ƙwaryar rufe take da fefe. Ɗaukarta matar tasa ta yi ta riƙe tare da ɗagata sama. Bakinta ɗauke da addu’a ta ƙwaɗata da ƙasa. Take wata irin hallita ta bayyana me tsananin girma. Hancinta dogo yayinda kanta yake kamar na mutum sai dai tana da ƙafaffu guda huɗu tare da fuka-fukai masu ban tsoro. Wata murya ce ta karaɗe gidan gaba ɗaya,

“Labaran ka saɓa alƙawari zaka girbi abin da ka shuka…”

Cikin hanzari ta ɓace ɓat a sararin samaniya su kuma suka miƙe duk a tsorace suka koma ciki suka gyara gadon yadda yake. Da taimakon Baba Ladi komai ya kammala ba tare da wani ya gansu ba. Dan matar Alhaji Labaran ta koma kan kekenta na guragu ta zauna kamar yadda take a matsayin nakasashiya.

*****

Tun da Dr Badamasi ya fito gabaɗaya hankalinsa a tashe yake. Bai taɓa zaton abin da ya binne zai fito ba. Shin ta yaya Abdallah ya san ya yi sadaukarwa da ɗiyarsa Aisha? Kansa ya ɗaure tamau ya san Abdallah da naci da bin ƙwaƙwafin abin da ya sa gaba, amma bai taɓa tsamanin cewa ya kai haka ba.

 Daga shi sai Alhaji Labaran da wasu manya cikin hadiman Alhajin suka san da wannan batu. Ko Salisu da Gundul ba su san da wannan ba, duk duniya matar Alhaji Labaran ce kaɗai warraki da ta san wannan lamari kuma sun yi dalilin da ba za ta iya motsi ba ma balle kuma a kai ga magana. Gumi yake sharewa har ya ƙarasa mahaɗarsu wajen da ya kasance sirrantacce a wajansu.

Yana shiga gabaɗaya ya same su cikin shiri, a tsaye ya tsaya fuskarsa na bayyana tashin hankalin da yake ciki. Gabaɗayansu jajayen kayane a jikinsu, idanunsu zagaye da farin abu yayin da aka jashi a tsaye daga kan hancinsu zuwa tsakiyar goshinsu.

Gabansu wata ƙatuwar ƙwaryace wadda girmanta a ƙiyasi za ta ci mutum hamsin. Gabaɗaya an zagaye gefanta da wuri mai ɗauke da kaloli mabambanta. Cikinta jini ne yana wata irin zaɓalɓala kamar ana rura wuta. Haka kowa yake saka ƙwarya ƙarama ya kwarfa ya sha kamar ruwa. Sai da suka gama sannan suka zauna suka zagayeta suna waɗansu irin surutai. A daidai wannan lokacin ne kuma maiɗakin Alhaji Labaran ta fasa ƙwaryar da ta ɗauko.

Take ƙwaryar ta soma wani irin tambal-tambala. Ɗakin ya gauraye da wani irin sauti mara daɗin amo da saurare. Jini ne ya soma zubowa ƙasa, saboda girgizar da ƙwaryar take yi. A take wannan hallitar ta bayyana rabin jikinta duk ya ƙone sakammakon addu’ar da suka yi kafin su fasa ƙwaryar. Da wata irin murya ta ƙara me amsa kuwa,

“Babu wani sauran abin sauraro Labaran ku je zaku gani ƙarshenku na dab da zuwa…”

Kamar ɗaukewar ruwa, sautin da ƙwaryar da suka zagaye da kuma hallitar suka ɓace ɓat a wajen. Take cikin kowanansu ya ɗuri ruwa suka hau tattauna yadda zasu ɓulowa lamarin.

*****

Lokacin da Baba Barista ya koma gida, ya cika da tsananin mamaki ganin Salisu a ƙofar gidansa, amma kuma sanin tuggun Alhaji Labaran ya ba shi tabbacin zai iya komai domin ya kafa tarko ya mallaki abin da ransa yake da muradi.

 Amma a yanayin yadda tashin hankali ya bayyana a fuskarsa ƙwarai ya tabbata abin da ya kawo shi ba mai sauƙi ba ne. Tun kan ya fito daga mota ya ƙaraso bakin motar yana fitowa kuwa ya damƙe hannunsa kamar zai masa gafara.

“Wallahi duk wata shaida da kake buƙata zan baka ita matuƙar za ka karɓo mini ‘yata, dan Allah ka taimaka mini kada ya salwantarmin da ‘ya”

Yanayin da yake magana ya ba shi tabbacin ba a cikin hayyacinsa yake ba, dan haka kallo ɗaya ya yi masa ya tabbatar da zuwansa ba tuggu ba ne, akwai abin da ya kawo shi. Hannunsa ya kama ya shiga da shi cikin gidan. Yana shiga kuma ya riski wani sabon tashin hankalin. Kamala ne zaune a kan kujera ya yi zurfi cikin tunani har bai ji sallamarsu ba. Kansa ɗaure yake da bandeji yayin da gefan bakinsa yake a kumbure babu kyan gani domin bakin ya karkace gefe ɗaya. Da sauri ya ƙarasa wajensa yana tambayar,

“Kamal lafiya kuwa?”

Ruɗewa ta saka shi kiran cikakken sunansa wanda rabonsa da hakan har ya manta tun da Aufana ta soma faɗar Kawu Kamala maimakon Kamal su ma suka ara suka yafa. Idanu kawai ya runtse sai ga hawaye na zuba kamar ƙaramin yaro,

“Kaicona Abdallah kaicon biye wa zagon ƙasan marasa imani da sunan ba wa ahalina kariya. Da hannuna nake ɗaukar makami na saka a mota na siyarwa da ‘yan ta’adda a yi amfani da su a kashe ‘yan uwana musulmi.

Da hannuna nake ɗaukar kayan maye na tuƙa mota na kai wurare da dama a siyarwa da matasa ‘yan uwana da sunan bada kariya ga ahalina.

Da kaina nake tuƙa marasa imani na  kaisu wajen da za su yi shirka domin samun duniya duk da sunan ba wa ahalina kariya. Sai dai duk da hakan da na yi bai isa ya zama waigi gare su ba, hakan bai yi musu ba, sai da suka raba ni da Innata da sunan jan kunne.

Wannan ma bai musu ba, suka raba ni da ƙanwata Halimatu bayan ta yi yunƙurin bayyana mini wani sirri da take ɗauke da shi. Duk wannan bai ishe su ba, yau sun raba ni da Aufana ban san halin da take ciki ba kuma shi ne ba su haƙura ba suke farautar rayuwata. Tabbas ɗan hakkin da ka raina shi ne yake tsone maka idanu, wallahi ko zan mutu sai na bayyana wa duniya asalin fuskar Alhaji Labaran”

Ya ƙarashe da ƙaraji mai ƙarfi,

“Ba kai kaɗai ba Gundul, wallahi har da ni. Domin ina ɗauke da tashin hankali kwatankwacin naka”

Gabaɗaya suka zuba masa idanu suna mamakin abin da zai sa ya bijire wa Alhaji Labaran ɗin bayan shi ne babban yaronsa kuma amintacensa. Bai damu ba ya ci gaba,

“A yanzu haka ‘yata da ƙanwata da ‘ya’yan yanayana suna hannunsu. Sun yi garkuwa da su!”

“Garkuwa kamar yaya?”

Baba Barista ya katseshi da sauri,

“ƙwarai kuwa Barista garkuwa da ka sani. Ina da tarin hujojin da zan ɗaure Alhaji Labaran da jijjiyoyin jikinsa matuƙar na sami goyon bayan da ya kamata. Alhaji Labaran na da hannu a sace ɗaliban makarantar ‘yan mata ta gwamnati. Barista ka san mafi yawa daga laifukan munafikin mutumin nan, ka san duk wasu ɓoyayyun ɗabi’unsa ina da tabbacin za ka zame mini tsani”

“Salisu duk da na san komai ta yaya za mu ɓulo wa mutum mai haɗari irin wannan? Kada ka manta yana da manya a ƙasa da sama”

“Barista a baya rashin nagartattun jami’an tsaro ne ya sa ba a hukunta Alhaji Labaran, to a yanzu ba mu da wannan fargabar, kayan sun tsinke a gindin kaba, ina mai ba ku tabbacin wannan sabon kwamushinan ‘yansandan ya zarta duk tunanin wani mahaluƙi wajen gudanar da gaskiya da riƙon amana, lokaci ya yi da za mu shigar da ƙara, ni kuma a shirye nake ina da tarin hujojjin da ko da baku da ko guda ɗaya zan tsaya tsayin daka wallahi Alhaji Labaran sai ya ci sarƙa”

Jikinsu ya yi sanyi sosai, duk abin da ya fito da ɓera daga rami ya faɗa wuta to haƙiƙa ya fi wutar zafi, don haka gabaɗayansu suka yi na’am da ƙudurinsa.

“Na gamsu da bayaninka Salisu. Sai dai muna buƙatar jajurtattu cikin tafiyar tamu. Aiki ne ja a gabanmu, be zo ba be ƙare ba. Ƙasarmu a rarrake take da wani irin rami me sarƙaƙiya.  Duk yayin da mutum ya yi wani ƙwaƙwaran motsi to akwai na bakin ramin da yunƙurinsu su tunkuɗa mutum. Babu ruwansu da zai iya kaiwa ko kuma zai ji ciwo matuƙar burinsu zai cika”

“Haka ne barista amma kuma matuƙar muka dogara da ubangiji zai ji ƙanmu”

“Nan ma ka yi magana me fa’ida”

Kamala ya furta yana cije leɓansa. Sosai suka jima suna tattauna lamarin duk wani waje da Salisu da Kamala da suka san Alhaji Labaran na gudanar da ayyuka da suka haramta sai da suka zayyanewa Barista. Ba ƙaramin daɗi ya ji ba, a zuciyarsa yana jin ina ma Halimatu na raye yana da yaƙinin za ta fi shi jin farinciki matuƙa, akwai ƙudurin fansa a ranta fiye da dukkan ƙoƙarin da suke yi. Har yanzu yana takaicin rashin saduwa da ita domin bayyana masa sirrin da take ɗauke da shi.

Cikin ikon Allah suna zuwa barista ya riski ashe ma kwamishinan ɗan ajinsu ne. Nan da nan suka ware suna hira har yana tambayarsa Doctor Badamasi. Bai ɓoye masa komai ba game da abin da yake faruwa, sosai ya karɓe su kuma ya yaba da jajjircewarsu sai dai al’ammuran nasu nada sarƙaƙiya domin yadda Salisu da Kamala suke da hannu dumu-dumu a sha’anin Alhajin.  Dole sai an yi taka tsan-tsan. Ba su baro wajen ba sai da komai ya kammala.

Duk wannan kujuba-kujubar da suke yi Aufana na maƙale cikin zuciyarsa kuma bai gushe ba wajen nema mata kariyar Ubangiji a duk lokacin da ya ɗora goshinsa. Cikin kwanaki biyu suka fara cuku-cukun shigar da ƙara yayin da addu’a ta rinjayi burin ƙarar tasu. 

 Cikin tsakanin Baba Barista ya sa ayi masa sauka be san adadinta ba. Haka ma sadaka sosai yake yi musamman ga ƙananun yara. Da kansa ya koma matattarar almajiran da Aufana take zuwa, bayan ya samu keɓewa da Indo mahaifiyar yarinyar da Muddasir ya kaɗe sun tattauna sosai a nan ya bayyana musu ɓatan Aufana da kuma wanda suke zargi.

Sosai suka nuna alhininsu nan da nan suka shiga yi mata addu’ar kariya da kuma Allah Ya bayyanata. A ranar da yamma sai da ya sa Baba Laure ta dafa abinci mai yawa aka kai musu aka rarraba, haka kuma bai gushe ba yana aikata hakan kowane yammaci a zuciyarsa yana ƙudurta sadaka ne domin samun nasara a kan abin da suka sa a gaba.

*****

Cikin ikon Allah komai na zuwar musu da sauki fiye da tunaninsu. Matakin farko da suka ɗauka shi ne Salisu ya koma jikin Alhaji Labaran ba tare da nuna wata damuwa ko tashin hankali ba. Sosai ya shiga aka ci gaba da gudanar da yaƙin zaɓe tare da shi.

 Alhaji Labaran ya shiga tashin hankali matuƙa ganin rugujewar dodon tsafinsu. Gashi kuma tunda ya ɓace be sake bayyana ba sun yi duk wani ƙulumboto sun ga ji. Sun kuma kasa gano ta ina matsalar take tamkar an shafe ƙwaƙwalwarau dan haka suka tattara suka haƙura saboda suna cikin rurrumar zaɓe. Alhaji Sammani ne ya samo musu wani sabon bokan suka cigaba da gunar da aiyukansu yadda suke so.

A gefe ɗaya kuma suna rura wutar gaba tsakaninsu da ƙungiyar adawa ta hanyar biyan matasa suna shiga gidajen yaɗa labarai suna yi wa gwamna mai ci bore kan a biya diyya a sako musu yaransu. Tabbas hakan ya yi wa Alhaji Labaran daɗi duniyarsa yake ci da tsinke, komai na zuwar masa yadda yake muradi. Ko kadan rashin ganin Kamala bai dame shi ba, domin tunanin yake barazanar da ya sa aka yi masa ce ta ɓoye shi.

Duk da cewa a gefe guda yana ganin kamar ya yi wauta domin bai kamata hakan ya kasance ba. Amma yana jin gara ya tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro. Da wannan damar ya zamana duk wani aike da ya karkata a wuyan Kamala ya koma kan Salisu cikin hikima ya fahimci wajen da ka ɓoye Aufana a wata tattaunawar Hamana da Alhaji Labaran da ya laɓe ya ji. Dan haka bai yi ƙasa a gwiwa ba ya turawa barista da bayani da kuma kwatancen gidan.

Wani abun ƙarin armashi kuma tsakanin kwana biyu da yin hakan sai ga shi Alhajin da kansa ya nemi da ya yi musu rakiya. Hakan ba ƙaramin daɗi ya yi masa ba, dan haka ya sake fakar idonsu ya turawa Abdallah bayanin halin da ake ciki. A ƙarshe ya tabbatar masa da ya bar wayarsa a kunne amma ya sakata a silent.

A daidai lokacin suna tare da kwamishina suna tattauna yadda za a ƙara ƙarfafa bincike. Dan haka ya cika da tsananin farinciki. Cikin ƙanƙanin ya haɗa jajjurtattun yaransa masu gaskiya da riƙon amana. Motoci ne guda uku suka ɗauka tare da wadatattun kayan aiki yadda suka kamata.

*****

Zaune take a cikin ɗan ƙaramin ɗakin, gabaɗaya ta rame ta fita hayyacinta. Tun tana tsamanin zuwan Baba Barista saboda dogaron na ga agogon hannunta har ta fitar da rai domin cajinsa ya ƙare.

Kullum da kalar azabar da Hamana yake gana mata. Ya aske mata gashin kanta tas, yayin da ya yi mata tsagu a hannayenta da sangalallen ƙafaffuwanta. Ba ƙaramar azaba ta sha ba, domin da an zaga sai an barbaɗa mata gishi ko ya ji a wajen. Idan aka ba ta abinci da safe, sai wata safiyar, ruwan pure water guda uku da ake ajiye mata shi ne take cancanawa ta ɗaura alwala da shi ta samu ta gabaci salloli biyar.

Damar yin sallah kaɗai da take samu shi ne yake sassauta zuciyarta, domin ta tana da tabbacin ko badaɗe ko ba jima Ubangiji zai karɓi roƙonta. A lissafinta yau kwanakinta ashirin da ɗaya cif, a iya kwanakin Allah kaɗai ya san adadin hawayen da ta zubar, kuma shi kaɗai ya san irin baƙaƙƙen addu’o’in da ta yi wa masu hali kwatankwacin na Alhaji Labaran. Ga cizon sauro ga na cinnaku ga zafi da fama da yanar giza-gizo.

Turo ƙofar aka yi da ƙarfi, wata irin zabura ta yi tare da tattare jikinta waje ɗaya. Domin ta san kwanan zancen ba zai wuce Hamana ne ya zo azabtar da ita ba. Sai dai saɓanin tunaninta, Alhaji Labaran ne da kansa.

Bayansa kuma Hamana ne da kuma Salisu wanda tun tahowarsu su barrister suke biye da su ta hanyar wayar Salisun da suka yi tracing. Wata irin dariya ya kece da ita bayan sun ajiye masa kujera ya zauna, Hamana ya sa ya ɗaukota kamar wata ‘yar tsana ya dankwafar da ita gabansa. Baya-baya ta soma yi tana kuka, jikinta ko’ina rawa yake yi,

“Wato ke tsagera ko? Ai dama da ganin idanunki sai jinin Halimatu Lantana. Ku gabaɗaya danginku ‘yan shiga sharo ba shanu ne ko? To bari ki ji abin da baki sa ni ba. Garin irin wannan shisshigin na danginku ne na tura uwarki ƙiyama. Haka ma kakarki na kuma yi amfani da ƙarfin ikona na mallaki ƙanin uwarki ya zamana bawana ta hanyar yi mini safarar miyagun ƙwayoyi da kuma kayan ta’addanci.”

Zare idanu ta yi, bakinta a buɗe, ya yi murmushin mugunta,

“Eh! Kuma ni Alhaji Labaran ni na kashe mahaifin wanda kuke taƙama da shi wato Alhaji Alhussain Gilɓowa saboda ya shiga gonata, ni na saka Hamana ya kashe shi tare da mai ɗakinsa, na kuma sa aka ƙone gidansa domin na mallaki duk wata kadara da yake taƙama da ita.”

“Kai maƙiyin Allah ne, kuma ƙarshanka ba zai yi kyau ba ina da tabbacin ta sillar kamani da ka yi sai asirinka ya tonu da izininin Ubangiji.”

Ɗauketa ya yi da mari, bakinta ya fashe kanta ya bugu da bango. Ya sa ƙafa ya dake mata gefan ciki. Ƙara ta saki mai amsa kuwa, a daidai lokacin ne su Barista suka ƙaraso cikin gidan ta hanyar sanɗa, domin sun bar motocinsu da wasu jami’an a can bayan gidan gudun jin motsi. Sauri suka ƙara, kuma a lokacin ne masu tsaron gidan suka soma ankara da akwai baƙin fuska. Sai dai sanin makamar aiki irin na ƙwararrun jami’an ya sa ƙafin su farga suka shiga yi musu kisan mummuƙe.

Hanyar da sautin muryar Aufana ya fito nan Barista ya nufa gadan-gadan. Gabaɗaya babu wani tsoro a tare da shi, sannu a hankali har ya isa bakin tagar. Daidai lokacin da ɗaya cikin yaran Hamana ya banka ƙofar da tsananin ƙarfi yana faɗin,

“Oga kwalawa”

A kuma daidai lokacin aka soma musayar wuta tsakanin jami’an da yaran Alhaji Labaran. Kallon-kallo aka yi tsakaninsu, mamaki ƙarara ya wanzu a fuskar Hamana da ubangidansa,

“Ya aka yi aka san muna nan ko ka aiki wani cikin gari ne?”

“Ban aiki kowa ba yallaɓai ya za ayi na yi wannan gangancin?”

Tsai Alhaji Labaran ya tsaida idanunsa a kan Salisu, tuni jikinsa ya soma rawa. Taku ya yi har zuwa gabansa,

“Ban taɓa zato ba Salisu, ni za ka ci wa dunduniya?”

“Yallaɓai…Alhaji…Oga…”

Hannu ya sa ya shaƙe masa wuya ya haɗe shi da bango, tuni ya soma wuntsul-wuntsul. Aufana ta saki ƙara karo na biyu, daidai lokacin Barista ya turo ƙofar ya shigo hannunsa ɗauke da bindiga ya saita shi yana furta,

“You are under arrest!”

Kafin ya ƙarasa Hamana ya kwashi ƙafafunsa ya faɗi ruf da ciki. Ƙara ta sake ƙwalawa, ta yi kansa daidai lokacin da ya saita shi da bindiga ta yi tsale ta dire a gabansa take harbin ya same ta a kafaɗarta.

Ƙarar da ta saki da wadda Barista ya saki ta yi daidai da shigowar jami’an tsaro ɗakin. Aka samu wani mai zafin nama cikinsu ya harɓi Hamana a ƙafa, yayin da wani ya yi wuf ya doke hannun Alhaji Labaran daga wuyan Salisu ya faɗo ƙasa ba ya ko motsi. Nan da nan aka fara tattare su, yayin da masu zafin nama cikinsu suka fara yunƙurin fita da Aufana wadda take kamar matacciya. Ban da gumi babu abin da Baba Barista yake yi.

<< Fitsarin Fako 10Fitsarin Fako 12 >>

2 thoughts on “Fitsarin Fako 11”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×